← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 115

Sashe 18

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi sosai ya ce mishi. "Mutum irin Maina wanda magana bata dame shi ba, idan yayi magana tabbas duniya zata yarda, rashin maganar Maina masifa ce, haka maganar shi kamar ukuba ce da zata iya kawo juyin juya hali." Tabbas Maina kamar dutsen wuta ne me aman wuta daga lokaci zuwa lokaci. Idan har Maina da yake da hujjojin fa a haka yayi shiru tow wallahi babu wanda ya isa magana, don haka zai kai Maina wurin Mahaifiyarshi. Ta shiga tsakaninsu da Maina. Wagaduwada. Zubawa Tirsi idanu Sanaya tayi, tana son tantance abun da ta fa a mata. "Ban gane me kike nufi ba? Kina nufin yankan baya zaki yi haba Kaka." "Ke ki min shiru duk abin da nake domin ki nake, idan don kaina ne tuni an wuce wurin." "Kinji na gaya miki ina da buri ne? Ko na ce miki ina da wani akida ce da zata bun asa duniyata? Kin yi kuskure babba ni ba zan goyi bayan abin da kika yi ba, na rantse da Uwargijiya ba zan yarda da haka ba." Inji Sanaya. Mamaki cike a fuskarta ta ce mata. "Ni zaki kubcewa zani a kasuwa? Don waye nake wannan faffutukar an gaya miki bani da buri ne akanki?" Girgiza kai Sanaya tayi tana kallon yadda ranta ya b'aci. "Ni ba zan bi bayan rashin gaskiya ba, don haka duk abin da ya faru ba zan yarda na kare ki ba." Rintsa idanun tayi tana mamakin yadda Sanaya ta rufe idanu tana tafka mata rashin mutunci. "Kenan duk abinda nayi a banza ne?" "Ni dai ban ce ba, amma su wanda kika yi domin su ba lallai su jibanci alamarinki ba, sannan ni bani da tsimu bani da dabarar da zan kare kaina a wurin Layla da Kaka Jami, sannan al'ummar Wagaduwada suma ba zasu kyale wannan zalincin ba, wai me kike bukata? Me yasa ba zaki bar kowa ya huta ba. Ina jiye miki kada reshe ya juya da mujiya domin idan baka iya kama barawo ba, shi zai iya kama ka." Daga haka ta fice daga dakin domin babu amfanin biyewa son zuciyar Kakarta, ita bata san yadda zata rinka kome a hankali ba, kome wuta-wuta take cin shi kamar masifa, don haka ta wuce ta bar ta nan sake da baki. Tana fita Tirsila ta shiga dakin halwanta, ta fa a ciki kamar kamar zata mutu,can wani dan tsabunburin mutum ya bayyana da muryan shi kamar ta gyare ya ce mata. "Tirsila ruhin da yake tare da ita ba zai barta ta gane gaskiya ba, idan har kina son ta baki goyan baya sai nan da wani lokaci mu fito mata da salon da ba zata kwace mana ba, ungo wannan ki shayar da ita ba zata kara miki musu ba. A dankwafar da zuciyarta lallai ta amshi batunmu." "Duju ina jin tsoron kada wani abu ya taso na kasa kwatar kaina." Juyawa yayi yana dariya da muryan nan kamar ta gyare ji kake yana wani bada sautin "ki-ki'ki" ya kalle ta kafin ya ce mata. "Ni bana tsoron takife, kuma ba zasu iya ba daga yau har zuwa lokacin da kome zai kammala ki cigaba da tsuma kanki da jikarki. Zamu bawa kowa mamaki." ---- "Kiyi hakuri ki bamu kayanmu!" Lekowa tayi tana kallonsu kafin ta ce musu. "Yo me zan baku?" "Haba Layla tuntuni muke rokon ki bamu kayanmu kin ki zamu