← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 154

Sashe 110

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tana dakin fammah ne,fammah je ki sanar mata Dad dinku na kiranta"

Dakatar da fammah din yayi yana sake bude bakinsa yace abarta idan ya dawo zuwa dare zaiyi magana da ita.

Dadin hakan sukaji dukansu dan haka abincin suka faraci hankali kwance da farin ciki banda shi da juice kadai yasha ya miqe ya fice.

Da rana Mum fita tayi bata dawo ba sai yamma sosai tareda baqi suka shige palonta sunata firarsu da turanci tana sake jin kanta sbd a cikinsu mijinta shine babban nasu mazajen.

Fammah ma taje cikinsu ta gaidasu suka dan taba firar da ita kafin ta fito ta barosu ta fita tana waya zataje da mota gidan wata abokiyar karatunta da sukai zata bar qasar yau so akwai sauran takardun da zata karbo a gurinta dan haka tana fita motocin Dad dinta suna dawowa bayan sallar magrib kenan.

Koda ya shigo ba kowa koina shiru Ms Meenah da bakinta suna can baya an hada musu table a kusa da swimming pool na gidan zasuyi dinner dinsu acan.

Kai tsaye bangarensa ya wuce ya shiga shower wadda ta daukesa mintina sosai sbd kansa ya kasa dena ciwo.

Yana fitowa cikin fararen kayan shan iska ya shirya marasa nauyi shirt da wando sai slippers bayan yayi sallah ya fito zuwa dining.

Ba kowa a dining room din dan haka baima zauna ba sbd ya juya yabaro gurin tareda nufar palonsa kai tsaye ya koma ya zauna yana jin sam kansa ba dadi.

Wayarsa ya dauka sbd bazai iya jurewa ba kansa bugawa yake neman yi ya saka kiran Meenah wadda tana dauka cikeda nishadi da wata isa ta ambaci sunansa tana cewa

"Hi my love"

Kai tsaye bai tsaya wata maganar hayaniya ba da nutsuwa yace

"I'm back ina buqatan something liquid mara nauyi"

Cikin kulawa da nuna soyayyarta a bayyane tace

"Ok zansa SANAAH ta kawo maka tinda daman zakai magana da ita"

Tana gama fadan hakan shine ya kashe wayarsa da mamakin ko bata gida ne?
#MAMUH
09033181070
[11/06, 1:47 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

107
Wayar dakin SANAAH ta kira wadda take zaune ta idar da sallah tai shiru tana jin dumi na sauko masa alaman zazzabin datake dan fama dashi duk dare amma batama damu ba sam ita da gaske gida takeson komawa.

A natse da rashin hayaniya takai hannu ta daga wayar tareda bude bakinta da sautinta mai sanyi tace

"Yes"

Jin muryan Mum ya sakata dan kallan wayar kafin ta sake gaidata da girmamawa da nutsuwa sbd tinda mum din ta dawo basu hadu ba tana daki bata fitoba.

"Ki kaiwa Dad dinku wani dan liquid abinda zaici ko sha yanxu nan pls dan bayajin Dadi"

Tana gama fada ta kashe wayarta batareda jiran jin komai daga SANAAH dinba wadda taso cewa itama batada lafiya bazata iya fita ba.

Shiru SANAAH din tayi tana sake jin wani abu mai nauyi ya danne kirjinta na duka kalaman Mum din kaf dinsu.

Wurgi tayi da wayar tanajin sake tsanar gidan gabaki daya da jin wlh bazata iya cigaba da zaman ba.

Sai data jima bata fitoba kafin ta fito ta isa kitchen ta hada masa wani lafiyayyan Cereal dayaji madara sosai amma bata saka sugar ba sbd zaqin madaran is ok banana ta yanda masa a ciki mai dan karfi ta doro a tray ta fito fuskanta a kame normal yanda duk wanda bai taba saninta ko ganinta yake iya fara ganin ta nufi dining taga baya nan harta ajiye zata tafiyarta sai kuma ta dawo ta sauka sbd zai huce ta juya ta nufi palonsa.

