← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 154

Sashe 98

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanya ya nuna mata suna tafiya da magana sama sama a tinaninta inda motar da zasu tafi da ita suka dosa sbd batama kawo a ranta daidai wannan lokacin da ake can ana fara hidimar ace Fleet na nan ba dole kila ya isa dan halartar taron.

Mantawa tayi da cewan wani zaa aiko mata ba Imran ba wadda ta yadda da kila Fammah ce ko mum suka aikosa a tafi din da ita tinda wanda akace din zaa aiko ma kila driver ne wanda bata sani ba ita tsoron ma mutanen da bata saniba takeyi.

Hanyar da suka kama kebantacciyar da suna isowa kusa taga securities dinsa a hanyar ya saka gabanta faduwa ahankali ta danso dakatawa sbd takunta dayayi sanyi ta dan kalli imran din tana kasa iya masa tambayar datake cike zuciyarta.

Kofar palon imran yakai hannu a natse ya bude mata bayan sun tsaya cak a bakin kofar wadda ta kasa motsawa bare daga kafarta ta shiga ta kuma qi kallan Imran din dan batason yaga yanayin data shiga na mutuwan jiki.

Daga kafarta tayi a natse da sanyin jiki ta saka a ciki tana shigewa da mataccen jikin da yayi sanyin datake tabbatarda na sauyawan bugun zuciyarta ne dan tin kafin ta sakasa a idanuwanta idanuwanta ke wani irin sanyi da zuciyarta data sauya bugawa da wani irin nutsuwa da samun sukun.

Rufe kofar imran yayi yana barin gurin ya da sake bada umarnin babu wanda zaibi ko hanyar.

Imran kai tsaye ordern abincin daya saka a wani lafiyayyan luxury Restaurant dake da Nigerian dishes a menu nasu ya koma yana jiran isowan order din dan yasan kowace lokaci motar kawo abincin zata iya isowa.

Daidai wannan lokacin Motar Maleek ta sako kai harabar gidan yayi parking tareda fitowa cikin brown kayansa masu kyau da suka zauna jikinsa fresh dashi shima balarabe mai kyau da kwarjini.

Ciki ya shige kai tsaye ya isa har gurin Ammah ya gaidata ya buqaci SANAAH din wadda batanan.

Dakinta akaje aka dubo masa ita amma batanan.

Wayarsa ya daga yana fitowa harabar gidan yana dubata ya saka kiran wayar Ms Meenah dan sanar da ita baiga SANAAH din ba.

Wayar na hannun fammah har lokacin dan haka kai tsaye itace ta dauka da yarensu ya sanar da ita SANAAH bata nan.

Cikin dan hankalinta daya dauku a gurin bikin sosai tace masa ya kira wayarta tana hanun SANAAH din yaji inda take.

Kashewa yayi ya nemo numbern Fammah din ya saka kira wadda tafara ringin a hannun SANAAH datai kasa wucewa can cikin dakin ta kuma kasa juyowa tana tsaye ta rasa gane ma abinda take ji gashi bata gansa ba babu kowa a lafiyayyan qaramin palon da babu abinda yake tashi dai kamshinsa da sanyin Aircon.

Daga hannunta tayi tana kallan wayar hannun nata taga sunan Uncle Maleek din a rubuce dan haka ta danyi tinanin sunan dataji kaman anfada ne zaizo daukanta dan haka ta daga a natse tareda kai wayar kunnenta ta bude baki zatai magana da muryanta mai dadi da zata ratsa wayar zuwa kunnen Maleek din ba tsammani cikin wani slow taji an birkitota a lokaci daya tareda saukan bakinsa a nata ya rufe muryanta da har sautin yafara fitowa.

Wani yarrrr taji jikinta yayi na kaman tsigar jikinta zata tashi gabaki daya sbd kwata kwata batai tsammanin kowaba a tafe bayanta bare shi din...