gayawa Kaka Jami." Lekowa tayi sannan ta ce musu. "Zan baku kayan ku, amma so nake idan kun gama wankar sai ba ku." "Mu dai mun gama!" "Kayya ku cigaba!" "Layla dare ne yake yi me yasa kike mana haka ne?" "Ba fa zan bada ba!!" Haushi ya kama daya cikin yan matan ta mike, ai kuwa Layla ta kwashe da dariya. "Laa kuzo ku ga mace tumbur!" Da sauri ta koma cikin kudidifin, ta tsuguna. "Amma dai Uwargijiya ta yi tir da ke Layla!" "Sai kuyi kuma!" Tattara kayan tayi tare da watsa musu cikin ruwa ta dire daga bishiyar ta arta aguje. Bata tsaya ba sai a wani makabarta, tun daga nesa ta hango kamar Tirsila. Tsayawa tayi sosai tana kallon yadda take hak'a sabon kabari. Kallonta take a tsannake. Kafin ta cigaba da tafiya abinta, har tazo jikin Makabarta. Tirsila ta d'ago suka yi ido hudu da Layla, da sauri ta sunkuyar da idanunta. Kafin ta sake juyawa sai ganin Layla tayi a bayanta. Wani irin tsoro ya cikata ta juya da baya. A hankali Layla ta cigaba da rufe kabarin. "Duk da baiwa da tsafi da muke da shi, ba zan lamunci hana masu barci barcinsu." Ta fa a tare da d'ago kai gashin kanta ya tashi tsaye, idanunta ya koma fari tass. "Kada ki sake na rufe bakina ba ki..." Kafin kace kwabo Tirsila ta b'ace. A hankali ta karasa rufe kabarin sannan ta shiga juya hannunta, a hankali guguwa yake tashi har ta samu damar sarrafa wasu irin kayoyin tsafi masu matukar dafi kamar muganyan maciji, sannan suna dauke da wasu irin shud'in fure da korayen ganye masu kyau da ratsin rawaya. Tare da manyan alasuman tsafi me karfi ta kange makabarta yadda wani bai isa ya shiga ba sai da izininta. A hankali ta fito daga makabarta lokacin garin yayi duhu, takawa take kamar wacce tasha wani abu, har ta isa Majami'a, a bakin kofar majami'an.ta zube tana aman wani ba in ruwa da hayaki. Ravi ya fito kenan daga majami'an ya kunno wuta, kawai ya ga mutum a yashe. "Kai Layla!" Ya fa a da karfi, jin muryan Ravi yasa malamin majami'a juyawa da gudu zuwa bayan majami'a sake zawo, ai zuwan Layla a wannan lokacin gara a tashi garin da yaki, sake jin muryan Ravi yayi yana fa in "Malam kazo ga Layla!" Yasa malamin majami'a sake yunkuri sake kashin sa, ji kar "fatseeeeee! Kurrr tuttutu!" Yana yi yana gumi yana fa in "Uwargijiya kome zasu yi ba zanje ba, haba yarinya dai kace Annoba." "Malam!" Ji yayi cikinshi ya sake murd'awa haka yayi ta katse cikinshi da tsoron Layla. Ganin babu kowa Ravi ya juya ta goyeta, tare da rike fitilarsu, har gidan kaka Jami da take bakin kofar gida, tana jiran dawowarta, ga kofar gidan ta cika da Mutane. Tirsila tana kallon yadda kaka Jami zata yi handling case din Layla a wannan daren. "Ku bani hanya ku bani hanya." Ya shigo da ita har gaban Kaka Jami. "Haeda amshe ta!" Karbata tayi, ta kwantar da ita a kasa. Yadda kaka Jami ta zuba mishi idanu yasan tana son ta ji me ya faru da ita ne, sai dai shima kafin ta bude baki ya yanki jiki ya fad'i. Yana shure shure. Rike cikinshi kaka Jami tayi ta matse ruwan cikinshi wani irin hayaki ne ya shiga fita da gudu, kafin ta buga sandarta