← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 154

Sashe 84

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taji saukan idanuwansa akanta dan haka taqi dagowa ta kallesa tana miqawa Mum din ta juyo a natse ta zauna kusa da Fammah dake gaidasa da kulawa da kewa ta bude baki a natse da sanyayyar sauti mai kamewa da nutsuwanta tace

"Ina wuni"

Sai daya bawa fammah amsa tukuna ya dauke idanuwansa daga kan fammah ya saukesu akanta da wani irin kaifin daya sakata kasa riqe zuciyarta dake jin kaifinsu ta dago idanuwanta masu zallan kyau tai masa wani sanyayyan kallo daya ta dauke idanuwanta tana maidawa akan fammah a narke ta kalleta taji sautin muryansa ta ratsa kunnuwansa yace

"How are you???

Har cikin zuciyarta taji saukan maganar dan haka ta dan ja numfashi mara sauti da bayyanarwa ko kadan ta gyada kanta ahankali sbd bazata iya magana ba dan idanuwansa na karya kowace garkuwan jikinta a daidai lokacin da kaifinsu.

Mum data gama zuba masa tea kallansa tayi taga idanuwansa na kan SANAAH din dan haka babu tinanin komai tace

"SANAAH yi serving Dad dinku"

Dagowa SANAAH tayi ta kalleta da wata irin kasala tana jin gabanta na faduwa sbd kusantarsa a lokacin zai iya hana gangar jikinta amfanuwa.

Ganin babu wanda yabi ta kan zancen dole ta miqe a tsanake tana takawa ahankali ta nufo gefensa daidai nan mum din tace Fammah ta dauko musu ruwa mara sanyi wannan yayi sanyi.

Tana isowa gefensa qamshinta ne ya shiga hancinsa dakyau a tsanake amma bai dagoba sbd yana kallanta yasan zata iya barin da zata illata kanta dan haka ya hana kansa kallanta sai hannuwanta ya saukewa idanuwan nasa da shima anan tajisu.

Cikik nutsuwa ta fara zuba masa brown paster da chicken salad din da aka dafa.

Tana kokarin zuba masa meatballs din dake gabansa hannunta ya dan fara rawa ahankali wanda babu tsammani taji saukan hannunsa a natse da wata irin sanyi da kulawa da kamewa akan nata yana dagowa kai tsaye ya sauke mata idanuwansa da suka sakata tsayawa cak ta dago ta kallesa idanuwanta na neman narkewa.

Janye hannunta tayi tana maida kallanta a natse gurin Mum wadda dago a daidai lokacin batareda ma hankalinta yakai ba.

Magana ya bude baki zaiyiwa SANAAH din batareda damuwan komaiba sai Meenah ta yankesa da dora hannunta akan cinyarsa tana ambatar sunansa da cewa yafara shan tea din.

Janyewa daga gurin SANAAH tayi tana komawa ta zauna sbd Mum din Fammah data dawo tafara kokarin zuba mata.

Kadan ta zuba abincin ta cinye batareda bata lokaci ba tasha ruwa ta dauki tissue ta goge bakinta tana kokarin barin gurin Mum tace

"Fleet gobe inason zamu je spa ni dasu Baby SANAAH sbd fara shirin tafiya bikin Abid dan inason zamu tafi da SANAAH insha Allah banason mu barta saika nema mana izinin tafiya da ita gurin Dad dan Allah pls kaji"

SANAAH dataji maganar kaman daga sama bata tsaya qarasa ji ba ta fice sbd a saninta hadda shi zaayi tafiyar.

Fammah na jin hakan taji wani dadi duk da tasan su zasu fara wucewa kafin Dad dinta din dan haka indai Dad jeerah ya bari to Dad dinta zai taho musu da Dad dan haka ta kalli Dad din wanda ya dago ya kalli Meenah da mamakin yanda kai tsaye take yanke hukuncinta ba lissafin komai.

