Sashe 88
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kariya!" "Allah shi ne ya kare shi ba ni ba!" Daga haka ta nufi inda ake ta murnan ya kubuta lafiya, amma shi Layla yake son gani. Lokacin da ya fito tana arin isa gare shi, shima yana saurin ya iso wurinta, koda suka isa ga juna ri e hannunta yayi yana fa in. "Na gode!" Girgiza kai tayi tana fa in. "Ban yi kome ba Sultan!" Rungume ta yayi yana fa in. "Na gode sosai Allah ya kubutar dan i ta silarki na gode!" A hankali aka watse a a wurin ya kalli Queen Hamidah da Aliyyah. Janye Layla yayi ta nufe su. "Allah ya kare ni!" Juyawa Aliyyah tayi ta bar wurin dakyar take jefa kafarta domin baki aya hankalinta a tashe ya e, Murmushi yayi yana fa in. "Queen Hamidah akwai matsala ne?" "A'a nayi mamakin yadda abin ya faru ne baka ji ko ciwo ko nakasa ba" "Ga wanda yayi imani da Allah, ba abin da zai faru matu ar ya yarda da Allah." Shiru tayi tana me jin zafin me yasa babu abinda ya same shi. Kasa kasa Layla take kallon Aliyyah da ta cika tam, duk ta nuna mata ta wuce tunanin ta daga inda take ta kwala kira. "Ifraz!" Tayi kamar zata zura a guje. "Baki da hankali ne e?" "Ifraz ne fa!" Ta fada a mugun shagwab'e. "Muje kafin na bata miki rai!" "Ifraz!" Ta kuma kwala kira, tare da jan hannunta. Cak ya dauke ta ba zai iya iskancin Layla ba, da auren shi tana kiran Ifraz. Duk Maina ya zauce haka ya wuce da ita ta cikin dandanzon mutane. Tana kuka da ihu, har suka shiga pavilla dinsa. Ya direta a hankali yana tsareta da idanun. "Don Allah ya isa haka, idan kika bari fushina ya kwace zan kashe dan mutane!" Cikin kukan rigima ta ce mishi "Hmmm kawai don ka tsane ni shine zaka kashe shi bayan bai maka kome ba. Ai ni ce nace ina sonshi!" Tushe mata baki yayi a matu ar gajiye. "Kin san abin da kike yi babu kyau." Ya fada yana tsatsareta da idanun. "Tow Meye nayi?" "Kome ma!" Ya fada yana kai hannunshi kan shafafeen cikinta yana fa in. "don Allah ba don ni ba, ba don na isa ba ko don wannan abin!" "Gaskiya ba a kyauta min ba!" Ta fada tana ture shi. Janyota yayi ai kuwa ta fasa ihu tana kuka tare da ture shi da yakushinsa, ita ba zata yarda ba tunda ya daina sonta gara kawai su rabu ta tafi wurin Ifraz. "Kiyi hakuri kin ji nasan nayi laifi amma ai ke ce kika ce bakya sona!" "Eh Amma kaji farkon hiran ne ko kawai haka naka adalcin yake! A bikina kayan da zan saka matarka ce zata bani don ina shiru bana kula kome sai na zama abin wulakantawarka! Kawai na gaji xan koma wagaduwada kawai." "Amma nace kiyi hakuri!" "Ba wani nan lokacin da kake min na baka hakuri ne? Kawai a bar min kayana nayi masifata, kuma ma wallahi kifi zamu je ka kamo min!" "Kifi dai Layla!" "Shi kenan tunda baka sona!" "Ni bance haka ba muje tow!" Ai kuwa ta saka shi a gaba har wani ramin da ruwa yake taruwa ya cire alkyabar shi ya nad'e kafar wandon ya shiga niman kofin, a hankali bayin masarautar da sauran mutanen da suka zo bikin suka yi ta zuwa ana ganin! "Wai Ni kan baka kamo kifin ba