← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 154

Sashe 93

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Mum ta lura da yanayin nata daya sauya jikinta yayi wani irin sanyi da nuna batada raayin tafiyar dan haka tai kaman bata gane ba sam ko fahimta sbd tafiyar itace maslahar datake fata idan ba hakan ba Hakeem bazai taba dena daga musu hankalin raba aurenba dan haka tafi farin cikin Raheem din ya tafi da SANAAH din kafin dawowansu zata samu ta lallaba Hakeem din yabar maganar.

Dafa SANAAH din tayi da kulawa da kauna mara sirki tace

"Kada ki damar da kanki tinda kinsan baki gama warwareba hakama kada ki takura kanki idan kinje ki saki jikinki tinda ga Raheem nan you'll feel safe ga kuma fammah da itama zata kula dake sosai na sani,
Dad dinki yasan da tafiyar tini kin sani dan haka ba lallai ki samu ganinsa ba yanxu dare yayi hakama da asubanma ba ganinsa zakiyiba ki bari idan kun isa saiki kirasa nima da safe zan masa bayanin kinso ganinsa tinda yasan da tafiyar da wucewan naku"

Shiru SANAAH tayi tanajin jikinta na sake sanyi ta dan sauke numfashi mai sanyi tana gyada kai ahankali wanda ya saka Dr mum sake murmushi tana sake dan dafa hannuwanta da kulawa da jin dadi tace

"Thats my Baby"

Safiya da itama hakan ya mata dadi sosai tana kallan SANAAH da dariyarta da fatan ma kada ta dawo shikenan Dad din fammah ya tafi da ita miqewa tayi ta fice dan hado mata luggage din tafiyan.

Dr Mum cigaba da kwantarwa da SANAAH hankali tayi da wata irin kulawa da kaunar data saka SANAAH jin ta karbi tafiyan a zuciyarta da nutsuwa.

Dr Mum na barin dakin Maamah ta shigo tareda wasu LV suitcases guda biyu marasa girma sosai ta tura gefe tana qarasowa gurin SANAAH din Safiya na bayanta dauke da tray dayake dauke da wani maganin daban da Maamah din ta hadawa SANAAH datake hada mata kullum dan yanayin jikin nata.

Bata tayi tana cewa ta karba tin yanada dumi ta shanye.

Jiki a mace ta karba tana dan bata fuska ta fara sha ahankali maamah din da safiya na mata fira dan hanata shiga damuwan barin gida tin yanzu.

Sun dan jima sosai kafin safiya tai musu saida safe ta fice ta wuce dakinta.

Maamah ma shirin bacci tayi ta kwanta tabarta lafe a kujera tana son yin waya sosai amma ba daman hakan sbd Maamah ce ta karba wayanta wanda da alama kilan ya fada mata hukuncinsa ne.

Dad takeson kira sosai ta masa sallama amma ba daman hakan haka ta miqe ta shiga bathroom ta fito tayi shirin bacci ta kwanta jikinta duk yayi dumin da koyaushe kwana biyun haka yake dan dumi sbd yanayin maganin da ake bata sai ya zamana jikinta baya sanyi ko kadan koyaushe a dan dumi yake.

Da asuba Maamah ce ta tada ita tai wanka da ruwan zafi tana fitowa har Safiya ta dan hado mata light breakfast wanda chips ne da plain egg.

Sallah tafara yi kafin taci abincin kadan wanda Maamah ta sakata ci kafin ta bata magani a cup mai dumi ta sha kadan amma maamah ta sakata shanyewa.

Dr Mum ce ta fito itama ta iso dakin lokacin tini maamah ta gama sakata shiryawa...

Gaida dr mum tayi da sanyin jiki tana qarasa saka ipad dinta a handbag dinta dake gefenta ajiye.

Miqewa tayi ta nufi dakin Mommy wadda bata fitoba tana zaune tana lazimi.

Tana shiga gaidata tayi kai tsaye tana qarasa ta zauna kan sofa tana daukan wayar mommyn dake aje gurin ta nemo numbern Dad ta saka kira kai tsaye.

Bata shiga ba ta kuma sake saka kiran still bata shiga,
Shiru tayi kafin ta sake danna kira babu alaman ma wayar na kashe dan haka ta fara neman numbern Mr Sideeq daidai nan Maamah ta shigo tace tafito Raheem ya kira motocinsu are ready.

Faduwa gabanta yayi da wani irin karfin daya saka jikinta sanyi daga sunansa kadai da Maamah din ta ambata.

Mommy hannu ta miqa ta karbi wayarta tana qarasa adduarta ta kalleta tace

"Ki tashi mana kada ki barsu suna jira,
Allah ya tsare yakai lafiya a dawo lafiya"

Dago idanuwanta da suka sauya take tayi ta kalli Mommyn kafin ta miqe tsaye ta bude baki tace

"Amin" da qaramin sauti a taqaice tukuna ta juya ta nufi kofa ta fice.

Safiya ce ta ja suitcases nata ta fita dasu tin daga nesa security daya ya qaraso ya karbi kayan daga safiya sbd bazata samu daman qarasawa har gurin motocinba dan Fleet din yana ciki already dan haka daga nan ta tsaya cak Maamah ce ta qarasa har kusan gurin mota da ita tin kafin su qaraso aka budewa SANAAH din motar da Fleet yake ciki a zaune cikin wasu fitinannun brown Armanis marasa kauri sosai da suka maidasa kaman saurayi.

A natse ta shiga aka rufe kofar take aka ja motocin suka nufi babbar gate din ficewa wanda tin daga nesa aka wangale musu shi suka fara ficewa da wani irin speed.