Bude baki yayi a natse yace

"Bata buqatan xuwa koina"

Bude baki tayi zata sake magana suka ga fuskan hakan dan haka tayi shiru da niyar zuwa gurin Dad da kanta ta roki alfarmar ya bari idan Fleet zai taho ya je mata da SANAAH din.
#MAMUH
09033181070
[02/06, 9:34 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

78
SANAAH na komawa daki sallar ishai kawai tayi tai shirin bacci ta kwantawanta tana jin bata buqatan tafiyar da ake kokarin sakata dan sam bazata iya binsu ba a qasar da zata zama yar rakiya da takura.

Tanajin Fammah ta shigo itama tayi sallah tayi wanka da shirin bacci ta kwanta tana dan taba wayarta tukuna ta ajiye ta kwanta da wuri dukansu sukai bacci sbd SANAAH din datai sanyi tai baccin da wuri.

Washe gari bata bisu cin abincin ba ta tafiyarta bangarensu Mommy acan tayi breakfast tareda su daganan tayi zamanta anan.

Fammah ma anan tazo tayi breakfast daga baya iyayenta ne kadai sukai breakfast dinsu ayau.

Ita kanta Mum daga baya nan ta taho bayan tabi Raheem din taje ta gaida Dad fammah ma taje da safen ta gaidasa ta jima acanma suka tattauna.

Mum na zuwa bayan ta gaida su Maamah ta zauna tana cewa

"Dr Mum auren Zaid saura wata daya cif amma inason tafiya kafin lokacin kaman nan da Sati biyu nakeson tafiya ni da Fammah"

"Masha Allah,Allah ya nuna mana gashi bana nan zaayi sbd zuwa lokacin bana saka ran na koma gaskia"

"Nima banason ki koma Dr Mum gwara ki tsaya anan tareda mu tinda kusan babu me ranar barin nan tukuna yanxu a cikinmu muma ana gama bikin zamu tafi America amma mu dan qarasa hado wasu abubuwan mu dawo"

Hakan data fada ya saka Dr mum din ta dan kalleta tana cewa

"Zaku dan dade kenan"

"Aa Dr mum ni da nakeson ki dan saka mana baki dan Allah zanje da SANAAH taje bikin hakama acan America ma ba dadewa zamuyiba"

Sai a lokacin Maamah ta dago ta kalleta daga wayarta datake karanta sakon Al'amin daya shigo wayarta ta Whatsapp..

Mommy ma data iso gurin lokacin taji abinda ta fada dan kallanta tayi tana ajiye shayin maganin data dafowa Dr Mum na muran datakeyi ta juya ta koma kitchen tana ci gaba da aikinta da safiya.

Dr Mum kuwa dan basarwa tayi tana daukan maganin ta da mommy ta ajiye tace

"SANAAH kuma?
Kuda zakui tafiya ba qasa daya ba hakama ba lallai me ikonta ya bari ba"

Da dan karfin hali tace

"Dr Mum zai bari zan tambayesa da kaina na roka pls"

Maamah ce ta kalleta gabaki daya dai tana ajiye wayar hannunta tace

"Shi me ikon nata zaki roqa?

"Eh Maamah zan rokesa dan Allah abari mu tafi da ita mana tinda zamu dawo"

Dr Mum ma kallanta tayi da idonta gabaki daya tace

"Komai na tafiyarta bazai hadu ba a lokaci daya kinsani.....

Katseta Meenah din tayi da cewa

"Eh kafin Fleet ya tashi tafiya daurin auren komai ya kammalu sai su tafi tare"

Maamah data fara quluwa da halayen Meenah din itama akan naci tace

"Meenah idan kuma zai biya wani gurin fa kafin ya isa Morocco din yaya zaiyi da ita??