ne?" Ta fada tana tura baki. "Layla zan kamo miki!" Ya fada a gajiye, ai kuwa cikin ikon Allah ya kamo wata tarwad'a. "Hmm gaskiya kayi kokari! Namijin gaske! Ni na fasa cin kifin man! Muje kawai ka dauki mashin din can akayi ta yawo da ni a Masarautar nan!" D'ago kai yayi da niyyar ce mata a'a, amma suna had'a idanun yadda tayi mishi wani kwarkwasa, bai san lokacin da ya wuce ta ba ya je ya amso key ya tashi mashin din. Kafin wani lokaci labari ya karad'e masarautar ga Crown Prince nan yana zuba soyayya a masarautar abin da aka tsinewa albarka, Queen Hamidah har tana tuntube. Tazo ta ganshi da idanunta. Tuni ta saka aka kira Malik koda yazo ya ji me take so kiri-kiri ya ce mata. "Ba xan hana shi ba, idan ya mutu ba shi daya na haifa ba amma tabbas ba zan lamunci tauye kaina da suma Yarana suna da hakkin su rayu da soyayya." Daga haka ya bar parlour gabanta ne ya fadi ba dai shirinta na shekaru saba'in yana shirin lalacewa ne. Tabi bayanshi da idanun cikin tashin hankali. Shi kanshi fita yayi ya hango Maina da Layla suna ta shawagi. "Hmm!" Aka yi gyaran muryan Ayrah ce da danta Jawad. "Baban Jawad ya kake?" "Lafiya!" "Yanzu da saninka Maina yake wannan abin kunyar da yarinyar da bata wuce yar cikin shi ba?" "Ke lokacin da kika amshi tayina ai baki wuce yar cikina ba, sai shine zan hana shi?" "Allah ya baka hakuri, bari na shiga wurin Khamila!" "Kuma idan naji wani abu ya fito mara dadi sai kin gamu da ni!" Daga nan ya wuce yana jin Allah yasa Maina ya kawo karshen matsalar masarautar domin tunda har zuwa yanzu yana raye tow tabbas Maina shine xai karya kome amma ya batun tsoho Zafir!" A gaggauce ya juya yana kallonsu. Tow ai Layla bata da kowa aka ce sannan baiwa ce daga masarautar su Khamila, sannan zuriyar Zafir babu kowa a raye duk sun mutu. Ajiyar zuciya ya sauke, Ayrah tana tashi wurin Aliyyah ta wuce tana murmushi. "Kin tabbata bora, tunda ga yarinyar da ta rike mishi zuciya can yana abin da take so da ita. Ruwanki ne ki kwace Mijinki ko ki zama yar kallo!" Kallon Ayrah Sainah tayi tana fa in. "Sai na gayawa Papa kinzo kina zuga Mum tunda Allah ya gani bata da mugun hali sai da muka dawo kika fara shigo mata da mugun abu wallahi sai na gaya mishi!" "Tow kin gani ba, Layla ta rabaki har da Yaranki sun fi son ganinta da Ubansu!" Ai kuwa Aliyyah ta hau dokin zuciya tayi ta marin Sainah sai da ta fasa mata baki, sannan ta kyaleta. Maina bai dawo ba ya turo Layla da kayanshi lokacin Ayrah tana nan a bangaren. Tana shigowa ta kalle su . "Sainah me ya same ki?" Ta fada tana nufar kofar Maina. "Ke shegiya karuwa. Uban me zaki yi a dakin mijina?" Kallon gefe da gefe Layla tayi cikin hasala Aliyyah ta ce. "Shegiya dake nake!" Tayo kan Layla kamar wacce aka cirata da kasa aka bugata da kasa, ko motsin kirki ta kasa saboda azaba. Murmushi Layla tayi tana fa in. "Bafa da bane da zaki dake ni, yanxu a bayan Mijinki nake kwana don haka a kiyaye ni mutum ce me hatsari!" Ta wuce abinta. "Taya za ace anyi