Yana zaune a natse a kame idanuwansa akan flats screen yana kallan da hankalinsa bawai yana kai bane nutsuwan kwakwalwansa yake buqata sosai ko kansa zai dena ciwon dayake fama dashi.

Da sallama ta shigo a natse idanuwanta basu dago ba inda zata ajiye tray din ta kalla tana isa gurin ta ajiye ahankali tareda dan dagowa babu kowace yanayi na sakewa ko sabo tace

"Ina wuni,gashi Mum tace na kawo"

Qarasa ajiyewa tayi tana juyawa zata fice ya bude baki ya ambaci sunanta data jisa da kyau har cikin kanta amma bata juyoba ta tsaya cak daga inda take na tsawon seconds kafin ta juyo kadan ta bude baki tace

"Naam"

Wani irin kallo ya sauke mata da idanuwansa da suka sauya ya sauke kafarsa dake kan daya ya miqe tsaye tareda takowa ya iso gabanta gap sosai har suna shaqar numfashin juna ta dan motsa ahankali tareda yin baya ta dago tai masa wani kallan daya saka yunwar cikinsa bacewa a take kansa na sake sarawa yace

"Yaya kike?
How are yoh
How have been??

Bata dago ta kallesaba sbd wani nauyin daya danne kirjinta da bakinta ta dan ja baya kadan ahankali tareda dago kanta bata kallesaba tace

"Alhamdllh,thank you"

Dan shiru tayi tana jin wani zazzafan kallansa akanta wanda take jin sanyinsa da rasa abin fada akanta dan kaman maganarsa ta qare baisan ta inda zai fara bayanin abinda bama zai bayanun ba.

Dagowa tayi kadan ta kallesa a lokacinda yayi taku daya gareta zai kama hannunta tace

"Inason komawa gida pls"

Kaman daga sama yaji zancen dan haka kallanta ya dan dago yayi tareda juyawa ya koma inda ya taso ya zauna yana jin ciwon kansa ma na dawowa sabo ya sauke wani zazzafan numfashi yana bude baki yace

"Why?

Hannunsa daya ya miqa mata yana kasa riqe kansa yace

"Zo ki fadamun menene matsalar?
Zo ki fadamun abinda ya saka kike wahalar da kanki bayan bakyason ganina bare nasan dalilin"

Wani sabon kishinsa ne ya taso mata ta dago ta kallesa da idanuwanta da suka shiga cikin nasa yaji yana sake rasa nutsuwa da kwanciyan hankalinsa kafin yace komaib tace

"ba komai ni gida kawai nakeson komawa"

Tasowa ya kuma yi wannan karan damuwan dake boye a cikin kansa da mamaki dan bayyanuwa sukai ya nufota bai tsaya komaiba ya kamota gabaki daya xuwa jikinsa ya mata wata riqon da har cikin jininsu suka jisa da wata irin kewan da zata iya kasa dukkaninsu rasa kansu ya kalli fuskanta data rintse idanuwanta da karfi batason kallansa wasu hawaye suka gangaro dags cikinsu wanda ya sakasa binsu da kallo tsigar jikinsa na tashi dan kuwa yasan ba qaramin radadi take ji ba dan haka ya bude hannuwansa ya sakata jikinsa yana rungumeta da wata irin sanyi da tsananin jinta a zuciya da jini da bargo da kowace tsiga ta gangar jikinsa.

Kawai kuka ta fasa masa mai wani irin ratsawa da rashin sauti sosai yana shigarsa tako ina da warware kowane kamewa,nutsuwa da lissafinsa yana jinta.

Kukan take masa sosai tsawon mintina kafin ta zare jikinta daga nasa ta juya kawai ta fice tana wucew dakinta da gudu tabarsa tsaye.

