← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 154

Sashe 101

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinta yayi yana juyawa da saka doguwar wandon silk kayan baccinsa black tana ganin ya bar girin ya koma bedroom ta sake biyosa a natse tana isowa gabansa ta dago cikin karfin kuzari da bayyanarda damuwanta sosai ta bude baki ta sake basa hakuri tana rasa abinda zata dora dashi akan bada hakurin sbd kaman ba hurumin shigarta bane shiga maganarsa da Mum din dan haka tayi shiru.

Miqewa yayi ya kama hannunta ya sake komawa closet din da ita ya zaro kayansa na bacci da sam bazasu iya zama a jikinta ba ya saka mata a hannu sbd ta shirya ta kwanta tayi bacci kawai.

Numfashi ta sauke tana kallan kayan tareda rasa duka sukuni da nutsuwanta sbd da alama anan yake nufin xata kwana to me zata cewa su fammah?
Yaya zata fuskancesu?

Ta jima a cikin closet din tana rasa tinanin kamawa har kafafunta sukai sanyi sosai da tsayuwar ta zare kayan jikinta ta saka rigar daya bata wadda iyakacinta cinyarta danma ta mata yawa ne sosai ta sauka.

Kasa fitowa tayi ta durqusa a gurin tsawon lokaci shima kafin ta miqe a sanyaye ta shiga bathroom dinsa ta dauka sabon brush ta wanke bakinta ta tayi alwalan bacci ta fito.

Tana fitowa a sanyaye ta fito bedroom din daya ragewa haske sosai yana kwance a gadon idanuwansa a rufe.

Kasa hawa tayi ta tsaya tsakiyar dakin tana kasa cire tinanin abinda zai iya faruwa da safe idan akasan tana tareda shi.

Zurfi tayi a tinanin da batasan yaushe ya bude idanuwansa ba sai hannunsa daya kawai ya miqo ya kama hannunta daya ya janyota ta fado kansa ya birkita da ita dayan gefen ya kwantar yana juya mata baya ahankali sbd da alama rigima take son masa.

Hakan da yayi ya sakata kallansa da idanuwanta tana jin damuwa na sake rufeta sai kawai itama ta juya bayan ahankali tana rufe idanuwanta jikinta a mace sbd ta rasa yaya zatai ta iya fada masa abinda zai iya faruwa da safe idan ta kwana anan.

Bata ankara ba bacci mai karfi da nutsuwa ya dauketa a hakan wanda yanajin alaman tayi baccin ya juyo a natse cikin kwanciyan hankali ya zira hannunsa daya ya janyota jikinsa yana rungumeta da wata irin nutsuwa tareda saka kansa wuyanta ya rufe nasa idanuwan da shima ba jimawa baccin ya daukesa.

Acan kuwa gurin biki mantawa gabaki daya da SANAAH Mum tayi tasha hidimarta cikin farin ciki da walwala da wata irin murna,
Fammah ce ta damu sosai da rashin ganin SANAAH din amma sbd yanda itama aka ringa daukan hankalinta ya saka hankalin nata ya kasu gida biyu hakama tasan zuwa yanzu dole SANAAH na gida bata zo ba kenan.

Bikinsu suka sha har tsakar dare sosai kusan karfe boyi da rabi aka tashi aka fara watsewa kowa na tafiya da motocinsa.

Sai karfe uku da kusan mintina suka iso gida a lokacin kowa a matiqar gajiye yake dan haka Mum dakinta kawai ta shige ta cire komai ta fada toilet tayo wanka tana kokarin saka kayan bacci ta nufi gurin Fleet fammah ta shigo dakin tana kallan Mum din tace

"Mum SANAAH bata nan fa banganta a koina ba"

Qarasa fesa wani turare Mum din tayi tana ajiyewa tace

"Tana gurin Amma inaga tinda ba kowa a gidan dole can zata ta kwana"

