← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 154

Sashe 29

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daqyar SANAAH ta dawo masa daidai gashi kuma har lokacin zuwan iyayen nasa yayi basu taho ba sai aka qara masa kwanaki a lokacin ne ya shiga wani irin sabon tsananin zuciya daya fara sakar musu wasu irin mahaukatan kudi dasu da yan layin kaf haka ya ringa yi musu barin kudi da barnarsu kaman mahaukaci sbd kawai a dena maganar.

Kwanaki da lokacin aka sake dauka dan haka sai damuwa mai tsanani ta rufe Al'amin da nauyin uba yake kansa ganin irin son da SANAAH kewa AA gashi dai a karo na babu adadi ya sake nuna ba kowane su din ba dan haka sai ya sake kokarin rabasu sbd itama mommy ta fara shiga damuwan abinda ake fada a anguwa akansu.

Manyan anguwa ne suka nema AA din da kansu suka hadu da Al'amin sukai masa kashedin karshe akan SANAAH tareda yanke kowace alaqa wannan karan ko auren kwata kwata an fasa basa baa buqatan manyan nasa ma su taho.

Tinda suka fada masa hakan batareda SANAAH ta saniba zuciyarsa ta shiga duhu da nauyin dacin ganin irin mutanen da suke zaunar dashi suna fada masa magana dan haka yau da kansa yaje makaranta daukan SANAAH wadda ba damuwan komai ta shiga motarsa suka kama hanya.

Kallansa tayi a dan natse tana dauke kai tareda dago wayarta tana duba sako ta bude baki zatai magana sai kuma ta fasa sbd ganin yanayinsa kaman baya hayyacinsa kuma duk yanayinsa ya sauya da damuwa da kaman qunci.

Hanyar daba gida zata kaisu ba ya dauka ta dan sake dagowa ta kallesa tana son masa magana amma ganin yanda fuskansa take hade sai itama ta basar dashi taci gaba da duba wayarta sai data sake dagowa taga anguwan da suke shiga ta wasu gidajen masu karfi a qasa dasuke da tsaro tsit ba hayaniya hakama ba ruwan kowa da kowa koina shiru ne kaman ba muten a anguwan manyan gidaje ne da wasu irin tsarin da ita batama taba zuwa irin guraren nan ba ya sakata ajiye wayarta tana dagowa ta juyo ta kallesa da kyau ta bude baki tace

"Meyake faruwa?
Me nakeyi anan?
Kasan bana zuwa koina ko?
Pls mu juya ka maida ni gida ko ka ajiyeni a hanyar da zan hau napep din wucewa gidan.

Time ta kalla taga magrib ma ake kokarin kusan yi dan hakan taji ma gabaki daya hankalinta na neman tashi dan bata taba zuwa koina ba batareda sanin yayanta ko mommy ba hakama sam bayan makaranta vata zuwa koina tana gida koyaushe.

Baice mata komaiba ya qarasa lafiyayyan mahaukacin bungalow dinsa take yayi horn security dinsa ya fito daga ciki ya bude masa gate din mai kyau da tsari ya shige ciki yayi parking.

Wayarta ta daga zata saka kiran yaya Al'amin ranta a matiqar bace sai AA din ya saka hannu ya karbe wayar tareda jefar da ita yana bude motar ya zagayo ya budeta tareda kama hannuwanta biyu dake rawa sosai ya fixgota daga cikin motar yana kallan cikin idanuwanta da suka ciko da wani irin hawayen baqin ciki da tsananin tsoron da bata taba shiga ba yana jin kaman ya bude cikinsa ya sakata kowama duniya ya rasata sai shi ya gangaro da idonsa a hannuwanta daya damqe sa karfi tana kokarin fizgewa yaji wani tsananin sonta mai hade da shaawa me karfin gaske dayake son sauke mata sbd kawai yaji ko zai rage sonta da kuma idan yayi mata hakan ne kawai yayanta zai hakura ya jirasa ya aureta.

Yace

"SANAAH bazan taba iya barinki ba kaman yanda bazan taba iya aurenki ba,
Bansan tayaya zan iya rabuwa dake ba,
Meyasa dole sai munyi aure yanzu?
Nace ki bani time Insh Allah zan tilastawa zuciyata aurenki kuma zatai sbd tana sonki amma ba yanzu ba pls.....

Turesa da wani karfi tayi tana jin wani baqin cikin dayake neman kasheta yana danne kirjinta da idanuwanta da sukai jajir suna rufewa sbd ko zata mutu batajin har abada ma yanzu zata iya auren AA.

Riqota yayi da karfi yana daukanta gabaki daya tareda rufe bakinta data bude da karfin gaske zatai ihu.

