← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 154

Sashe 55

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya karbi auren kenan ko me??
Hakeem ya samu abinda yakeso kenan na nuna mata isa da iko ko me?
Ana nufin Meenah wahab kishiyar da basa rayuwa da ita zatai kokuwa itama akan hakan aurenta zai iya zamowa tarihi kamar ita?
Raheem irin abinda Mahaifinsa yayi mata zaiwa tasa matar ta rabu dashi kenan?
Ita tayi karfi da taurin zuciyar zabar rabuwa da hakeem,Meenah wahab bazata iya hakanba dan kuwa zata iya kashe kanta ko Raheem dinma akan ta rasashi ta barwa wata dan haka sam bazata yadda mummunan tarihi ya maimaita kansa ba.

Bata sake cewa komaiba ta shiga tinani mai zurfi dayake cikeda da rashin nutsuwan zuciya da tashin hankali gashi a yanda Raheem din ya yanke maganar idan tace ta bayyanarda nata tashin hankalin mai zafi hayaniyar dazata saka Meenah ta sani ce kawai zata tashi wadda batama son hakan sbd bata kaunar ko kusa meenah ma tasan da maganar yanxu dan itama sbd tana yiwa Raheem tsananin son datasan duk duniya babu macen da zata sosa kaman hakan sedai sbd dukiyarsa da matsayinsa dana familynsa hakama a yanzu daya kai wannan matsayi da girman me zaiyi da wani aure.

Maamah kuwa kokarin jansa da wata maganar tayi sbd ragewa tension din gurin nauyi tana sakewa da kulawa.

Dining tayi umarnin aka hada musu suyi dinner tareda shi sbd suna hakan indai yana qasar ba ruwansu wayewa da ilimi ya ratsa su duka.

Sai bayan ishai sikai dinner hadda Abbu dukansu kuma ko a lokacin saida Dr Mum ta tada maganar auren sbd Abbu ya saka baki amma yanda Fleet din yakame sosai babu kowace walwal ko sakewa a fuskansa da yanayinsa ya saka kowa ya kasa cigaba da maganar Dr Mum ta sake shiga tashin hankali da mamakin me hakan yake nufi kenan.

Washe gari bayan lokacin tashinsa yayi ya tashi yayi wanka da duka abubuwan dayake yi ya fito guraren 11 ya isa bangaren Abbu ya fara gaisawa dashi kafin ya isa gurin su Maamah ya gaidasu babu wanda ya sake kowace maganar data shafi yan Nigeria ma ya fita.

Bai dawoba sai dare ya fita da Abbu zuwa duba businesses dinsa da akeyi a qasar shima na dukiyar daya ware ta harkar zinari,

Da daddaren babu wanda ya gansa sai washe gari.

Maamah ce take kulawa da cinsa da shansa matiqar yana gari duk da yanxi ba itace take aikin komaiba masu aiki keyi kawai dai itace ke bada umarnin komai dan Dr Mum bata wani zama gida kaman ita tana can gurin harkar likitoci dan ita yanzu sun zama manyan da ake komai na harkar qwararrin manyan masana lafiya dasu.

Kwanaki kadan yayi a qasar ya bar qasar wanda ya saka duka iyayen nasa shiga shakkar komaima sbd hakan da yayi shine yake nuna iya girman iyakar dayake son yayi akan zancen auren ga kowa dan haka Maamah ta sauko tareda aje komai ta koma adduar Allah yasa auren nan shine mafi girman alkhairi a rayuwarsa ya kuma kawar da kowace damuwa da tashin hankali da duk zai biyo baya dan kuwa akwaisa duk ranar da matarsa da 'yarsa suka sani.

Dr Mum kuwa duk abinda ya faru shekara da shekaru dawo mata sabo yayi kuncinta da baqin cikinta suka dawo suka ninku sbd wannan abin da Hakeem yayi mata shine karshen baqin cikin dazai mata na janye danta daga gareta ya maidasa Qasarsa cikin hikima hankali kwance.

Daga nan America ya koma dan yana buqatan hutu daga duk wannan tashe tashen hankalin da zaa fara sbd a yanzu abunda ya sani shine wulaqanta wannan auren da zaayi shine zaaga mummunan bacin ran Dad hakama shi kansa yana cikin wani matsatsen daurin da bazai taba iya wulaqanta macen datake zuciyar dan uwansaba ga kuma Dr Mum da itama ya sani bazata taba karban aurenba hakama bazata taba iya saukowaba idan ba sakin auren akai ba sbd batasan wacece matar ba, ga bangaren daya Matarsa da itama yake jin girman sonta da bazai iya hada kaunarta da kowace macen ba kuma bayason hayaniya ko damuwa a gidansa dan hakan baya buqatan tasan komai a yanxu dazai hanasu sukuninsu.

Wannan tinanin da dalilan ya saka ya daukewa kowa wuta har Dad din akan maganar auren ya hana kowa shiga maganar ya barwa kansa komai sbd shine dai mai auren dan haka shine zaisan menene matsayin auren a gurinsa da ita wadda auren yake kanta.

