← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 115

Sashe 83

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonshi. "Shima sun saka tafarnuwa." "Me kike so?" Girgiza kai tayi ya kwanta tana me lumshe idanu. "Tana da ciki ne?" Bude idanu yayi yana fa in. "A'a babu ciki kawai ciwo ne!" Matsawa Aliyyah tayi ta kai hannunta saman hannun Layla. "Ya kike ji?" "Na gaji, kuma ina jin yunwa amma ban san me nake so ba." "Papa she is pregnant!" "Amma ga test dinta babu ciki fa." Domin a tsorace yake da batun cikin. "Yaushe robonki da last ganin date inki!" Kallon Aliyyah tayi iyaka kafin ta juyar da kai tana fa in. "Ban sani ba!" "Kamar ya?" Inji Maina. " hasale ta kwace hannunta."kin wani damu kamar har cikin ranki kin damu, dalla fita mata a daki munafuncin banza munafuncin wofi, kina tsammanin ciki ne da ita ta ba ciki bane da kike tambayar Hailarta!" "Hilda!" "Masoyi!" Ta fa a tana mika, bayan ta tashi zaune. "Kin ga bata da lafiya ki fita don Allah." Murmushi tayi tare da maida kanta baya "Ba inda zani idan na tafi ma zan dawo ai na gaya maka babu inda ta dace dani sai jikin Layla." "Hilda ki fita nace!" Tura baki tayi tana fa in. "Ka ce Matarka babu ruwanta da Layla ko mu mata rashin mutunci." Daga haka Layla ta koma ta kwanta tare da rungumar cikinta da yake mata mugun ciwo, sai zufa take."Ka gayawa Ummimi?" "A'a!" Cikin azaba ta ce musu. "Sultan cikina ciwo!" "Sannun kinji My dear!" Ya dan duka yana shafa kanta. "Kiyi mana booking yau zamu bar Washington in sha Allah!" Juyawa yayi kan Layla yaga fatarta yayi wani irin fayau.......(Meke faruwa ne Matar Maina? Oya mek una come and buy my Book lol 0472282105 ramlat ABDULRAHMAN Manga gtbank 500 zaku shiga WAIT-LIST faka-faka oooo) [9/10, 10:13 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu Innalillahi WA Inna ilaihirrajiun, wannan filin tana jajjantawa Al'ummar jahar Borno da kewayenta bisa ambaliyar da ya same su, Allah mun tuba ka yafe mana ka kawowa Yan uwa da abokan arzikinmu mafita Ya Allah mun tuba ka yafe mana laifuffukanmu Ya Allah ka dubi albarkaci Yara da tsofin da suke cikin alummar Annabi ka yafe mana Ya Allah mun tuba ka sassauta mana fushinka da fusatarka, Allah mun tuba Ya hayyum Ya Kayyum Ya Allah mun tuba ba ka yafe mana. _________53 aukarta yayi yana fa in. " Muje daga nan ki wuce ki mana booking she need blood again!" Ya fita da ita, Aliyyah tana biye dasu, yaushe yaushe take fada da masifa akan yarinyar lokaci guda Yarinyar ta koma wata irin halitta. Haka ta gayawa su Sanah tana zuwa ga abin da yake faruwa da Layla. "Allah ya sa ta mutu!" Ware idanu Aliyyah tayi ta ce mata. "Don kaniyarki Papanku kika kashe domin sai iya mutuwa shima!" Ta fada tana barin dakin har waje ya samu ya saka Layla a motar ya shiga yana jiranta, tana shiga ta zauna a gefen Layla tana kallonta. "Muje;" ta ce suka bar gidan, asibiti suka fara zuwa ya bata motar ya shiga da Layla. "Amma idan nayi booking din zan dawo nan sai ka koma gida!" "A'a ki je kawai ki fara shirin kafin mu dawo!" Ya fada tana me