← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 154

Sashe 6

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manyanci ya kamasu sosai sosai dukkaninsu sbd rayuwa data ja sosai hakama cigaba yazo sosai dan kuwa babu wanda baya kan babban matsayin da duniya take girmamawa a cikinsu,

Hussain dayake babban dan siyasa saida ya taka matsayin gwamnan jaha guda kafin yayi senator tukuna ya tattara yabar qasar shi da iyalansa suka koma Morocca da zama sbd business dinsa dayake tafiya sosai acan dakyau dakyau.

Hassan ma da Ahmed sun bunqasa sunci sun tayar da kai a fagen tarin dukiya da businesses dan kuwa suma basu bar qasar ba sedai basu cika zama ba sbd zama busy.

Farouk dayake retired soldier yanada dukiyar gaske mai yawan daya mallaka tin daga qasar America din hakama dansa Hakeem dayake can yana cikin dukiyar a wadace duk da aikinsa bai taba basa damar jin kowane irin dadi ba ya duqufa ya sadaukar da rayuwarsa kaman yanda kakansa da mahaifinsa sukai sbd shima baida niyar tsayawa insha Allah saiya kai karshen lamba.

********
A cikin familyn jeerah da babu wanda zaa ambata sunansu yace bai saniba kaf Hakeem jeerah ne baa saniba sbd baitaba fitowa duniya tasansa ba yana duniyar ruwa kuma hakan shine alfaharin da mahaifinsa yakeyi cikeda jinjinawa ya zama hakan,

Sauran ahalin zuriar duka mata ne sbd Alh Ahmed jeerah duka duka yayansa biyu rak kuma duka mata ne hakama dukansu anyi musu aure kuma dukansu baa qasar ba suna wasu qasashen.

ALH HASAN JEERAH ma yayansa hudu duka mata ba biyu sunyi aure biyu sunata zuba karatu me zurfin dayaqi qarewa basu shirya aurenba.

ALH HUSAIN JEERAH kuwa yayansa uku biyu mata sai namiji daya,

Dukansu duk da sun kasance haihuwan turai basu wani riqe aladar rashin aure ba dan haka kusan dukansu babu wanda ba matansa biyu ba dan haka sai ya zama kaman al'ada ko Alh farouk daya dawo daga baya a cikinsu saida ya qara auren.

**********
Rayuwa taja,lokaci yaja an samu sauye sauye sabbi da cigaba da qaruwa harma da rashe rashe sbd a halinda ake yanzu Babu Alh hassan jeerah a duniya sun tafi sunbar yan uwansu Alh Ahmed jeerah Alh farouk jeerah da husain jeerah wanda ya tattara ya dawo qasar kuma sun gina wani mahaukacin estate da babu aljannar duniyar da babu a cikinsa kuma duk wani ahalinsu mai amsa sunan jeerah yana cikinsa dan haka suka sake zama sunan da har lokacin babu kamarsa a kunnuwan mutane.

Abdulhakeem jeerah ya zama cikakken captain 1st rank a Lokacin ne ya samu fara gudanar da luxury rayuwar nutsuwa da kwanciyar hankali tareda fara kaiwa kasar mahaifinsa da kakanninsa ziyara sbd a yanzu yakai matsayin tafiya koina.

Zuwansa na farko duniya tasan waye ABDULHAKEEM JEERAH,

Mahaifinsa ya gabatar dashi hakama dayan baban nasa wato alh husain,

Daga nan ne aka fara kokarin gabatar masa da matar aure a cikin dangi yan uwansa amma sam baida raayin hakan dan haka sai aka kyalesa dukda a yanzu cikin familyn basajin zasu barsa auro wata daga waje tin akwai yan mata masu class da wayewan da ilimin dika a cikin family amma dai basason tada masa hankali a natse zaai komai.

