← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 115

Sashe 98

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hadiye yawu bakinshi yayi yana kallonta. "Kace Maina ya dawo a duk inda yake! Ya kawo min yarinyar nan idan ba haka ba zaku fuskanci ukubar da zata saka ka roki mutuwa na hanaka" "Maina ba zai dawo ba. Rayuwata fansa ce akan Maina da Layla!" Inji Auta da ya tashi yana rike kanshi saboda jinin da yake zuba a keyarshi. "Kai bawa ba da kai nake ba, da Ubanka nake." "Eh saboda na ke ce kika haife shi ba, wacce ta haife shi tana can." Mikewa zubur Queen Hamidah tayi tare da tsayawa kafin ta ce. "Ku gyarawa Yaron nan zama!" Zubewa Malik yayi a gabanta. "Zan kira shi, kiyi hakuri kin ga halin da yake ciki!" "Cilla mishi waya ta yi tana kyalkyalwa da dariya. "Ni ce na baka Baihak a hannunka. Nice na baka damar yadda zaka yi a Baihak amma kake nuna min iyakata." "Ki yi hakuri dai!" Yadda yake bata hakuri yasa ta saka aka kyale Auta. Malik bai da wani za i ya kira Maina sai dai wayar bata shiga. Kallonshi tayi tana zaga dakin tana murmushin mugunta. "Zan auki yarinyar can, na kaita wa mutane na, su tsafe min ita bayan sun mata abin da kakanta yake yiwa Yaran mutane. Ina ga haka zai saka Maina ya zo daga duk inda yake a fadin duniya. " k'amkame Sanah Aliyyah tayi wani irin tsoro yana shigarta. Batan lokacin da ta fashe da kuka ba, gara ta ga gawar Yarta da wani ya lalata mata rayuwar Y'a. "Ku dauke ta " ta fada tana me nuna musu Sanah. Tsayawa Malik yayi a gaban Aliyyah, Haisam da Abraham. "Ku fara kashe mu kafin ku isa ga Yarinyar!" "Wai duk akan yarinya daya? Tow fa." Inji Queen Hamidah. "Kai Abraham bani da lokacinka, shi kuma Haisam bari na gaya maka wannan abin da kake ba zai tab'a baka wani abu ba, mulki ko tow Malik shi ya kashe Mahaifiyarka." "Na sani, amma ai Malik bai kashe Ummana ba sai da goyan bayanki. Don haka ki fara da ni!" "Kai dakaru ku kashe min duk wanda ya hana daukar Yarinyar." Ta juya ta fita su kuma dakarun suka nufo su a fusace da wasu irin makamin dukar mutum. Sai dai kafin su isa gare su wani irin haske me karfin ya shiga tsakaninsu daya daga cikin dakarun da yayi yunkurin shiga hasken daskarewa yayi kafin ya fadi yana me tarwatsewa kamar an fasa ara akan floor. Ja da baya suka yi suna masu jin tsoro sosai . "Ku kwantar da hankalinku, babu abinda zai same ku da yardan Allah, ku dai ku kasance masu imani da Allah ku kuma cigaba da niman tuba, sannan kada wani abun da Queen Hamidah zata yi ya baku tsoro ku yarda da Allah. Malik ina mika maka ta'aziyar rashin da kayi me zafi da ba zaka sake samun gurbinsa ba Allah ya jikan magabatanmu!" " wacece ke?? Kuma waye ya rasu!" "Ni Ko? Sunana Hafsatul ikram binti Sheikh Imran Kisra! Zan tafi kada ku fasa addu'a domin ba a fushi da addu'a, shi makiyi yana iya zuwa maka ta yadda baka zata ba. Amma idan kayi hakuri da addu'a Allah zai amsa maka." Daga haka ta juya ta bar dakin. Sarawa kan Malik yayi shi duk a tunaninshi Haisam ne ya mutu, amma ina wannan ba haka ba ne a