Ciki yayi da ita yana shiga a palon ya jefar da ita a kan babbar lafiyayyar kujeran 3 seater sbd yanda take wani zillo da karfi tana jin zuciyarta zata buga.

Da karfi koina nata yana rawa ta yunkuro zata miqe da sauri,
Danneta yayi yana mata runfa da kirjinsa tareda danneta da hannuwansa biyu yana kokarin kai hancinsa wuyanta dan shaqo qamshinta dayake kashe hankalinsa.

A daidai wannan lokacin Samrah data ga motarsa a daidai lokacin dayake shigowa anguwan tana cikin tata motar biyosa tayi sbd ganin mace a gaban motarsa data tabbatarda SANAAH ce wadda take zuciyarta ta shiga wani baqin duhu da tsananin zafin kishi da hatta idanuwanta wasu zafafan hawayen baqin ciki suka cikosu suna kokarin zubowa ta iso kofar gidan tayi parking daga waje.

Buga gate din tayi take security daya ga itace ta security camera ya bude mata kofa ta shigo kai tsaye ciki tayi batareda ta tsaya ta amsa gaisuwansa bama.

Tana isa kofa bata tsaya knocking ba ta bude kofar kawai ta shiga sbd tasan password.

Cak ta tsaya idanuwanta na rufewa da wani duhu kafafunta na rawa ganin abinda yake shirin faruwa tanajin jiri na neman dibarta.

Tura fuskansa yakeyi a wuyanta tana turesa da karfi tana wani irin kuka mai karfin gaske tana neman ceto da fatar Allah ya dauki ranta kafin AA yayi nasarar yi mata wani abin.

Samrah data rasa me zatayi hannuwanta dake rawa ta daga da wayarta ta ringa daukan abinda yake faruwa idanuwanta na tsiyayo da hawayen baqin cikin kishins AA din.

Juyawa tayi zatabar gurin bata ma gani sosai sai kuma kishinta na barin SANAAH ta rigata sanin AA ya sakata juyowa ido rufe ta dauki qatuwar flower verse dake gurin ta buga masa akai da karfi take ya zube gurin.

SANAAH data gama fita hayyacinta sbd kuka da tashin hankali da tsananin tsoro miqewa tayi koina nata yana rawa gyalenta a hannu da dankwalinta tayo gurin samrah din da sauri bata hayyacinta ta riqeta da karfi tana fasa kuka da neman taimakonta.

Mota samrah ta fito da ita ta turata ciki sbd gabaki daya SANAAH din bata hayyacinta rawa jikinta yakeyi me tsananin gaske.

Suna barin gurin da gudun gaske samrah taja mota bata tsaya koina ba sai kofar gidan su SANAAH din wanda Al'amin ke tsaye yana kaida kawo idanuwansa jajir wayarsa a hannunsa sbd tinda SANAAH take bata taba kai dare a waje ba ga wayarta yanata kira tana ringin baa dauka.

Parking motar samrah tayi wadda ta saka idanuwan duk mutanen dake layin dawowa kansu.

Shima kasa motsawa yayi saida yaga SANAAH a gaban motar jikinta na rawa har lokacin idanuwanta jajir.

Tana ganinsa ta fito motar jikinta na tsananta rawa shi kuwa mutuwar tsaye yayi da mamaki zuciyarsa na wani irin mugun harbawa da karfi sbd kallo daya yayiwa SANAAH mummunan tinanin da gwara ya mutu daya ji hakan akan SANAAH ya shiga ransa.

Ita kanta SANAAH tana fitowa wani irin kuka tafasa mai ratsa zuciya tana fadawa jikin Al'amin wanda koina nasa ke wata irin rawa.

Samrah sauke glass tayi ta kallesa ta bude baki tace

"Idan har bazaka iya bata tsaron daya kamata ba to ka shirya tabbatarda abinda bai faru ba ayau zai faru wata rana"

Tana gama fadar hakan taja motarta ta bar gurin tabarsa tsaye jikinsa na tsananta rawar da hatta kafafunsa kasa daukansa sukai yayi baya saida ya dafa bango.

Dukkanin wainda ke kofar gidan a zaune sunji abinda ta fada dan kowa koina yayi tsit suka kafe SANAAH da idanuwansu cikeda mamaki da tsoro dan kuwa ma a yanzu a take wani kallan suka fara mata.
#MAMUH
09033181070
[28/04, 10:25 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

29
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Suna shiga cikin gida Yaya Al'amin dakatawa yayi tsaye cak a tsakiyar gidan yana riqo hannunta da karfin gaske har lokacin koina jikinsa rawa yakeyi ya kalleta idanuwansa jajir ya bude baki zaiyi magana ta fasa wani irin kuka tana fada masa abinda ya faru cikin matsanancin tsoro da rikicewa batareda ta jira yayi tambayarba.
Chapter 29 · 0% Book details