Abu babba daya da akasan familyn jeerah dashi bayan dukiyarsu da matsayinsu da kuma tsananin ilimin da suke dashi shine sunada riqo da addini me karfi da aka shede su dashi wanda ya saka hatta bangaren malaman addini basu girma da mutuntawa sukeyi sosai da gaske,

Bayan hakan kuma sunada tsananin girmamawa da tsare mutuncin sunan ahalinsu sbd kaf tinda suke babu wani wanda ya taba bata musu suna ko aikata abinda zaa aibata ahalin sbd tin asalinsu sun dauki suban tamkar rayuwar da baa buqatan mutuwarta.

Babu kowane mai rai dayake ahalin da baya tsananin kishi da kare martabar sunan gidan dan hakane iyayen suke tsaye tsaf gurin hana kowa da komai taba sunan jeerah batareda tsananin girmamawan da har jini zaka jita ba.
#MAMUH
#JEERAHS
#SIR HAKEEM JEERAH
#FLEET RAHEEM JEERAH

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

6
*_HAXXY's KULI_*
09123227777
Kin taba cin best qulin dayake tamkar alewan madara kokuma muce tamkar ba quli ba sbd dadi da nutsuwan daya samu gurin aikinsa??
Shin kin taba banbance kuli mai capacity da kuli kuli?
To taho ki gwada wannan special kulin da zaki iya cinsa da kuma shansa a komai wato HAXXYs KULI.

Gombe|Nationwide delivery
1500NGN per pack
Muna saida su yajin kuli, man quli, kuli kuli na dunqule da gyadan kunu duka.

*******
Girman matsayin da Captain Hakeem jeerah yake takawa yake qara daukaka sunan ahalinsa wainda a yanzu babu wanda baya alfahari d bugun gaba da matsayin nasa kuma hakan yake sake saka sunan zuwa manyan matakai da abaya ma bai kaiba sbd duniya ta sake fitowa daga zamanin baya sosai da samun wayewa da cigaba tako ina,

Abu daya dayake shima kaman a jininsu shine duk inda suka fara taka matakai sai sunji suna son gida tareda kasancewa a cikin ahalinsu dan qara dabbaka suna da martabarsu da itace abinda babu wanda ya isa kaf ya taba batareda yasan girman masifar daya tarowa ahalinsa ba.

*****
Jirgin karfe hudu ne ya sauka a airport din dake babban birnin Morocco wanda a cikinsa Captain hakeem ne da abokan aikinsa suka fito suma
Motocine kusan guda hudu dana securities suka taho daukansu dan isar dasu masaukinsu dayake tsakiyar babban birnin.

Isarsu masauki yayi daidai da isowar sabbin likitocin da aka gayyato daga qasar Morocco din dan aikin sati biyu da sojojin ruwan da suka taho daga wata qasar.

FAMMAH SAAD tana cikin sabbin likitocin da aka taho dasu da bata wani jima da gama karatu da fara aiki ba sedai tanada kokari sosai dan kuwa tanada wata irin dagiya ne akan duk abinda ta cimma buri kuma ta gado hakan ne itama daga nata iyayen wainda mahaifinta likita ne mai riqaqqen raayi me karfi hakama mahaifiyarta professor ce kaifi dan haka ta gado iyayenta dukansu ta zamo mai zafi da riqon raayi da tsananin sanin yanci da ikon kai da kuma tarin ilimin da bata yadda tayi wasa dashiba.

Da farko ranar data fara haduwa da Captain Hakeem jeerah kusan dukansu zafin kansu ne ya hadasu sbd babu sakewa ko wata alaman sakewa ko kadan a tsakaninta da duka navys din dama sauran abokan aikin nasu dan bashine ya kawota ba a ganinta,

Shi kuwa a nasa ba itaba ko manyanta babu kowace irin sakewan fuska daga garesa duk da shine babba a cikin tafiyar dan haka sai yanayin zafin kansu ya saka suka ankare da juna ta hakan kuma suka dan sabu da juna sbd kallan juna a wainda basa tattareda da shiririnta sakewa ko kadan.