mishi abun bai kama shi ba?" Hamidah ta fada a fusace domin aikin da aka yi an lalata. "Ban sani ba!" "Ayi wani abu kafin raina ya b'aci. A hankali Tirsila take juya ruwan da yake cikin tukunyar da sauri ta ja da baya. Ganin Kalya. "Me ya kawo sarauniyar Ruhainai...... Kuyi hakuri yau na shiga rububi ne amma abi ni bashin na yau gobe in sha Allahu ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/19, 9:34 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu __________57 "Wacece ita?":juyawa tayi domin samun damar amsa tambayoyin Falwa da Queen Hamidah, tukunyar ta fashe da sauri tayi baya tana fa in. "Na shiga uku na lalace, akwai gagarumin matsala!" A rude suka taru a gabanta. "Wacece Amaryan jikanki?" "Tana can wata kyakkyawar yarinya ce mara kunya, ni bana sonta a ha a min kayan farin ciki domin ciki ne da ita, na sadaukarwa gorunfa ya shanye cikin." Da Queen Hamidah tasan cikin a jikin wa yake ba zata fara tab'a Layla ba, don haka Falwa ya ha a mata kayan sannan ta cewa Tirsila. '"kiyi kokarin halarta bikin da za ayi gobe!" "Zan zo!" Inji tirsila. Falwa ya ha a kome ya mikawa Queen Hamidah ta fito daga cave, tana fita Tirsila ta ce mishi. "Ban ci ta zaman ba, akwai matsala." Shafa gemunsa yayi yana fa in. "Matsala ya wuce wancan tasashen ruhin! Me za'ayi da ita ne." Kalfana da aka daure ta da wasu manyan sarkan tsafi. "Zata yi amfani amma yanzu ina da uzuri." Ta fita. * Ba karamin faduwa Aliyyah tayi ba, don haka da kyar ta mike zaune bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba. Taci kuka har ta godewa Allah, Ayrah sai zugata take suna haka Jasy ta shigo ganinsu tare ta ce musu. "Kuyi hakuri!" Ta fita bata kula wajensu ba, ta wuce bangaren da suka sauka ta samu Layla da Bahiyya suna hira shiga cikinsu tayi tana murmushi. "Sannunku!" "Yawwa, sannunki kema!" Yadda Bahiyya take bawa Layla labarin ita kuwa sai murmushi take yana kallon Bahiyya. "Kuma shi kenan sai kika yi shiru abinki, da kinyi magana da zai cigaba daga inda ya tsaya. Ai daga lokacin da kika haukace akan namiji shi kenan ta kare miki, shima da gangan zai ta miki abin da baki so, sannan xan iya yabon Sultan yana iya zama ya biyewa kowaccen mu don a zauna lafiya!" Inji Layla. "Hmm ki bari kawai ba sai ga yarinyar mun zama kawaye ba yanzu ta daina damun Mubarak da!" Dariya suka sake sakawa. Kafin Bahiyya ta cigaba da cewa. "Bro Maina yana kokari amma, zuwa yanzu sai kin tsaya da kafarki domin ba zan boye miki ba son kan Aliyyah ya fara yawa. Bata iya boye son kanta." Ta fada tana kallon Jasy, yi tayi kamar bata wurin tayi ta hidima da wayarta. Kallon Bahiyya Layla tayi tana girgixa mata kai. "Dole nayi magana fa!" Inji Bahiyya. "Ba dole sai magana tayi amfani a wannan yanayin ba, mu bar zancen!" Inji Layla. "Kina tsoron Aliyyah ce!" Dariya tayi tana fa in. "Cab wani tsoro kuma kawai dai bana son shiga hakkinta ne." Daga haka ta mike tana murmushi. Ta wuce dakinsu. Wanka tayi ta gyara jikinta ta saka riga da wando na