aukar Layla har cikin asibitin abin ya bawa likitocin Mamaki don haka suka rufa kanta, basu ga wani abu ne tsotsar jinin ba, sai dai an kara mata na Maina dake ya nutsu bai yarda ya saka damuwa a ranshi ba, haka suka dibi jininsa, aka saka mata aka dawo da shi dakin da take ya kwanta. Yana kallonta. Jinin na fara bin jikinta fatarta ta dawo dai-dai, har wurin dare tana sallah kawai yake fitar da shi, sai wurin Asuba ta farfa o, a daren ya kira Ummimi sun yi magana sosai, ya ce mata suna hanya. Sannan koda Aliyyah ta ce mishi zata kawo abinci ya ce ta zauna kawai ta hada kome kawai ta yi parking dinsu a tafi da su gasu nan zuwa. Haka ya faru kuwa domin kuwa gari yana wayewa yayi sallah ya dauki Layla aka wuce dasu airport har lokacin barci take. Koda suka isa sun same Yaran suna ta marmarin ganin su. Layla tana kwance a kan gadon da aka turota domin a motar asibitin suka tawo."ya jikin nata!" "Da sauki sosai!" Ya fada yana amsar yar aramar flast din da ta bashi ya zuba ruwan zafi ne ya fara sha. "Ya ake ciki?" "Eh zamu tafi yanzu kayan za a tura tukun jiya suka tafi da kayan gidan." "Good ;" ya nuna mata hannu bayan ya sha tea, bayan minti talatin jirgin su ya fara niman fasinja haka suka tafi sai da suka fara shiga sannan ya dauki Layla, jami'an asibiti suka dauki gadonsu, yana shiga dama first class ne shi da iyansa nan ya suka shiga ya kwantar da ita. "Papa Mami bata da lafiya ne?" "Eh Nur!" Matsawa tayi kusa da ita. Tana shafa kanta. "Mami ki tashi kin ji gamu a cikin jirgi!" Ta fada tana shafa kan Layla. A hankali ta bu e idanunta ta bu e baki zata yi magana taji bakinta yayi nauyi haka ta hakura ta rike hannun Nuri tana murmushi. Kallon Maina tayi sannan ta sakar mu mishi murmushi me sanyi."Ya jikin naki?" Tashi tayi dakyar ta nuna mishi alamar zai iya bata brush? Brush dinsa da ya saya a asibitin ya mika mata, da toothpaste din, tura baki tayi ta dawo mishi da su, shi ya latsa mata ta mike jiri ya kwashe ta Aliyyah ta ce. "Ka kula da ita kada ta fadi!" Dake kujera na bayan, take ta koma ta fadi a kai. A hankali ta ta kara mikewa. "Ka kaiita mana!" Riko Layla yayi da take tafiya da kyar sai da ya tsaya ta wanke bakinta, sannan ta kalle shi.tana murmushi. "Sannu!' Ya ce mata, murmushi tayi tace mishi kayi murmushi mana." Ta fada tana me e zama zata yi fitsari yana kallonta. "Ba kyau magana a ban daki!" Rike baki tayi sai da ta gama tayi tsarki ta ce mishi. "Tsami nake fa!" "Ban ji ba!" Ya fada yana rikota suka fito daga ban akin ya dawo da ita wurin zamansu suka zauna abinci aka kawo mata ta kalla toma girgiza kai. "Me kike so?" "Babu." Mika mata wata kula Aliyyah tayi ta amsa, a hankali ta ce mata. "Allah ya biyaki daidai yadda kika min!" Ta bu e gurasa ce da sauce din kayan ciki. Bata ci ba ya yawunta ya tsinke. A hankali ta saka hannu ta fara ci. Tana kallon Maina. "Ka ci abinci kuwa?" "Eh!" Sultan ruwan zafi kawai ka sha, maza saka hannu muci!" "A'a ci na koshi!" "Kowa ma yazo muci waye ya sani ko iya farin cikin kenan" bai kulata ba ya kai hannu ta