← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 115

Sashe 95

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannunta, waje da shi aka yi. Ya kara mikewa zai shiga aka rufe kofar da asalin ara. Wani irin kad'awar sanyi gidan yake saboda tsabar karfin da yake jikinta. Kurawa kofar dakin "Layla!!" "A'a kai ka kira mu ai, kace tana takama da mu, eh damu ta dogara bata da kowa sai mu, mahaifinta ma behind corner ya boya kana tsammanin zamu barta ku ta wulakantatta ne kada ka sake ka kara kiran sunanta domin sai mun hana kowa sakata." Ta fada da karfi. "Aisha ki saurare ni!" "kada ka kara kiran sunan nan domin ba nata ba ne!"ji yayi duniyar tayi mishi zafi "why! Why !!Why!!!" Shiru dakin yayi ta koma ta kwanta. Fita Maina yayi da sauri ya bar gidan. Aliyyah da yara kuwa basu san meke faruwa ba, amma wani irin matsanancin sanyi ne ya cika gidan da ya hana kowa sakewa don sai da ta kunna room heater. Amma sanyin kamar kara huro shi ake. Kiran Maina tayi cikin kaduwar sanyi ta fashe da kuka. "Don Allah ka zo, sanyi zai kashe mu!" Ta fada tana kuka. A can dakin Layla kuwa dafa bangon dakin tayi tana murmushin mugunta. "Lallai sanyi zai kashe ku!" Sake dafa bango tayi, bangon gidan ya daskare da ara,a cikin abin da bai fi dakika dari da ashirin da biyar ba, ara ya lullube gidan. Tana kallon Aliyyah da yaran suna rawan sanyi sakamakon kome na dakinsu da ya daskare. "Innalillahi!" Maina ta fada lokacin da ya ga gidan ya na daskarewa da ara. A haukace ya shiga Ammar yana bin bayanshi. "Ammar ka fitar da Aliyyah da Yaran ni zan fita da Layla!" Na shiga bangaren da gudu. Yana zuwa ya daki kofar suka fad'a cikin dakin tana dafe da bangon dakin tana murmushin mugunta. Bangajeta tayi ta fadi a kan gadon. "Kayi kokari! Amma ka sani sai na kashe su!" Ta kuma buga bangon take gidan ya fara girgixa. "Na gaya maka mun zo ne fa!" Ta kuma dukan bangon. Sai ga shi ya rushe, ja da baya yayi har yana faduwa. Baraguzan bangon ne da suka rushe suka fara harhaduwa izuwa suffar mutane, (Look labarin nan bafa a gaske ba ne, ku mishi duban kamar karanta irin adventure ko fantasy novel domin bana son ace yayi wani iri) zuwa gabanta baraguzan suka tayi, har suka hadu bakidaya suka fara shirin cika dakin, rungumar bayanta Maina yayi. "I'm sorry! Na fada miki don Allah kiyi hakuri, kiyi hakuri Laylatuna mai hakuri ce da yafiya Please kiyi hakuri nasan nayi laifi amma kiyi hakuri!" Ya fada yana juyata tana Kallonshi. Dariya ya ta saka me sauti mara dadi. "Mun zo kenan Hatim!" Ta wani ingije shi sai da ya fad i can. "Ka tafi kar nan kafin mu maka iyaka da ita har abada! Kada ku sake ya kara shigowa harabar gidan nan!" Haka baraguzan nan suka kore shi, waje tare da rufe gidan. Juyawa yayi kamar maraya da yarasa kome na shi ya cewa Ammar. "Rayuwata tana cikin gidan nan, da alamu ba zasu barta haka ba, Ammar kayi wani abu." Ya fada tare da jingina da motar da yake gidan, "muje za a san abin yi!" Haka suka fita zuwa bangaren Ummimi nan aka shiga tashin hankali jin labarin abin da ya faru da Layla. Kafin wani lokaci kome ya dagule babu abin da kake ji sai labarin matar Maina ta zama matsafiya. A wannan lokacin Hamidah da sauran mutane suka taso Maina a gaba. Idan ka cire Malik da Abu Ammar da Galadima, sune suke tare da Maina, amma sauran mutanen fadar a bayan Hamidah suke. A cikin abin da bai wuce awa 24 ba, sai ga Maina ya xabge. Ko Queen Hamidah tana asibiti labarin ya isa mata don haka.ta emirates counciler su hade kai a raba Maina da Layla idan ba haka ba tow babu me tsira. Hamidah tayi ta tura musu kyautar kayan arziki a daren ranar da labarin ya zo mata. Domin gagarumin meeting suka yi asibitin ba tare da sanin Malik ba. Sannan aka had'a tawagar marasa tsoron Allah da iya kisar gilla, aka tura su har Mansion din Maina akan su tabbatar sun kashe Layla no matter how kada su barta ta rayu domin masifa ce, bayan haka kada su bar pieces na Albi. Haka suka isa Mansion din da ace sun fahimci girma da azabar da yake cikin gidan babu wanda ya isa ya fara zuwa amma haka suka dauki wannan kasadar suka isa gidan a cikin sulisin dare, lokacin Maina yana zaune a kofar shiga gidan, ya ki barin wurin tun gari da haske Ammar da Salahudeen suka so ya bar wurin amma yaki, wasa wasa Sai gashi har wurin karfe daya na dare ya zauna a kofar shiga gidan, a can dakin kuwa da Layla ta mai dashi fadarta tana kallon Maina ta jikin madubin dakin, tana hango lokacin da wasu suke kokarin hauro gidan. "Ku zagaye shi, su kuma wadancan