Ficewa fammah tayi ta nufin dakin Amman ita kuma Mum ta qarasa shirinta ta fito tana kokarin ficewa Fammah ta sake dawowa gurinta damuwa na fara kamata tace

"Bata can"

Itama Mum din fara shiga shakka tayi ta juyo ta kalli koina a palon babu alaman inda mutum yake a kwance tace

"Kaman yaya wai bata nan? Ina zata tafi? Ina ta sani kowafa bata saniba,kuma Maleek yace baima ganta ba koda yaxo na dauka ai ta fasa zuwanne tayi kwanciyanta"

Qarasa maganar tayi zuciyarta na neman rikicewa dan tasan wlh Dad jeerah akan a rasa SANAAH tsaf zai datse aurenta da Fleet wanda da hakan ya sameta gwara ayi mata mutuwa.

Juyawa tayi tana bazama dakunan gidan daya bayan daya tana saka kiran wayar fammah da wayarta hankalinta na mugun tashi.

Fammah ma hankalinta mugun tashi yayi ta fara jin kirjinta na bugawa dan kuwa akwai matsala ne sosai ita kanta ai zuciyarta bazata iya daukan wani abi ya samu SANAAH dinta ba.

Wasa wasa sai ga gidan kaf a tsaye cikin tashin hankalin daya saka gajiyan kowa bacewa da shiga fargaban sace 'yar mutane a gidan.

Kasa iya sanarwa Fleet sukai sbd basusan yaya lamarin zai kasance ba dan Mum batama fatar abinda zai saka Koda wasa Zancen ya fita.

Kasa riquwa hawayen Fammah sukai sbd tinin aka fita harda motoci gurin nemanta a tsakar daren babu ji ba gani.

Mum jin tayi kaman Allah ya dauki ran Dad jeerah a daren kafin yaji labarin bacewan SANAAH da baasan inda zaa ganta ba babban tashin hankalinta kada wani abin ya sameta da bazai boyu ba.

Fammah kuwa jikinta har wani rawa yakeyi sbd sunyi kiran wayarta yafi so dubu bata shiga gashi babu wanda ya ganta ko a harabar gidan ko fitarta ko shigarta koina babu wanda ya ganta shi kansa mai gadi baiga fitarta ba ko wanda ya fita da ita sam dan haka kowa ya sake shiga rudu.

Kiran sallar asuba aka fara wanda ya sake sakasu tashin hankali mara misali babu wanda ya rintse a tsaye suke cikin rashin sanin mafita tsilli tsilli babu me nutsuwa.

Sabon tashin hankalin Mum gari na wayewa dole fleet zaisan abinda ake ciki dan haka ta zauna a palo ta dafe kanta cikin tsananin ciwon kai da fara jin takaicin SANAAH din data sakasu wannan tashin hankalin a daren daya kamata su kwana suna cigaba da farin cikinsu na biki.

Wayarta ce dake kusa da ita tayi ringing sbd kiran dayake shigowa.

Kallan wayar tayi da sauri tana jin kanta na sake sarawa sbd ganin numbern Imran ce mai kiran.
#MAMUH
09033181070
[08/06, 11:00 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

97
Tinanin qin daukan wayar tayi sbd kada susan abinda yake faruwa amma kuma tinanin dole akwai mugun babban dalili mai girma na saka Imran ya kirata da asubar ya sakata saka hannu ta dauki wayar tana dorawa a kunnenta ta kimtsa muryanta tace

"Yes Imran"

Cikin nutsuwa da bata girmamawa yace

"Barka da Asuba,mota na waje da zata daukeku zuwa airport jirginku zai daga karfe 6 zuwa America Umarnin Fleet ne"

Mamaki ne yaso kasheta daga zaunen ta bude baki da bayyanarda rashin fahimtarta tace

"Menene wata mota da wani ticket din tafiya kake magana,waye ne zaiyi tafiyar??