hana shi da kanta take bashi, "Mum kiyi hakuri kin ji" ta fa a tana mikawa Maina abincin, murmushi Aliyyah tayi domin zuwa yanzu ta fahimci irin kishiyarta, ita dai bata san lokacin da tausayin yarinyar ya shiga ranta ba, amma tabbas ta rasa wani hanya kishi ya bi ya gudu. Sannan wani abu da ta fahimta yarinyar Maina ya cusa mata soyayyarshi haka yasa bata damu da kowa ba matu ar Maina yana tare da ita a wuri mantuwa take da akwai wani mutum. Da ta gama cin abincin, ta koma ta je ta wanke hannun ta dawo ta jingina. "Ya dai?" afafuwana ke ciwo!" "Sannu!" Ya fada yana me riko kafar ya fara mata tausa har barci yayi gaba da ita. "Papa meke damunta?" "Sweetie ban san me yake damunta ba, amma jini aka saka mata har sau biyu!" "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah My love!" Ya fada yana kallon Sainah. .. Karfe shida na yamma suka isa, Ammar ya zo ya dauke su, ganin yadda Layla ta fara dukawa da rike cikinta gaban Maina ya fadi. "Ka fara ajiye mu a asibiti!" Haka suka wuce da ita asibiti aka ajiye su. Suna isa wani likita ya amshi su domin yana ganin Layla gabanshi ya fadi, har zai wuce ya fada ya ce musu. "Tun yaushe ta fara ciwon?" "Kwana biyu kenan!" Inji Maina ya fa a, haka mutumin yayi gaba suna bin shi a baya, har emergency aka karbe su aka fara dubata. "Ku duba mana bloodbank akwai jini?" "Ga nawa a duba?" Kallonshi likitan yayi ya ce mishi. "Ka je a duba ka mu gani!" Haka ya wuce suka tafi aka fara duba shi kafin aka dawo da result jininshi ba za a tab'a ba. "An dibi jininka nan kusa ne?" "Eh jiya!" "Kayi hakuri mu ga wani!" "Matata ce don Allah kada a saka mata wani jinin idan ba nawa ba." "Tow amma jinya biyu da ayi !" "Eh na yarda!" "Ku debi jininsa!" Haka aka dibi Leda daya aka zo aka saka mata. Likitan ya ja shi gefe. "Matarka tana da aljanu ne?" Kallon Dr din yayi kafin ya ce mishi. "A'a!" Prince Maina matarka tana da matsalar Jinn! Ko zuwa an jima zasu zuke jinin abin da zan iya taimaka maka da shi zan baka ruwan addu'a ka." Tunda ya fadi haka ya juya ya fita, "Dr ya sunanka?" Duk da ya dan girmewa Maina cikin murmushi ya ce mishi "Jafar Zafir!" A hankali yayi ta nazarin ina ya tab'a jin karshen sunan, haka ya gama nazarinshi bai fahimci kome ba, can su Ummimi suka iso suna zuwa ya tafi masallaci. Sai da ya sauke sallah kanshi. Kafin ya dawo ya samu fatarta ya dawo dai-dai. Abinci Ummimi ta zuba mishi. "Bari ta farka sai muci tare." "A'a ka ci dai!" "Wallahi ba zan iya ci ba sai ta farka!" Shigowar Dr Jafar ya mika mishi addu'ar, "tana farkawa ta fara shan wannan!" "Na gode sosai!" Daga haka ya koma kan Layla ya tab'a kanta murmushi yayi sannan ya ce mishi. "In sha Allah zata ji sauki sosai, and congratulations Maybe har da little prince a tare da ita fa!" "What!! Amma an tabbatar babu cikin fa." "Alhamdulillahi, ku bar maganar a tsakaninmu domin ba kowa Allah zai fahimtar da shi cikin ba, sai wanda Allah ya zab'a!" Daga haka ya fita, karfe goma ta farka lokacin Ummimi tana matsa mishi ya ci abinci, yana
Chapter 83 · 0% Book details