Airport suka nufa kai tsaye sai a lokacin da suka hau titin dayake tsit ba mutane sosai sbd duhun asubar taja wani numfashi mara sauti ko kadan na zuciyarta data sauya bugawa tinda lokacinda ta sako kafarta motar zuwa zaunawanta qamshinsa daya gama kama cikin motar gabaki daya ya shigeta take kokuwa da riqe bugun zuciyarta dayake bugawan da ta sani ba nata bane...

Hadiye numfashin tayi tana sake riqe nutsuwa da kamun kanta da rashin hayaniyarta ta bude baki da wani irin sauti mai nutsuwa da sanyinta tace

"Ina kwana?"

Imran da shine yake driving din motar da kansa kuma shi kadai ne a tareda su sake taka motar yayi yana qara wani lafiyayyan speed,

Fleet kuwa da muryan tata ta ratsesa batareda tsammanin zata yi maganar ba sbd yanda ta gujewa duk wata hanyar haduwa dashi ko ganinsa a kwanakin kwata kwata wayarsa dake hannunsa ya dan dakata daga scrolling yana duba sako ya dago a natse tareda juyowa kadan ya sauke mata idanuwansa da suna saukar mata taji kaman an zuba mata ruwan sanyi ta dan qanqame hannunta a gefen rigarta tana hadiye wani numfashin daya sauka a idanuwansa ya qarasa sauke mata kallansa gabaki daya a cikin wani slow da nutsuwa.

Bude bakinsa yayi ba tsammani taji ya amsa a taqaice yana dauke idanuwansa daga kallanta sbd kowace fitar numfashinta da shaqarsa da idanuwansa basa tantancewa hakan yana tabbatarda yana samun matsala dan haka bai sake kallanta ba ya maida hankalinsa akan wayarsa ya bude baki yace

"How are you?
Yaya jikinki?

Wani irin nauyi da kunya ce mai tsanani suka rufeta data kasa iya amsawa da bakinta saidai ta dan gyada kai daqyar ta furta

"I'm ok,thank you"

A cikin muryan nata da bata fito ba sosai yaji kunyarta data basa mamakin gaske ya sake dakatawa yana dago idanuwansa ya kalleta take taji wata sabuwar kunyar me tsanani ta sake rufeta da batasan lokacinda ta daga hannunta daya ta rufe idanuwanta ba tana juyawa da fuskanta gefen windon tana jin kaman zata rasa kanta da irin nauyin datake ji.

Bai iya dauke idanuwansa daga kanta ba sbd mamakin kunyar datake ciki sosai,
Jin idanuwansa akanta kunya da nauyi na neman sakata shiga tsaka me wuyar sani da hawayen da suka ciko idanuwanta ta dan bude bakinta kadan da qaramin sauti tace

"Plss" batareda ta iya juyowa ba bare janye hannunta.

Bai dauke idanuwansa ba da suka kasa yadda da abinda suke gani sai dayaji kamewansa na barazana ya dauke idanuwansa yana dan furta "YA KADIR" da sautin da bai fito ba ko kadan.

Babu wani magana ko doguwan motsi data sake tashi a motar har suka isa airport wanda jirginsu ne zai tashi a lokacin na sauka a lagos sbd acan aka samu ticket na jirgin Morocco din dan haka dole can zasu tafi sai yau da rana jirgin Morocco din ya tashi.
#MAMUH
09033181070
[05/06, 1:07 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

88
Da securities dinsa da babu kowace sauki a lamarinsu indai gurin aikinsu ne  aka bude masa mota ya fito tareda SANAAH din dake gefensa sanye da straight skirt daya lafe a jikinta da rigar da itama take kwance a jikinta bawai matsewaba brown itama sai babbar kimono abaya dake kan kayanta mai kyau da tsadan gaske sai mayafin rigar datai rolling da handbag dinta a hannunta ana biye dasu da kayansu a baya hannunta ya kama a natse sbd lura da bata son mutane sosai Duk da suna tafe ne securities a bayansu da gefensu.
Kai tsaye suna shigewa departure baa bata kowace time ba suka shige..

Koda gari ya waye sosai Mr Sideeq bai shigoba da wuri sai rana sosai dan hakanne babu wanda yasan Fleet ya bar qasar sai securities sai daya shigo securities suka sanar masa baiyi tinanin Dad bai saniba dan haka baiyi gaggawar sanar dashi ba ya shiga office dinsa na villa din dan gudanar da wasu mahimman aikin dake gabansa bayan ya isa ya gaida Dad kenan wanda har lokacin baisan meyake faruwaba.

Dr Mum kuwa tinda taga sun wuce baccinta ta koma sbd tasan Hakeem bazai saniba da wuri tinda bame samun ganinsa sai yamma yawanci ko dare.

Sai da suka hantse rana tafara fitowa sosai suka tashi tai wankanta ta fito ta xauna tai breakfast dasu Maamah suna firarsu hankali kwance anan ne Maamah ke fada mata dole fa anyiwa Dad laifi saita hakura ta tausasashi akan hakan idan ba hakan ba fushin da zai kuma dauka lamarin zaiyi muni.

Ita kanta Dr Mum din tasan da hakan dan haka daman dole zata je da kanta ta tabbatarda baiyi fushin da zai komai zai iya lalacewa ba.

A bangaren daya mommy itadai ta danne ta boye ne amma tana addua da fatan yanda sukaje lafiya su dawo lafiya batareda Ms Meenah ta gane komaiba sbd komai zai iya faruwa acan gwara idan sun dawo anan gaban kowa ta gane zaa iya samun daman bata hakuri da rarrashinta da fahimtar da ita hakama batason fammah taji babu dadi.
Chapter 93 · 0% Book details