wannan kifar da mulkin da Hamidah ta saka yi, ta tura gidan Wazir Abu Ammar, garin ya kare kanshi da iyalinsa aka kashe shi, yanzu haka Matar Salahudeen da Ammar suna hannunta. Sannan abin bai tsaya ba, har gidan Galadima ta tura, aka dauko mata shi . Dake bai yi gardama ba. Fitar Hafsatul ikram, dakin da aka ajiye matar Salahudeen da Ammar ta je suma tayi musu iyaka da sharri Hamidah. A can bangaren Hamidah jin shiru shiru yasa ta kuma aikowa, sai dai haka ya ara faruwa da wani, kai da ta ga babu wanda ya kuma dawo mata da abin da ya faru, kawai ta zo da kanta sai dai tana yunkurin tab'awa taji kamar an watsa mata wuta a jikinta da sauri ta dauke hannunta. "Kun zata wannan shine karshen? Lallai Malik kayi da yar halak!" Duk yadda taso cutar da su amma abin ta ci tura. Da asuban fari suna nufi masallaci, bayan sun dawo ne suka kara gaisawa har zuwa lokacin Layla bata farka ba. "Abar Kauna ga Ummimi na!" "Wannan Salahudeen, shi kuma wancan Ammar Husainah da Aisharka!" Shafa kai yayi yana fa in. "Matar nan kin fara duba ne?" Make shi tayi tana me mikewa ta ce mishi. "Dake nayi maka kama da bokanya ba;" ta nufi bangaren kitchen din gidan, dama haka kawai jiya ta saka aka yanka mata katon ragonta, tayi sadaka sauran ta hade shi a tukunya ta dafe shi da kayan kamshi. abin karyawa tayi tare da dafa farar shinkafa. Sannan ta juye rabin namar ta kawo tana me ajiye wa sannan ta kuma riko kunnen Maina. "Zo ka taya ni!" Ya shiga kitchen din zai dauki namar cikin tukunyar ta make hannunshi. "Acici!" "Abar kauna har yau bana jin dadin abincin kowa daga naki sai na Ummimi sai jagwalgwalen Layla!" Girgiza kai tayi tana fa in. "Aliyyah fa?!" "Eh ba laifi na ta." "Ka zama Adali ba ace kada kaso matanka ba, amma ka koyi yadda zaka boye darajar kowaccensu.!" Gyada kai yayi ya fita da abincin, ya ajiye su a parlour sai lokacin Layla ta tashi da taimakon Ummimi tayi wanka ta gyara jikinta, sannan ya fito tana me zama a can gefe guda. "Dawo nan!" Inji matar, komawa gefen Maina tayi inda matar ta nuna mata. "Me kike so a zuba miki?" "Naji kamshin dafuwar shinkafa ita nake so da miyar naman can!" Murmushi Matar tayi ta wuce kitchen din ya zubo mata yadda zata ci har ta rage. Haka ya ajiye mata ta fara ci maina ya kai cokali zai tab'A mata, ta buge hannunshi. "Kai Papa ba zaka bar ni nayi kiba ba." "Ina son naji yadda dafuwar take da miyar!" Layla ta make hannunshi, tana b'ata rai. "Ummimi abar kauna, ku bata hakuri ni ne na janyo tai samu matsala har da Sainah!" Shiru tayi kanta a asa, idanunta yana kawo ruwa. "Amma me yasa Maina? Kai da nake maka kallon mutumin kirki." Inji Matar nan, "Mutumin banza dai, mara bincike baki aya abin da aka gaya mishi yake aiki da shi." Inji Ammar yana kwada mishi harara, Kallonshi Maina yayi a matu ar gajiye domin duk lokacin da ya tuna abun da yake gaya mishi kenan. "Me yasa baka da mutumci?" "Ummimi!" Ammar ya kira sunanta. Sai kuma ya rike kirjinshi da yake bugawa da karfi da karfi zuciyarshi kamar zata yi waje. "Lafiya?" "Zuciyata