Dantsen hannuwanta ne a riqe da hannuwansa bakinsa na rufe da nata din yayiwa wani riqon dataji azaba na shigarta sbd kaman ma baisan yana mata wannan muguwan riqon azabar ba dan haka ta dan motsa tana tana son kwacewa amma ba qaramin riqo bane dan haka ta motsa bakinta zata budeshi tai magana amma motsawan da budewan bakin nata akan nasa dayake kai ya saka bakinsa shiga kai tsaye cikin nata yayi mata wata irin tsotsa daya data saka numfashinta fita da wani irin yanayi mai karfi da tayar da tsikan jiki wanda har wayar datake hannunta hakan ya ratsa.

Subucewa wayar hannunta tayi qasa wadda kiran Maleek din yake kai bai yankeba.

Sassauta riqon da baisan ya mata ba yayi yana sake bata wata fitinanniyar tsotsan da kafafunta sukai sanyi suna kasa daukanta sbd duka abinda ta rasa gane kanta a kwanakin suna taso mata musamman dumin jiki na abubuwan da ita kanta tasan sune suke bata wannan yanayin da aka ringa basu suna sha gata jinin be karfin nasu ba.

Jinsa a jikinta ya saka jikinta jin dukannin nutsuwa da samun zazzafan yanayin da batasan ma tana jinsa ba.

Maleek da kansa yayi mummunan sarawa da jin abinda yaji din kasa yadda yayi da kuma cikakkiyar fahimtar me yaji duk da babu kalma ko daya data ratso wayar amma numfashi da nishin dayaji ya sakasa a babban rudani da kasa gasgatawa dan haka ya kashe din ya sake saka kira.

Ringing wayar ta fara wadda kafa kawai Raheem ya saka ya shurata ta bugi bango ta dauke wuta gabaki daya tana fashewa batareda ya saketaba ita kuma sai a lokacin ta dago idanuwanta masu shegen kyau da sukasha kwalli a cikinsu mai kyau daya qara musu wani irin kyau da daukan hankali ta saukesu akan tasa kyakkyawar fuskar datai ja idanuwansa sunyi wani irin jan daya sakata sauke ajiyan zuciya ahankali tana kallan cikinsu sbd sai yanxu ne daya shura wayar ta dan fahimci abinda yake faruwa batasan lokacinda ta daga hannunta daya ba ta dora akan nasa dayake riqe da itaba ta bude bakinta daya dan lalata lipstick dinta da wata irin sanyi da nutsuwa harma da tsananin kewan da batasan tana bayyanaba tace

"Ba wayana bane...." qarasa maganar tayi cikin wani irin yanayin da kuka ke neman taho mata mai sanyi sbd bacin ransa datake iya gani"

Sakinta yayi gabaki daya fuskansa babu kowace irin rahama a cikinta yana juyawa zai koma ciki a karan farko ta saka hannunta biyu ta kama hannunsa daya tafin hannunta na hadewa da nasa ta dan qanqamesa tana sauke idanuwanta akan fuskansa da tana kalla take hawayenta masu dumi suka gangaro mata ta bude baki da muryan son fasa masa kuka tace

"Bansan wayeba yake kiran"

Dakatawa yayi cak da takunsa jininsa wani boiling yake yanajin kaman kirjinsa zai kama da wutar datake ci a jininsa da ruwan jikinsa na da ace nuryanta ya sauka a kunnuwan Maleek din ta wayar baisan mezai iya biyowa baya ba duk da yana kokarin control na hakan dan yasan ba wayar tata bace hakama batasan Maleek dinba....

Kuka kawai ta sake mara karfi da sauta wanda daman ta jima kwanakin hakanan kawai takeson fasa kuka sbd kewa da kadaicin da wata muguwar son dake neman kasheta duk da bazaka taba gane hakan ba sbd muguwar zurfin cikinta da iya danne yanayinta kowane iri ne bazaka taba ganewaba.

