← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 115

Sashe 97

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin rauni yaji me cike da tashin hankali. "Me yasa?" Ya tambaye, wani kara suka ji a sama. Murmushi tayi tare riko hannunshi suka tashi sama, kafin su nufi kofar ya bu e. Shiga dakin suka yi ta sake shi Layla ya gani a madubi. Zubewa tayi akan gwiwarta. "Tal ki dauki abin da kike so a tare da ni ki bar Sainah kiyi y! Ban da ita." "Layla!" "Papa!" Juyawa yayi yana kallon Tal da take tsaye tana dariya. "Kin isa matakin da ba zan iya hakuri ba!" Shake ta yayi tare da saka mata wuka a wuyarta. "Fita nace!" Ya fada a haukace. "Ka bani idanun Yarka zan fita." "A'a Papa kada ka bata ko da na karen Baihak ne!" "Kin ji me tace." "Zan dauka da karfin tsiya!" Ta fada tana me nuna musu tafin hannunta kwayar idanun ne guda biyu a tafin hannunta sannan ta ce musu. "Na tafi amma yakin bai kare ba!" "Zan zo koda akan rayuwata ne na amshi idanunta." Layla ta fada tana wani irin ihu da kuka, "Ka shirya mutuwarka domin kuwa ruhin Rihanna yana raye, kuma jikin Layla take hari." Daga haka ta sake dariya me kuwwa da arfi me aran gaske, kafin ta sauke Ajiyar zuciya. "Sai na dawo!" "Ka buge hannunta!" Ai kuwa ya aikata haka, kwayar idanun daya ya fadi kasa. "Dauka!" Dauka yayi "saka a aljuhun rigarka" haka yayi yasaka a gaban rigarshi. "Kina son Mijinki, Amma da hannunshi zai kashe ki!" Tana fadar haka ta rufe idanunta. Shi kenan suka tafi har da dayan kwayar idanun. Juyawa yayi ya kalli Madubin. "Layla!" Jan numfashi tayi tana me bude idanu biyu. "Sultan!" Ta rungume shi shima rungumarta yayi yana jin kwalla yana cika mishi idanu. "I'm sorry!" Ya fada a hankali, "ina idon?" Cirowa yayi ya mika mata, hawaye ne ya zubo mata ta goge. "Zan nimo Tal ta bani dayan. Kayi hakuri ban san haka zai faru ba wallahi!" Shafa kanta yayi yana fa in. "Na sani!" A hankali ta cilla idanun sama, tare da shafa sarkan wuyarta take wani phoenix Galaxy light ya bayyana. Idanun ya tsaya a tsakiyar. "Sultan kayi hakuri! Zan maida mata daya dayan xan nimo kayi hakuri!" "Me zaki yi?" "Ka kira zaka gani!" Mikewa tayi ta fada da karfi "Zarbabba zurkurarra zararrarar!" Wani irin girgiza gidan ya fara kamar zai rushe ita kuma iska yayi sama da ita. Tare da wani iska me karfi yana shawagi da ita me karfin gaske. Tal ce ta dawo. "Ba ni idon!" "Wani irin soyayya kike musu?" "Ba ni nace! Babu ruwanki da rayuwata!" Ta fada tana na mika mata hannu. Mika mata idanun yayi ya koma wurin dan uwansa. "Maina zai kashe ki!" "Na yarda da soyayyar shi a gare ni gaskiya ce, idan da karfin irin wannan soyayyar da ya dawo da ni daga duniyar da kika ajiye ni. Maina ba zai tab'a barin wani ma ya tab'a ni balle shi kanshi. Yana sona so matuka naga haka kin nuna min yadda ya fita hayacinsa wanda ya min haka ba zan manta da shi ba. Kuma xan yi hakuri ba zan sake fushin da zaki dawo gare ni ba." "Tunda ba zaki bani idanun Sainah ba, na dauki daya daga cikin Yaranki!" "A'a!" Tuni tayi b'acewarta, ita kuma iskar ya dawo da ita , idanun