ce ta tsinke kamar wani abu ya faru, zan koma Baihak!" Mikewa Layla tayi kafin tace musu. "Allah ya baku hajurin rashin da aka muku, sannan zaman ku anan ba zai yiwu ba. Domin mutanen gida suna bikaatrmu.", "Wacce irin magana ce haka?" Inji Maina. "Da gaske Papa Baihak tana bukatarmu, kuma dole mu isa Baihak kafin faduwar ranar yau!" "Babu inda zaki!" Inji Maina. "Zaka zo ka same ni a can domin xan tafi!" Ta sake labulen dakin. Mikewa yayi ya nufi dakin.yana d'aga labulen ya zata tafiyar tayi sai ya ganta zaune tana kuka. Shiga dakin yayi ya zauna. "Me yasa ki kuka?" "Mahaifin Ammar an kashe shi, Auta yana cikin wani hali. Baki daya babu Amince a cikin Baihak rayukan kowa yana cikin dar-dar." "Me Hamidah take bukata!" "Ni da kai Sultan iya mu take bukata." "Iya mu kawai?" Gyada kai tayi tana shashekar kuka. "Tow me yasa kike kuka?" "Tsoron kada wani abu ya same ka ne nake kuka. Idan wani abu ya same mika ban san ya xan yi ba." Rungume ta yayi yana buga bayanta. *** Ajiye wukar Tirsila tayi tana fa in. "Gani nayi wuka ce babu abin da zai mata." Dauka Queen Hamidah tayi itama tana juyawa kafin ta ce musu. "Meye amfanin shi? Bayan ba wani abu zai iya mana ba!" Murmushi Falwa yayi ya ciro wani kwalba ya bude kwalbar hayaki na fita ya zuba a jikin wukar take wukar tayi wani irin haske sannan ya ajiye musu. "Na gama hada wukar matukar ta yanki Layla tow ba makawa mutuwa zata yi a tabbatar ya yanke ta domin shi ne abin da ake bukata." "Amma ka kawo shawara me kyau!" "Tow yanzu ya zan yi da jinin da Ruhi yake bukata?" "Haka zamu bazama cikin gidan sarauta a nimo wacce zata mutu yau tunda Malik da iyalinsa ba zasu tab'u ba. Hadiye yawu Queen Hamidah tayi ta ce musu. "Na rasa yadda aka yi haka y faru, lallai idan na kama Layla sai na mata yankar rago!" ** A bangaren Malik kuwa Jinin auta yana ta zuba. Baki aya fatar shine kada wani abu ya samu auta. Bayyanar Hafsatul ikram ta cewa Abraham. "Zo ka auke shi, mu tafi da shi asibiti!" A r azane ya tako har wurin domin basu ganin fuskarta saboda gaske amma suna ganin kayana da suka kasance Farare....... *Tun ranar Alhamis nace ba xan samu yin typing ranar juma'a ba, kuyi hakuri ni kaina ban san labarin zai rike ni haka ba idan nayi rushing labarin can make sense don haka ayi min hakuri in sha Allah zan yi kokarin kafin nan da wasu kwanaki na kammala!* ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/30, 9:51 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________67 Rungumar Auta Abraham yayi, suka b'ace lokaci guda ba a kuma ganinsu ba. Ajiyar zuciya Malik ya sauke yana kallon iyalinsa a wannan halin yana me fatar Allah ya kubutar dasu baki aya. A duk inda Maina yake Allah ya kare su. "Ni da na sani na bi su Auta da aljanar nan." Inji Ayrah da tayi zuru-zuru tsabar tsoro. Babu wanda ya tanka mata asalima banza da ita kowa yayi domin dukkansu kowa ta kanshi yake waye zai iya mata balle har ya biye mata. "Shegu Mayu Queen tana zuwa xan ce ta auke ki da yarki." Hadiye yawu
Chapter 98 · 0% Book details