Kasa motsawa yayi yanaji gabaki daya shima gidan da qasar na ficewa daga kansa ahankali.

Ita kuwa tana isa dakinta kan gadonta ta xube tana cigaba da kukan dayake dankare da kirjinta duk kwanakin.

Ahakan fammah ta dawo ta sameta cikin wannan halin tana zaunawa kusa da ita cikin tsananin damuwa da tashin hankali da mamaki ta dafata ta fada jikin fammah din tana cigaba da kukan da saidata jima tana yi kafin ta iya samun abinda yake danne da ita ya dan fada mata.

Fammah duk damuwa ta shiga ta ringa tambayarta abinda ya faru amma bata iya cewa komaiba sai data shiga bathroom tayo wanka ta fito a natse ta sanar da ita gida takeso.

Kiram mum fammah tayi lokacin baqinta sun tafi kenan dan haka nan dakin tayo tana kallan SANAAH taji hankalinta ya tashi musamman dataga yanda idanuwanta da fuskanta sukai jajir.

Yanda suka daga hankalinsu hadda sanar masa ya sakata jin tausayi da sabuwar kaunarsu har cikin ranta hadda Mum din ta dan sake tana nuna musu ta dena.

Da safe koda ta tashi fuskanta ta sake ja idanuwanta ma sun dan kumbura sbd a cikin tsakiyar daren ma sai datayi sbd kafin Mum din ta wuce gurin mijinta sai data shigo gurinsu tana fidda wani fitinannen kamshi da wasu kayan bacci masu kyau a jikinta duk da ta saka babbar after dress akai kafin ta isa dakin nasa.

Suna tashi da safe SANAAH wankanta tayi ta saka kayanta marasa nauyi doguwan chiffon material budaddiya mai kyau purple ta dauke gashinta a tsakiyar kanta ta koma kan sofa ta lafe batada niyar ma ko fita palo bare zuwa dining din data yafe.

Mum ce ta shigo dakin bayan fammah ta gama shiryawa ta juyo zatai mata maganar fita breakfast.

Cikin adonta itama mum din take dan daidai ta iso tana kallan SANAAH din da bada umarni dan kawai ta tilastata fita breakfast din tace

"Ku fito dukanku oya SANAAH taso banason jin komai"

Juyawa tayi zatai fice SANAAH ta bude baki da dan sauti mai nutsuwa tace

"Banajin yunwa ba yanxu zanyi breakfast ba Mum"

Bata juyoba tace

"I dont care dole ki fito daga yau na hana wannan zaman dakin da kike wanda shine yake sakaki jin kewan gida kina wannan kukan"

Ficewa tayi SANAAH da idanuwanta suka sauya da wani irin damuwa da nauyin kirji mai karfi kasa dawo da kallanta tayi akan fammah zatai magana fammah din itama ta juya da sauri ta fice sbd itama batason wannan damuwan da SANAAH ke shiga gwara ta ringa fitowan.

Fammah na ficewa hanyar palon Dad dinta ta nufa gaidasa tana isa yana fitowa daga bedroom dinsa idanuwansa har lokacin babu saukin komai a cikinsu.

Qarasowa tayi tana dan rungumesa tana gaidasa da cewa

"You dont look good Dad,yaya kan?
Ko kana buqatan ganin likita ne Dad"

Girgiza mata kai yayi a natse yana dan kissing kanta yana bude baki wani hayaniya da son doguwan magana yace

"No Doc, alhamdllh insha Allah"

Fitowa sukai tana masa magana yana sauraronta yana saka kai a dining din matarsa datake kokarin zama fasawa tayi tana nufarsa sbd koda ta fito bai tashi ba daqyar ya iya samun baccin ko yauma sbd tsananin ciwon kan daya hanasa ko baccin arziki.

Gurinsa ta taho tareda dan rungumesa itama da kulawa tana cewa

"Good morning my love"
Chapter 110 · 0% Book details