Numfashi mai nutsuwa Imran ya sake yana sake kamar da kansa da muryansa yace

"Umarninsa ne"

Wani mugun takaici ne ya taso mata mai zafi da baqin ciki akan wanda take ciki tace

"Wai nice kake maganar fleet yace nabar Morocco yau na koma America?
Da akai me?
Akan me?
Biki fa nakeyi?

Kashe wayarta tayi kawai kai tsaye tana miqewa idanuwanta rufe da wani zafaffen tashin hankalin dataji ma maganar SANAAH kwata kwata ta bace mata akai dan kuwa wannan itace asalin tashin hankalinta bata SANAAH ba.

Tana miqewa fammah ta kalleta da jajayen idanuwanta da sauri tana cewa

"Anganta ne Mum??

Ko amsa bata bawa fammah dinba ta wuce ko gabanta bata gani sosai tsabar abinda taji yana taso mata yana danne kirjinta.

Bangaren da aka sauke fleet din ta nufa kai tsaye Fammah na biyo bayanta cikin fargaba sbd ganin halinda ta shiga.

Suna isa tin daga hanyar isa da fammah bata ga alamar securities din Dad dinta ba ta sake shiga mamaki da rudu Mum kuwa kai tsaye shiga tayi bata tsaya palonba ta wuce bedroom ta bude ko kafarta bata sakaba ta fahimci baya ma villah din kwata kwata ta sauke idanuwanta akan gadon dayake a dan yamutse ta kalla taji kanta ya wani sara da karfin gaske amma buqatar dai yanzu ta gaggawa itace ganinsa da magana dashi da gaggawar gaske.

Juyowa tayi ta fito daga bangaren gabaki daya tana saka kiran numbernsa jikinta har wani rawa yakeyi.

Bata shiga ba ta sake danna kiransa tana cigaba da tafiya kamar zata kurma ihu.

Kira kusan na goma take masa amma wayar bata shiga kwata kwata dan haka ta saka kiran imran wanda yana dauka tace masa ina Fleet yake tana buqatan ganinsa kota yaya.

Shiru ya danyi kafin ya bata hakurin bazai samu cewa komaiba kawai dai driver na jiransu kada a rasa flight dinsu.

Zaginsa taso yi sbd tsananin bacin rai da tashin hankalin datake jin yana shigarta dan babu ta yanda zata bar bikin nan batareda an qarasa shi da itaba kaninta da itace uwar biki kuma ma batasan dalilin dayasa kawai zaa tado mata wannan mugun ji da ganin ba.

Fammah da jikinta ya fara bata akwai babban laifin da sukai a gurin Dad dinta wanda ya sakata fara tinanin ko ya siyawa SANAAH ticket itama ya turata Nigeria kokarin dauko wayar Ammah tayi ta fara saka kiran Dad din nata tana jin zuciyarta na wani irin tsalle.

Ms Meenah zarewa taji kaman zatai dan haka taso tafiya gidan Abbu a cikin duhun Ammah ta hanata tana cewa ta bari gari ya waye sosai.

Securities da aka aiko tareda motar daukansu kuwa kin matsawa sukai koina sai da ita da fammah dan kuwa umarni ne da suke fatan sai sun cikasa.

****A daidai wannan lokacin kuwa Sallan asuba yaje cikin nutsuwa da kwanciyan hankali ya dawo ya tadda ita ta idar da tata sallan sanye da jallabiyarsa datai mata wani irin yawa sosai daya sakata mata tai rollin mayafinta.

Kallanta yayi da fararen idanuwansa da suke fes da wani zallan nutsuwan kwarjini da steez da babu wanda zai taba iya kallansa ya kuma ya maimaita a lokaci daya baiji komaiba a zuciyarsa.

Dagowa tayi itama a natse da sanyinta ta kallesa lokacinda ya iso ya miqa mata hannu a natse yana bude baki zaiyi magana ta katsesa da sautinta daya shigesa da kyau da cewa

"Ina kwana"
Chapter 101 · 0% Book details