Sashe 108
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawo mishi. Komawa gefen hanya yayi ya kifa kanshi. "Jay ka min al awarin zaka bawa abin cikina kariya Allah ya gani ina tsoron zuwa garin nan!" "Haba masoyiya hakkin kula daku yana kaina da rayywata." Hawaye ne ya zubo mishi da ya sani ya barta a wurin iyayenta da yau bata mutu a banza ba. Tasar motar yayi ya bar wurin kasancewar dare yayi sosai. - A can asibiti kuwa Tirsila ce ta nufi dakin da Layla take, tana shiga ta hango Annah kwance tana barci, a hankali ta iso gaban Layla, ta ciro abin da zata soka mata a kahon zuciyarta. Ta nufe ta a hankali ta d'aga abun kenan, kawai Layla ta bu e idanunta da suka yi baki wuluk. Murmushi tayi mata, zata soka mata taji kamar an wura mata sanyi me daskarar da mutum, ai kuwa ta b'ace domin sanyin zai iya hallakata. Lokacin da ta isa gidan kakarin Sanaya taji da gudu ta isa dakin ta ga ai abin da zata sokawa Layla ne ya dawo kan Sanaya wani irin ihu ta fasa tare da nufar Sanaya ta zare wukar da ta mai dashi kamar ittace. Ta rungume Sanaya tana kuka, wani irin ihu take tare da yin kokarin ganin wukar bai shiga cikin zuciyar Sanaya ba. Sai dai ina abin da ake bukata ne ana niman mutumin da zai bada rayuwarshi na Layla ya dawo aka samu. Sanaya kakarta tayi abin da zata yi alhakin ya koma kanta. A can garinsu Kayla tana durkushe taji garin yayi wani irin rugugi, kallon yanayin garin tayi ta ga ya koma dark kara mutsuwa tayi taji jikinta yana wani irin rawa, "Abba!" Ta fashe da kuka me karfin gaske, shi kuwa Mahaifinta yana zuwa cikin kurkukun wadanda aka tura can suka tare shi bayan ya dauki sundukin ya cire jinin Layla ya b'atar da shi kawai ya juya suka lullube shi sai da suka tabbatar ya daina numfashi sannan suka kyale shi, amma kuma madadin sunyi free kamar yadda suke zaton sai aka kara bunkasa musu azabar da ta fi ta da can baya. Sannan asalin masu kula da gidan suka fito da gawar sarki, wanda ran Kayla ya b'aci ta wuce har kurkukun tayi ta kashe wa anda suka kashe Babanta. Sai da ta kashe su baki aya daya, sannan ta binne Ruhin Rihanna a can cikin kurkukun ta kuma saka aka rufe kurkukun har abada. Sannan ta fito da jakar da ta gani na fata, jinin Layla ne, zubewa tayi ta fashe da kuka. A hankali ta kona jinin tasan zamanta da Layla ya kare domin ita ce zata cigaba da mulkin garinsu cikin kauna da begen yarinyar da ta kula da ita tun tana jaririya take hidimtawa Layla, tayi mata fatan samun lafiya. Sannan ta ji a ranta tunda mulki ya dawo hannunta ba zata tab'a yarda ta zauna a haka ba zata koma Addinin Maina domin ta yarda da Allah. Tun zuwan Tirsila ta farka amma ba ita ba ce, sai wurin karfe duhu saura da Annah ta tashi sallah dare ta ganta zaune tayi zugum. "Aisha!" A hankali ta bu e idanunta, duk da tana zaune amma idanunta a rufe suke. "Kin farka ne?" Gyada kai tayi tana kallon Annah. "Ina Sultan dina?" "Ya tafi gida anan muke wuni da shi da tun safe amma an jima ana fitowa masallaci zai zo ya ganki kafin ya kuma dawowa!" "Tow!" Ta fada tana komawa ta kwanta. Alola Annah tayi ta fito tana me shinfida abun sallah ta fara godiya wa Ubangiji sannan ta fara sallah. Sai da aka yi sallah asuba sannan ta cigaba da lazimi har budewar rana, kafin ta juya ta kalli har lokacin idanunta baki ne. Murmushi tayi tana fa in." Aisha baki yi barci ba ne?" "Eh ina jiran Sultan ne kada ya zo ina barci nayi kewarshi!" Annah zata yi magana aka bude kofar dakin, sansanyar turaren shi me bala'in kamshin ya daki hancinta. Tashi zaune tayi tana kallonshi shima cike da mamaki yake kallonta. Wani irin kaunarta yayi ya cika mishi zuciya, a hankali ya taka har ya isa gabanta. Fita a dakin Annah tayi ya rungume gam-gam kamar za a kwace mishi ita. "I miss you Layla!" "Ba ita ba ce Hilda ne na dawo nayi renon cikina ne!" Bai janye ba ya cigaba da shafa kanta, "Layla nasan kina jina, farka gani gare ki kada ki tafi ko bar ni, sannan kada wani ya yaudare ki ina tare dake." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma jikinshi tayi lumo. Kwantar da ita yayi ya fita ya kira likita aka fara duba ta, abin mamaki ya basu amma basu yi mamaki ba, domin sun saba ganin abin da yafi haka. Kuma zasu ga wanda yafi haka matukar akan majinya ne. Batun warkewa Layla ba a gayawa kowa ba, iya Maina da Annah sai Jafar da Malik suka sani sannan Malik ya basu shawara a mai da ita fin era a can ta zauna da Annah da Haeda ana kula da ita sannan Malik ya ce ya raba Aliyyah da ita kowa ya zauna a inda yake kawai hidima yana hadasu domin rigimar Aliyyah yana nasaba da zamansu a wuri guda ne. Kamar yadda Malik ya fada haka kuwa ya faru. Maina ya raba su. Sannan gefe guda Malik ya ara nisanta Layla da Hamidah ce. Bangaren Hamidah babu wani da yake tare da ita, tayi ta niman Tirsila bata same ta ba, haka ta je har gidan ta samu a garkame. Tirsila dai ta maida Sanaya Wagaduwada. Takaici ya ishe Hamidah ta dawo. A can wagaduwada babu wnada ya kula Tirsila da suka ga zata dame su koran kare suka mata da gawar Sanaya. Kamar zata haukace haka tayi ta ihu karshe wasu yan kasuwa suka amshi gawar aka binne, wanda haka yayiwa Tirsila zafi tayi alkawarin tana kashe Layla zata shafe garin wagaduwada. Jafar da kanshi ya nimo gidan da Tirsila take, yasa wasu yan iskann gari suka kona gidan har da sandar tsafinta. Kafin suka maida hankalinsu kan Layla da cikinta wanda Hamidah ta daina jin labarinta babu wanda yake kawo mata wani labari, abin da aka.sani lafiyarta da na cikinta wanda ya shiga wata na shida. Haka rayuwa ta mike cikin wannan yanayin Malik ya fara wani irin rashin lafiya, wanda haka kawai jikinshi yake wasu irin kuraje idan suka fashe wari ko ina yake tun ba aje ko ina ba, Malik.ya fara barin wasiyya. A safiyar juma'a aka kira Ummimi aka gaya mata Bahiyya ta haihu murna da suka yi tayi babu iyaka, koda aka fara shirin suna fir Maina ya hana layla zuwa kamar zata yi hauka haka ta hakura. Ta haifi da namiji aka saka mishi sunan Malik, suna kiranshi da Amir. Haka suka dawo suna tare da kayan suna Layla taji haushi domin taso zuwa sunan. Jinyar Malik yayi tsauri wanda ya saka har Layla ta tafi ta ganshi, kura mishi idanun tayi kafin ta ce mishi. "Abba me ka fahimta a kan ciwonka?" "Jarabawa ce!" "Tabbas Abba jarabawa ce da kuma hakki ka amshi haka hannu bibbiyu Allah zai baka lafiya;" daga haka tayi mishi sallama, bata bar bangaren ba hawaye na zuba mata. Ta d'aga kafa zata fita tamburan masarautar da bai kara kuma ba buga shi da kanshi yake buga kanshi yayi wani irin bugun da sai da taji har cikinta ya amsa. "Abba ya tafi!" Ta furta a hankali, dama dakin Salahudeen ne da Auta suke zaune kuma da ta shiga suka koma daya parlour suka barsu. Tana durkushe a wurin wani irin zufa ke karyo mata, Maina da Ammar suka shigo da gudu sakamakon wayar da Auta ya musu. Ganinta a wannan halin yasa Maina duk ya birkice, domin haihuwa ce ta zo mata gadan-gadan. Haka ya auketa ba tare da ya damu ba, ya wuce da ita bangaren Lady Hidaya, tana ganinsu itama a birkice take. "Crown Prince?" "Mama dubata ko ki saka a dubata Malik." Itama a rikice take don haka tasa yar dakinta ta kira asibiti aka tafi da layla, babu kowa a tare da ita hawaye ne ya zubo mata tana ta fama da azaba har zuwa dare babu alamar haihuwa ga arfinta duk ya are. Jafar da yaji labarin tana asibiti ya saka hannu za a shiga da ita tiyata. Ba tsoro ba ne ya kamata sai dai tana son ko da zata a mata Maina yana tare da ita, har ta cire rai xasu gana sai gashi ya shigo dakin da ake shiryata. Tana ganinshi wani irin karfi da kuzari yazo mata aikuwa ta furta sunanshi da karfi tare da muka mishi hannu, ya ri e ta baki aya kamar wacce ake zare ranta haka taji wannan nishin ya zo mata tayi da karfi sai ga jinjiri ya danno kai, cikin wata irin mutuwar jiki ta ce mishi. "Papa ba xan iya ba;" komawa bayanta yayi tare da rungume ta ya daura kanta a kirjinshi ya ce mata. "We can do it my princess!" Ya fada a kunnenta cikin mutuwar jiki ta bu e baki zata yi magana nurse din ta taimaka mata wurin janyo Babyn bayan tayi nishi da ya hanata magana, mai da kanta tayi kirjinshi tana ajiyar zuciya. "We did it my Princess!" Sumbatar kanta yayi yana fa in. "Sannu kinji!" "Yaw....!" Maganar ya makale ne lokacin da taji kamar wani nishin ya kara danno kai. "P....a...p...a!" Ta fada da karfin gaske sai ga second baby. Anan ne kuma jikinta ya fara rawa, Maina ya kwantar da ita aka mata allura shi kuma ya amshi Yaran yana musu addu'a, sai dai sun yi kankanta dole sai an kula da su. Namijin da aka fara haifa ne ake ta kokuwa da rayuwarsa. Domin Hilda tana Kanshi zata tafi da shi. Itama Layla da bata hayacinta tana rike da danta kuka take tana kokarin boye shi domin ba zata bari wani abu ya shafe shi ba. Wasu haske biyu ne suka bangaje Hilda ta fadi can, sannan suka tsaya a gaban Layla. "ke Hilda daga yau ko inuwarki na gani a cikin Baihak sai na kashe ki, wannan ita ce sarauniyar Baihak tare da Yaranta. Maza b'ace mana da gani." Inji Bintu Yaya ga Hafsatul ikram