suka b'ace, jikin Maina ta sauka ta rungume ta. "Garin babu lafiya an sakar da iskar guba!" A hankali ta ce mishi. "Ina Ummimi!" "Tana can suna kewarki!" Maranta ne ya fara ciwo. "Sultan muje!" "Ba zai yiwu ba iskar garin a gurbace ya e!" "Sauke ni tow," sauke ta yayi ta matsa daga gabanshi. Watsa hannunta tayi tuni sai ga ara ya shiga tsakaninsu. Ta dafa ara. "Jira ni nan zan dawo yanxu." "Layla!" "Yadda ka iya fitowa domin na, nima zan baka kyautar da zata gyara maka alkaryanka!" Ta fada tana gyara muryanta. Fitowa tayi daga dakin zata nufi stair iska ya auketa can. "Sannu Kalya!" Ya kaita waje, garin yayi wani irin duhu duhu. Rike kunnenta tayi tare da lumshe idanunta ta fasa wani irin ara da ya zaga kaf garin Baihak babu idan da ba aji wannan karan ba, ita kanta da tayi karan sai da jini ya fara zuba daga kasanta da hancinta. "Layla cikin jikinki!" Inji Kalya. "Tal ta dauka!" Ta fada idanunta rufe. Ta kuma fasa wani aran a karo na biyu, a hankali garin ya fara washewa. "Amma wannan aikin yafi arfi suma su hada da Ubangijinsu zai kawo musu auki!" Inji Kalya tana rungumar ta saboda ta fadi sakamakon jinin da yake zuba a jikinta. Sama tayi da ita zuwa dakin, suna shiga aran ya B'ace. Amsarta yayi suka fita ta sakar masa murmushi. "Muje yanzu kowa zai iya rayuwa." Fita da ita yayi, yana kallon yadda jini yake zuba a jikinta. Yasa shi fita a guje, yana kallon fuskarta. Kafarshi ma ko takalmi babu haka yake gudu. "Sultan kayi a hankali." "Tow tow!" Ya rufe ya rasa ina zai kaita kawai ya wuce da ita bangaren Ummimi, suna tsaye kan Sainah da take kuka idanunta. Yana shiga da ita suka nufe shi.." Alhamdulillahi!" "Ammar Salahudeen ku wuce da su asibiti." Haka suka nufi asibitin har da Sainah. Koda suka isa asibitin labarin abin da ya faru ake badawa. Kafin wani lokaci labarin ihun Layla yasa nata fadar shi. Likitocin sun yi mamakin da cikin bai zuba ba, amma har lokacin jini yake zuba. Idanun Sainah kuma sun rufe mata shi akan nan da kwana uku za a bude mata shi. Shi kanshi Maina da aka gaya mishi kome faduwa yayi domin ya gaji. Sai da aka saka mishi ruwa. Ummimi take tsaye akansu Malik ma yazo yaga halin da suke ciki. "Ya Layla din?" "Da sauki!" "Allah ya basu lafiya!" "Amin Ya Allah!" Haka ya dawo gida. Cike da jimami, a parlourn shi ya sami Queen Hamidah da wasu mutanen!" "Ku shigo min da sauran biyun da suka rage!" Aliyyah ce da Yaranta sai Abraham da Auta Haisam. Kafin Ayrah da danta. Lady Hidaya itama aka turo su. "Na fahimci ba zaka bani damar mulki ba, ka kira Maina yazo da yarinyar nan!" "Mother akan me?" "Arhhhhh!" Auta yayi wani irin ihu, tare da faduwa wayar ta fadi can. "Queen kira yayi!" Inji wani mutum katon gaske. "Dauko wayar na gani!" Mika mata yayi. Ta fara duba sakon. "Idan kun ga sakona ku gudu don ceton rayuwanku, kome ya lalace a nan an yi juyi mulki wa Abba Queen Hamidah!" "Ku tabbatar kun dauko min Layla Da Maina! Su kuma kuyi isolated dinsu, baki aya har sai na nime su." Abin ya matu ar d'aga hankalin kowa, Aliyyah me fada akan miji gata a hannun Queen Hamidah. Lokacin da sakon Auta ya isa musu, babu b'ata lokaci suka bar Baihak domin kuwa sun san zata saka a biyo su. Haka yasa basu tsaya a bai haka ba. "Ina zamu?" "Garinsu Ummimi!" "Bai yi nisa ba?" "Muje!" Haka suka bar bai haka domin kula da lafiyarsu Layla da Sainah. .. ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/28, 10:46 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________66 "Zuwa yanzu ya dace Malik ya san wacece Hamidah domin ba mahaifiyarshi ba ce, uwar da ta haife ka bazata maka wannan kullin ba." Juyawa Ammar yayi yana kallon Maina da mamaki domin bai ta a jin labarin irin wannan ba."Ban fahimta ba?" Murmushi Maina yayi sannan ya ce musu. "Idan muka tafi garin su Ummimi Hamidah zata takale su da yaki, amma mu tsaya a garin hutara!" Cike da mamaki ta suke kallonshi daga haka basu kara magana ba, tafiyar awa tara suka yi kasancewar garin kauye ne sosai. Sannan suka parka a kofar wani gidan, dake dare yayi sosai amma Maina ya fito daga motar ya buga kofar gidan. A cikin gidan wata dattijuwa ce ta bude kofar dakinta, ta fito tana fa in "su waye haka a cikin wannan daren? Maina?" Ta kuma kiran sunanshi. "Na'am abar kauna!" Ya fada yana gyara tsayuwarshi. Bude kofar tayi tana me haska fuskar shi da fitilar kwan da ta fito da shi. Murmushi yayi yana fa in. "Ban cika miki alkawarinki ba, Hamidah ta koro mu!" Ya fada yana riko hannunta har wurin motar. "Kai amma dai baka da kirki shine ba ka ce min da mutane dayawa ba, maza ku shigo dare yayi sosai." Ya fada tana make kafadar Maina. Yadda ya koma ga rungume ta yana fa in. "Abar kauna daga ke ba kari, sarauniyar baih..." Juyawa tayi ta make kanshi domin ita ma akwai tsawo don dai ya hadu da shekaru sun ja har tayi doro, bude motar su Ummimi suka yi duk suka fito daga motar. Suka nufi cikin gidan, da girmamawa ta kai Ummimi da Layla Maina ya dauko ta, Sainah Ammar ya dauko ta. Salahudeen yana bayan Ummimi saboda tsaro da bindigarsa. *** Yadda Auta yake kwance baya numfashi yasa, Malik nufar shi tare da d'ago shi ya daura kanshi a cinyarsa. "Haisam!" Ya fada yana girgixa shi. Amma har lokacin Auta bai motsa ba, sake girgiza shi yayi amma bai motsa ba, matsawa Abraham yayi yana fa in.."Yaron nan mutuwa yayi fa!" "A'a bai mutu ba, plus dinsa yana bugawa ka duba hannunshi." Inji Malik din yana kara rungumar Auta. "Tashi kaji ina tare da kai. Babu abin da zai same ka." Ya fada hawaye na zuba mishi, ya rasa fahimtar nadama ce tazo mishi ko kuwa kawai tausayin yaron da ya rasa Uwarsa daga haihuwarsa. "Kayi hakuri Malik Yaron nan ya mutu!" "Na gaya maka bai mutu ba!" Duk suka koma da baya, sakamakon yadda Malik ya daka musu tsawa, sai yanzu yasan yadda kowa yake jin zafin idan an tab'a na sa, yanzu ya gane duk mutanen da yayi sanadin ansu yadda suke ji, domin wanda bai ji ba bai gani ba tab'a shi akwai tashin hankali. Musamman Haisam da bai san kome ba. Takun Hamidah yaji zubawa kofar idanu domin a wuri guda aka tara su. Bude mata kofar aka yi ta shigo. Murmushi tayi tana fa in. "My boy!"
Chapter 97 · 0% Book details