Da wannan duka iyayen da kowama ya danne duk abinda yakeji suka kasa magana da fahimtar ana kokarin kaisa maqurar da kowa bazaiji dadiba.

Ms Meenah da batasan abinda yake faruwa ba sabuwar duniya ta bude ta wata irin soyayya mai zafi ga mijinta wanda tinda ya dawo still hutu yakeyi baya fita koina Imran yayi clearing schedules dinsu na kusan sati hudu dan haka duka masu tsananin son ganinsa Imran suke gani sun ma kasa gane a wace qasar yake yana America ko baya nan sbd babu me iya sanin ina yake idan ba Imran ne yaso ba.

Hutu mai nutsuwa da kwanciyan hankali yakeyi tareda matarsa datake sake jin Raheem jeerah shine rayuwarta da ruhinta da har abada babu namijin dayake da darajarsa a rayuwarta.

Ako yaushe yana kokarin bawa Matarsa daman mallakarsa yanda takeso da bata gamsuwan data riga ta zama Obsessed shiyasa ko kallansa tayi jin takeyi tana sake mutuwa akansa.

A bangare daya kuwa sosai yanzu ta saba dasu mommy da SANAAH sbd Fammah da kullum saisun dauki lokaci suna waya da juna harma da videocall daya saka tasan kamanninsu Musamman SANAAH da ita kanta take yabon kyanta.

Fammah ko Dad dinta babu ranar da bata kiransa tana gaishesa suyi magana sosai amma shi sedai yace yana gaida mommy amma bai tana magana da mommynba awaya bare SANAAH da bata taba damuwa ko bawa lamarin da duk ya shafesa mahimmanci ba dan a ynzu data zama kaman rabin jikin Fammah har abada basa fatar abinda zai shiga tsananinsu dan kuwa lokaci ya tafi sosai sun samu wtaa irin zazzafan shaquwa da kauna mai tsananin da sukewa juna data kasance suna jinsu kaman twins hakama sukejinsu kaman jini daya dan kuwa kusan a yanzu hatta komai nasu iri daya ne sedai kaloli su dan banbanta wanda suma kalolin kayansu da komai nasu basa wuce brown,coffee brown ko Nude kala,

Irin kauna da kusancin dayake tsakaninsu y saka zuwa yanzu babu abinda basu saniba na rayuwar juna wanda gane wacece SANAAH ya saka kaunar da Fammah ke mata qaruwa sosai hakama Ms Meenah tana gane wacece SANAAH ta sake jin nutsuwa da jin dadi alaqarsu da kusanci sosai da Fammah,

Ata kowace bangaren rayuwar luxury suke zubawa cikin zallan gata sbd Dad jeerah kudi sosai ya sakar masu hakama Fleet kudinne yake sako musu,

Mommy kam daman tini ta bawa fammah matsayin da SANAAH take dashi a gurinta babu abinda take nuna mata bayan kauna da kulawa ga yaya Al'amin ma shima ya hadasu sun zama kannensa dayake tsananin ji dasu musamman dayake fammah tafi SANAAH shagwaba sai zamana tana samun kulawa sosai daga garesa fiyeda SANAAH.

Matan gidan su Hajiyar Samad ikon Allah datake gani ya saka ta kusan zarewa abin duniya ya isheta ya sha mata kai jin takeyi kaman zatai zangai sbd son Fammah tasan da wainda take zaune amma tsoron Dad ya hanata magantuwa gashi a yanzu da suka zama aminan juna babu abinda zaka taba iya fada ka sakasu jin tsanar juna a duniya.

Fammah cikin dan lokaci ta koyi abubuwa da dama na al'ada da rayuwan Nigeria duk da su suna rayuwa ne daidai da kaman baa Nigeria din suke ba amma ta samu sauyi sosai a rayuwanta kuma taji dadin hakan musamman da suka samu shiga wasu classes na bayar da qarin ilimin addinin da Yaya Al'amin ya sakasu shiga kuma dad yaji dadin hakan hakama akwai bangaren iyaye da tsofi mata sai suka shiga hadda Mommy 2 hrs ne kullum dan haka sai suke samun rayuwa na tafiya yanda sukeso ga wata tsadaddiyar culinary school da suka shiga sbd dukansu ba wani lafiyayyan girki suka iya ba har gwara SANAAH ta iya irin girkinsu na baya.

***lokaci yayi jan da ake maganar shekara dan haka ya shirya tahowa Nigeria kai tsaye Ms Meenah ta yanke shawarar binsa ta koma Nigeria din itama da zama na dan lokaci tinda yanzu sunada wainda suke kalla matsayin yan uwa dan haka ta nace da rokonsa sbd sam baida raayin zamanta a Nigeria amma ta dage dan haka ya barta sbd baya buqatan hayaniya akan zancen hakama zuwan da ita zai hana mahaifinsa bawa wancan auren daman kebancewa ko wata maganar.
#MAMUH
09033181070
INSHA ALLAH ZAMU GWADA POSTING WEEKENDS MU GANI
[09/05, 8:27 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
Chapter 55 · 0% Book details