da kasa, hayakin ya dawo jikin sandar a guje. Dakyar ta tashi tsaye. "Tun bayan abinda ya faru ga Wada, an samu uwayen gijiyoyi sama da goma, Tala ita ce yau ta farka a jikin Ravi ban san yadda aka yi ta farka ba, amma tabbas wannan lamarin ba zai mana kyau ba, Ya ku al'ummar Wada, ina son ku sani farkawar daya daga cikin Uwargijiyoyinmu, yana nufin nan da dan wani lokaci masifa zata afko mana, ba hada ku da abin bauta kada wani ya kara kawo mana tashin hankali. Wannan masifar da zata nufe mu zai iya haifar da zuba da jini wanda haka zai iya kawo karshen alkaryan mu. Ina me rokon duk wanda yake da wata manufa ba sai ya tadda wata uwargiya ba, ya fito ya bar mana al'ummarmu muna son zaman lafiya." "Sai sai idan Layla ce zata fita ta, domin ita ce abin ya shafa Ravi taimako yayi kowa yasan da haka." Kallon Tirsi Kaka Jami take yi a matukar kad'e bata yi tsammanin jin wannan furuncin daga bakinta ba. "Idan har Layla zata fita, zan bita domin bawa Layla da rayuwarta kariya aka haife ni!" Inji Ravi da ya farka cikin tsannanin ciwo. "Duk da Layla bata jin magana, sai dai muna tsoron koranta daga cikinmu, domin Uwargijiya tana bamu sako ta wurinta ne." Take ran Tirsila ya b'aci, ta mike cikin fa a ta ce musu. "Layla annoba ce a cikin al'ummar Wada, ku nisantatta da mu ko kuma muna ji muna gani mu rasa rayukanmu!" "Kaka ki bar wannan abin da kike, Layla ba zata zama masifa ga al'umma ba, na had'aki da Uwargijiya ki barta." "Duk abin da ya faru babu ruwana!" "Da haka kika yi tun fil azal da babu wanda zai damu da abin da kike." Inji wani daga cikin manyan garin. Yayi gaba abin shi. A hankali aka watse, suja shiga da Layla cikin gidan shima ravi aka shiga da shi,magani aka bashi anan Kaka Jami ta ke tambayarshi. "Me ya faru?" Ya labarta mata abin da ya faru, murmushin takaici tayi sannan ta shafa kanshi tana fa in. "Kana da nisan kwana ne, har ka iya dauko ta amma Tala tana da karfin tasirin da sai ta jijiga mutum har barzahu." "Na gode kaka Ya Layla din?" "Layla jikinta babu karfi, zuciyarta tana son mutane wasa da kiriniya ya ci karfinta. Haka yasa uwayen gijiyoyi suke son musharaka da ita, ka tafi gida ka ji" Satin Aliyyah biyu ta koma, Scotland. Duk da yaran sunyi murnar dawowarta amma gogan wani shan kamshi yake shi nan, abin ya motsa don haka tayi ta tarerayarshi, domin zuwanta gidan nan a kwanakin da tayi ta sha gyara ciki da waje. Kwanan da tayi a dakinshi ya gyara abubuwa dayawa da ya kasa boye jin dadin shi, amma halin yaki nuna mata ya wani ji dadi, amma fuskarshi yau a sake take kamar ba Maina ba, wani nishadi yake yana wani bin ta da idanu, ko yayya ta motsa zai d'ago idanu yana kallonta. Yadda kuka san kurma yana wani bin ta da yarenshi me daukar hankali. Shi kanshi yasan ta sauya sosai, wani oukinta yake kamar yau ya fara hada shimfida da ita. Itama bata yarda ta bar shi haka ba, sai da ta cancand'a ado wanda ya kara gigita mishi lissafi, karshe kira yayi ya ce ba sai samu lekawa office ba, zai yi aikin a gida zai tura
Chapter 18 · 0% Book details