kurayen ku bazamasu su shiga inda aka turo su a haukace amma kafin nan ku azabtar dasu mafi girman azabar da idanun da ruhi basu tab'a gani ko ji ba." "An gama shugaba!" "Tala wannan ba yi ba ne, ki kyale Layla tana da rayuwa da miji, ga kuma cikin jikinta kada wani abu ya same ta. Na riko ki!" "Gashi Ni bana jin riko Kalya bana jin roko ni kin tsaya a gaba na, idan Ruhin Rihanna ya san da jiki irin na Layla abun ba a cewa kome!" Ta fada tana wani ha e rai. "Ki fita!" Kalya ta shake wuyarta, "Idan na ki fa?" Kamar zata cire kanta haka ta shake ta, fada sosai suke kafin Tal tayi nasarar daure Kalya ta koma gefe tana huci. A wajen kuwa sai da duwatsun nan suka zagaye Maina da barci ya dauke shi, sauran duwatsu suka bari mutanen sun shigo har cikin harabar gidan. Babu wanda yayi saura a waje suka cikin gifta zasu shiga gidan suka ga abu curi guda, zagaye shi suka yi zasu wuce. "Wato Bil adam akwai tsaurin ido, tow bari muga yadda zasu yi." Ja baya mutanen suka yi tare da cewa. "Idan ba tsoron ba ku fito kun koma gefe kuna kananun magana!" "Kato sauka akan kafana ko!" Aka fada juyawa mutumin yayi ya ga shirgeggen dutse akan shi wani irin ihu ya saka ai kuwa, aka fara zane su kamar daga sama wani irin bulala me azabar zafi idan aka zuba musu sai fatarsu ta dare, ga wani uban azabar da basu san ta ina ake kuntatta musu ba, ba a daina azabtar dasu ba tun suna ihu har suka daina. ----------- Goshin asuba aka korasu kamar dabbobi suka bar gidan, Maina kuwa tun fara abin wani basamuden dutse ya dauke shi har zuwa dakinsa na cikin gidan. Ya kwantar da shi aka lullube shi. Sannan ta fita. Ana shiga sallah asuba ya farka ganinta yayi zaune tana Kallonshi. "Ya daren naka?!" A matu ar dame ya sauko ya nufeta. "Koma ka zauna!" A gabanta ya zauna. "Layla ki zo mu ne tafi!" "Ni na kamar Hilda ba ce da bata iya sarrafa kanta. Ni namiji baya gabana. Sako xan baka zuwa wurin Hamidah idan ta kuma aiko min yan iskan da xan iya sakawa a raka su da guguwa idan nazo inda take sai dai a haifi me sunanta kul kada ta kara kusanto inda nake.... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/25, 10:35 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________64 "Na gaya maka kada kara domin zan kashe ta har lahira!" Daga haka ta mike tana me fa in. "wannan sansani na ne, wannan da'ira ta ce. Kada na kara ganin wani anan idan ba haka ba sai na shafe garin baki aya ka ajiye maganata!" Daga haka ta bar dakin yana zaune ya kasa motsi. Har ta isa bakin kofar dakin ta ce mishi. "Kaima bana bukatar ganinka anan!" "Ki fita a jikin Layla!" "Waw ta ina na shiga da xan fita?" Tsare shi tayi da Idanunta masu kalar na mage. "gaya min akwai kofa ne a jikinta da na kwankwasa na shigo? Idan ka kara min magana sai na rufe idanun Yarka!" Mikewa yayi ya nufeta tare da riko hannunta, tA wani watsa hannun sai ga ara ya musu iyaka. "Kada ka sake ka tab'a ni!" "Ki kyaleta ni ki hukunta ni na yarda idan ma kashe ni zaki yi!" Ya fada Idanunsa yana kawo kwallah. Takawa tayi gabanshi aran da ta saka ya narke ta kai hannunta daya gefen fuskarshi. "Wai dama kana sonta har haka ka mare ta? Dinke ta da mari kayi har biyu! Kalli nan!" Ta nuna mishi madubin dakin. Layla ce kwance a kasa tana rawan sanyi. "Na gaya maka ni jikinta na shiga ta hanyar da ka bamu damar shiga, ga matar nan ka dawo da ita sai na tafi. Idan kuma ka gaza na tafi d su dukkansu biyu! Da uwar da abin cikinta." A sanyaye ya bar gidan baki aya, ya nufi bangaren Malik da yake zaune a parlourn shi. Zubewa yayi a gaban Malik. "Abba Layla Aisha!" Ya fada muryanshi na rawa. "Kayi sallah?" Girgiza kai yayi. "Shiga kayi sallah!" "Abba!" "Kana da damuwa ka manta me maganinta ne?" Wucewa ban dakin yayi ya dauro alola yazo ya gabatar da sallah har da azkar da addu'o'i don ma bai da nutsuwa. "Me yake faruwa yanzu?" D'ago kai yayi idanunshi yayi jajjur ya ce mishi. "Sun ce a jawa Queen Hamidah kunne kada ta kara turo musu mutane. Abba Layla tana cikin madubi ma ganta da idanuna wacce take jikinta aljana ce ka taimaka min!" ,"Tow Muhammad zan duba lamarin!" Ya fada yana rarrashinsa. Lokacin da labarin abin da Queen ta saka mutanen nan sun kasa, tuni ranta ya b'aci tayi kiran gaggawa baki aya ta saka mutanen Fada zama a asibiti. "Layla duk abin da zaku yi ku tabbatar kun raba Maina da yarinyar nan sannan a fitar da ita daga masarautar. Na baku nan da awa 24.," "in sha Allah!" Suka fada sannan suka fito masarautar suka koma aka kira Maina suka hura mishi
Chapter 95 · 0% Book details