Programs ne kala kala aka gudanar a cikin kwanakin ayyukan nasu kuma ako yaushe suna sake dan samun kusancin magana da juna da hakan ya zamana a cikin likitocin itace wadda yafi magana da ita sosai dan haka sai kusan aka bar mata ta jagoranci programs din har suka gama kwanakinsu aka gama komai.

Bayan tafiyarsu suna dan communicating da juna sama sama har Allah yasa suka sake dawowa Morocco qaddamar da aikin da sukai din wanda a wannan karan ne soyayya me tsananin karfin gaske ta kullu a tsakaninsu wadda ta bawa kowa mamaki daga iyayensu har abokan ayyukansu sbd ganin zafi da kafiyar kowannensu akan duk abinda zai zamo raayinsa dan kuwa a yanzu kowannensu yakeda riqaqqen raayi da rashin yadda ya saka baa taba saka ran zasu iya soyayya mai zafi da karfin gaske da ake ganin sunawa junaba.

A bangaren hakeem jeerah din so ne yakewa fammah din da baitaba jin zaima iya rayuwa a yanzu batareda ita a cikinta ba dan kuwa abu ne da bai taba ji ko sanin haka yake ba,

Fammah kuwa kusan abinda take ji akansa yafi ma wanda yakeji sbd su kam a yanda jininsu yake idan suka kamu da son abu to suna mutuwa ne akansa gabaki daya da zasu iya rasa ransu akansa dan haka ABDULHAKEEM JEERAH ya riga ya shigo rayuwarsu da batajin kuma duk duniya zai iya zama na kowace mace bayan ita tinda har mahaifiyarsa bata raye to ita kadaice macen da zata zauna a zuciyarsa har karshen ransa dan kuwa a yanda tsananin zafin kishi da kaifin zuciyarsu ta asalin larabawan Morocco take zasu zabi mutuwa kai tsaye akan zuciyar mijinsu ta kasance da wata a ciki bare azo akan hadasu da wata a rayuwar aurensu.

Bayan wannan zazzafan zuciyar kishin da suke da ita datai bushewan da babu kowane irin lamarin dazai tausasa musu ita ita kanta fammah nada tata kafaffiyar zuciyar ta daban da batajin zata iya hada Hakeem da kowace mace a duniya tana fatar kada Allah ya nuna mata wannan ranar gwara ta mutu bata duniya.

Iyayenta Dr Saad da mahaifiyarta prof shaarat sunyi farin ciki sosai da samun captain hakeem jeerah a rayuwar yarsu sbd soyayyarsa ta sauya abubuwa da dama a rayuwarta tareda sanyaya abubuwa da yawa dan haka suke sonsa sosai suma.

A nasa bangaren iyayen basu wani yi murnan samo mata balarabiyar Morocco da yayi ba sbd sanin tsananin zafin kishinsu da riqon raayinsu basa wani lankwasuwa sosai amma kuma ganin irin yanda yake tsananin sonta a bayyane ya saka suka amince akan sharadin zai ajeta ne a Nigeria tinda aikinsa baa zaune yake ba duk inda ya ajeta zai ringa zuwar mata hutu ne tinda yana can duniyarsu dan haka gwara ya ajeta a Nigeria cikin jeerahs tinda itama ta zama jeerah idan bata amince da hakan ba itada iyayenta sedai a hakura.

Da farko shi kansa bai aminta ba da hakan amma mahaifinsa shima ya aminta ya tsaya akan hukuncin da yayyunsa suka yanke wato Alh babba Ahmed jeerah da alh husain jeerah
Ya kuma san idan iyeyensa suka hade kai suka yanke hukunci sedai ka mutu ka bar duniya su rufeka amma bazasu sauyasa ba sbd wani irin karfin zuciya da raayi ne dasu wanda acan ya gado harma ya wucesu dan kuwa nasa ya wuce na kowa sedai tinda su iyaye ne haka ya tsaya akan hukuncin nasu.
Chapter 6 · 0% Book details