Kallan Maamah din tayi tace

"Maamah Dad dinta ne fa duk inda zai biya ai dai zasu iya lafiya insha Allah"

Dr Mum katse zancen tayi da cewa

"Ai tinda kinaso shikenan tinda kome zaa fada ba fahimta zaki ba Allah yasa abarta tafiyar"

Farin ciki taji tace

"Amin ai insha Allah Dad zai barta tinda tareda ni ne ga fammah ga Fleet din da kansa"

Wata firar suka kama su kuwa su SANAAH suna daki suna tasu firar da wayoyi SANAAH na lafe gefen fammah kaman koyaushe tana kallan fuskanta kaman wata babynta.

Guraren yamma suka fita gurin wata yar siyayya da karbo sabbin hijabs din da suka siya sbd sunason saka dogayen hijabs har qasa indai suna yawon cikin gida sbd basa son kaya mai nauyi ko kadan musamman SANAAH shiyasa take yawan saka hijab da dare indai zata fito daga wani bangaren zuwa wani  bangaren.

Sai magrib suka dawo suka wuce bangarensu kai tsaye SANAAH ce tayi tuqin dan haka key din a hannunta yake suna isa bedroom dinsu sallah suka fara yi kafin suka fito.

Fammah ce ta wuce kitchen ta tadda masu aikinsu suna kokarin shirya komai a dining na abincin da suka kammala dan haka itace ta hada komai na Dad din takai masa SANAAH kuwa bata fito ba shikenan ta shigewanta ko abincin dare bata buqata tea kawai ta buqata aka kai mata da snacks kadan.

Washe gari Mum da kanta dataje gaida Dad ta bude baki ta riqesa tafiyar tasu da SANAAH wadda yaji zancen da mamaki ya dago ya kalleta a natse kafin ya dan yi murmushin manya yace

"Shi RAHEEM din da zaiyi tafiyar da ita kin sanar masa?
Me yace akan hakan??

Murmushin tayi itama tace

"Eh na sanar masa amma kaman dai kai ake jiran amincewanka, dr mum ma na fada mata tace sai abinda kace"

Wani murmushin manyan ya kuma saki tareda cewa

"Shikenan zanyi magana dasu naji"

Godia tayi tareda barowa cikin farin ciki da jin dadin alamar Dad zai amince.

Tana ficewa da daddare wayarsa ya dauka a natse ya saka kiran Dr Mum wadda tana ganin kiransa ta kama fuskanta sosai tana daurewa.

Kaman ba zata dauka ba sai kuma data kusa yankewa ta dauka.

"Barka da dare Likita" ya fada a natse da kwanciyan hankali da muryansa datake ta tsayayyen dattijo data ratseta har cikin kwakwalwanta ta daure fuska tana hana kowace makaminta sassautawa.

Bude baki tayi a tata kamewan tace

"Barka da dare"

Murmushinsa na manya mai sauti ya sake wanda sautinsa ya shigo har cikin kunnuwanta ta kalli wayar a natse tareda sake jin nauyin kirjinta na karuwa da dawowa sabo.

"Yarki taxo ta sameni da maganar rokon tafiya da tawa 'yar wanda nakeson ji daga bakinki kina buqatan na baki aron  'yar tawa kin yadda da amanar 'danki da 'yarki???

Wani numfashi ta hadiye tareda kallan wayar tsawon seconds kafin ta bude baki tace

"Zasu tafi har America daga can kaman tafiyar tayi tsayi"

Murmushi ya kuma sakewa mai tsari da nutsuwa yace

"Amsa daya zaki bani likita daga nan har bangon duniya idan zasuje matiqar 'yata is safe a hannun yarki to shikenan dan kada ku manta auren nan ina nan ina jiran abinda nace sbd babu inda zaije kuma kema kaman matsayar kike jira na rabawa ki koma ko??

Wani siririn tsokin baqin ciki dr mum ta sake mara sauti tana jin maganar tasa a kirjinta direct kuma tasan da gayya yake fadan hakan dan haka kai tsaye amsa daya ta basa tana katse wayar.
Chapter 84 · 0% Book details