Sake hannunsa tayi ahankali zata zare nata kukanta na sake qaruwa da rashin karfi ko kadan ya kama hannun nata batareda ya bari ta zare ba ya sauke numfashi mai zafin gaske daya sauka har akan fuskanta ta rintse ido ahankali wasu hawayen dake ciki suka kuma gangarowa dan zafin dayake cikin numfashin nasa data tabbatarda shine yake cinsa a cikin jikinsa da babu kaya a jikinsa daga shi sai towel ne sbd daga bathroom kai tsaye yana fitowa yaji motsin kofar shigowan yasan itace ya fito.
#MAMUH
09033181070
[07/06, 7:34 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

94
Maleek da wayarsa ke kan kunnensa dip yaji ya dago wayar ya kalla ya sake daka kiran yaji batama shiga,
Sake dannawa yayi cikin matsuwa da tsananin son jinta da matsuwa da ganinta a zahiri duk da yaga hotinanta kuma takowane bangare da siga ta masa ya kamu da asalin sonta da kaunarta bama dan iya son samun alaqantuwa da jeerahs ba.

Kasa samun wayar yayi kwata kwata dan haka ya sake kiran wayar Ms Meenah wadda sai da yayi kusan kira uku tukuna fammah ta lura ta dauka kai tsaye ya sanar mata da wayar bata shiga sam.

"Ok Uncle bara na kira Dad naji sbd na fada masa tana nan ko kila ya saka driver ya daukota"

Kashe wayar tayi ta saka kiran Dad dinta wanda har tayi ringin ta gama baa daga ba..

Sake kira tayi kusan so shida amma sam baa daga ba dan haka kai tsaye ta nemo numbern Imran ta saka kira.

Yana dauka tace

"Yawwa UM Dad baya daukan waya so bansaniba ko anbada mota akawo SANAAH idan baa tafi kaita ba pls ga Uncle Maleek nan ita yazo dauka yanason sanin ko an tafi da ita din"

Dagowa da shegun idanuwansa Imran a natse yayi yana kokarin juyawa daga harabar gidan bayan wata lafiyayyar mota ta kawo masa ordern da suka saka ta dishes din da sukafi guda biyar ya kalli inda Maleek din yake tsaye a jikin motarsa da waya a hannunsa yanata faman saka kira.

Bude baki yayi batateda yace komai ba yacewa fammah

"Zanji da komai"

"Ok thank you UM"

Kashe wayar yayi yana juyawa ya koma ya isa kofar Palon yayi knocking a natse.

Fleet din dake tsaye da SANAAH din dan kallan kofar yayi da jajayen idanuwansa kafin yaja hannunta zuwa cikin asalin Bedroom din da tsarinsa kusan tsarine da akasan yanaso.

A qaida da tsarinsu duk Imran yayi knocking kofar da uban gidansa yake ciki so uku baace komaiba to yana iya shiga dan haka yana gama bugawan a natse bayan seconds bude kofar yayi ya shigo.

Jere komai yayi a table ya juya ya fice ya sake rufe kofar ya koma harabar gidan babu kowace rahama a fuskansa kana ganinsa kaga soldier,

Tin kafin ya isa gurin Maleek din yayiwa wasu securities dinsu dake gate hannu alaman a budewa maleek din gate ya isa gurinsa ya kallesa.

Maleek na ganinsa ya danyi kokarin sake fuska yana miqa masa hannu.

Hannun Imran din ya kama yana katse Maleek din fara gaisuwa yace

"Fammah ta kira,kaje kawai"

Bude masa motar imran yayi da hannunsa daya yana janye hannunsa daya daga nasa yana dan basa hanya.

Kallan mamaki maleek yayi masa yana cewa

"Ina SANAAH din??

Kallansa Imran yayi yana kokarin controlling anger dinsa da batada kyau yace

"Batanan,zaka iya tafiya yanzu??
Chapter 98 · 0% Book details