← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 154

Sashe 45

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba hayaniya a gidansa da rayuwarsa,
Ba kowace irin damuwa ko buqatan bayani ko tsarin dokar kowane farin ciki da walwala a haka suke rayuwarsu da babu komai a cikinta sai zallan wayewa da asalin daula da kwanciyan hankali da kauna me karfi da soyayya mara sirki Babu ma macen da zata iya rayuwa a cikinsu,
Babu macen da suka zasu iya rayuwa da ita dan haka wannan aure ne da mahaifinsa yayi kawai sbd dawo dashi qasar Nigeria da zuwa akai akai kuma indai hakan ne baida kowace kalma ta fada akan hakan sbd a kalaman dayake bayyanar masa bin bayan daurin auren shine wulaqanta auren na nufin wulaqantasa.

Bai taba iya hayaniya ba da kowa bare mahainfinsa da babu kowace sakewa a tsakaninsu bayan umarnin daman da order tin yarinta hakama shima tin yarinyar haryanzu da manyancin yaxo bai tana daga ido ya kalli Hukunci ko umarnin mahaifinsa ba akansa dan haka a natse ya dan sake dago idanuwansa da suka dan sauya a take da wani mafi girman nauyin umarnin da baa taba basa ba irin yau koda kuwa na aikinsa ne tinda yake kuwa.

Bude baki yayi a natse da deep voice dinsa mai kaurin dake tada tsigar yawancin duk wanda ya fara jinta for the first time yace

"Nagode Allah ya saka da khairan ya qara nisan kwana da lafiya"

Hakan daya fada ya saka Dad saka masa albarka shima tukuna sukai sallama batareda kowace sabuwar magana ba.

Shima a natse ya ajiye wayarsa gefensa idanuwansa a sauye sosai Ms Meenah na gefensa bata lura da yanayinsa ba ta fara kokarin yi masa magana akan taso gaisawa da Dad itama a wayar.

Baice mata komaiba saima dagowa da yayi da wani kamewa yayi mata kallo daya da idanuwansa da suka mugun sauyawa take tsigar jikinta suka tashi sbd yanda kallan ya ratseta tajisa har tsakiyar kanta,
Fleet Raheem jeerah bai taba mata kallan da batajinsa ba har acikin kwakwalwanta ba koda kuwa na fushi ne idan sunyi fada sbd ita dai Allah ya jarabceta da komai nasa.

Dauke idanuwansa yayi daga kanta yana sanar mata yana buqatan silent time.

Bata damu ba sam da tambayar meya samesa ko meya faru a gida ko kuma dad dinne ba lafiya sbd ba dabiarta bace sam ita dai bata damu da kowa nasaba da komai dashi kansa indai akan abinda taga kaman sauyi ne kawai ita shi take so a kowace hali dan sam bai saba da samun kulawan tambaya ba ko karantar yanayi wanda shima baisan da hakan ba sbd sabon data basa na rashin karantar yanayi ko tambayar wanda hakan ya saka bata san abubuwa da dama ba gameda shi ko familynsa dake Nigeria ba ko mahaifinsa koma gurin aikinsa ba.

*****lokacin hajiyar Samad taga balain neman rasa danta ganin idonta hankali tashe ta kira Mr S ta sanar masa shine ya sanar da Dad wanda a hakan ya saka aka tattara komai na Samad din na tafiya yace akaisa airport idan ya farfado acan jirgi kawai zaibi.

Hajiyar Samad din qarasa yankewa tayi daga kowace sauki daga Dad din dan kuwa tsoro lamarin ya fara bata,

Ba imani haka aka kwashesu har airport itace ta hada kayan Samad din komai da komai aka tafi dasu.

Cikin daren suna isa aka saka securities suka tsaresu a mota har sai lokacin tafiyarsa yayi,

Koda ya farfado baima damu da inda ya gansu ba da halinda suke ciki jin yayi ya rasa kansa gabaki daya,
Wata muguwar rawa da jikinsa yakeyi zuciyarsa da tinaninsa sun bace bat dan haka hajiyarsa ta ringa kokarin dawo dashi daidai amma lamarin yayi munin da kuka kawai ta fasa ta fara yi wiwi tana rungumesa jikinta tareda ringa tsinewa auren da da wainda aka daurawa auren da fatar kada auren ya bawa kowa farin ciki har abada.

Samad kuwa baya hayyacinsa sam gashi an hanasu matsawa koina a wannan halin suka kai asuba aka fito da Samad din kaman wani qaramin yaro sbd baya hayyacinsa sam aka wuce dashi.

Haka akai masa kowai batareda ya dawo hayyacinsa ba aka wuce dashi hajiyarsa na airport din tana wani kukan baqin ciki cikin mota har saida jirginsu ya daga tabar Airport din aka dawo da ita gida.

Sabon tashin hankalin data fuskanta shine koda ta iso gidan guraren 8 na safe har an bude mata inda zata koma an saka sabbin furnitures masu tsada da kyau da tsari ba cutatarwa.

Bangare ne daya kusa dap danasu SANAAH hakama komai iri daya ne da nasu wanda yake shima babu abinda ya rasa na tsarin jin dadin duniya da daular gaske kawai dai hakan da yayi mata yana nufin ba sauran aure a tsakaninsu kenan tinda babu inda zata anriga an manyata an tsufa.

Baqin ciki da abinda taji ya danne kirjinta kwantawa ciwo tayi tana fatar Allah ya dauki ran Dad din ma ya mutu tin kafin asan da ya gama da ita kowama ya rasa a huta.

Komawanta bangaren sabo ya saka Umma jin dadin hakan sosai sbd hajiyar Samad itace fitinar gidan da kuma me isa da tinkahon itace me 'da a gidan tinda Raheem ya shafe kaman babu kowace 'da a gurin Sir jeerah sai Samad sbd Fleet Raheem jeerah yafi kama da business partner na jeerahs than a son dan shine yakeda babban hannun jari a businesses nasu da dukiyarda takeda karfin gaske.

SANAAH kuwa washe gari Dad da kansa ya kirata taxo ta samesa ya zaunar da ita ya sake mata nasihu masu ratsa jiki da suka bawa zuciyarta nutsuwa da kwanciyan hankali sbd ya bata tabbacin yanda ya daura auren nan bazai taba barin kowa a duniyar nan ya nuna mata rashin daraja ba ko waye kuwa.

Hakama Sabuwar mota dal data narke miliyoyan kudi masu yawan gaske ya mata kyauta a matsayin tukuicin biyayyarta da rayuwar da zata fara ta cikakkiyar budurwar datake da power a yanzu bama yanci da gata kadai ba.

Hajiyar Samad jinya tayi ta kwana biyu ta asalin zallar baqin ciki amma babu wanda yabi ta kanta taci baqin cikinta ta cinye ta miqe da tsanar kowama a gidan hadda uban gayyar wato Dad.

Su mommy kuwa yanzu da SANAAH takeda aure akanta hankalinsu kwantawa yayi batareda sun damu da Samad yana nan ko bayanan ba sun maida hankali akan hutawa da jin dadi kawai,

Dad ya budewa SANAAH sabon babin rayuwa me kyau da jin dadi dan kuwa komai saida aka sauya aka ninka mata aka zuba mata kudi masu lafiya a acct sbd yin duk abinda take so ga sabuwar motarta da aka dauki lokaci aka ware aka koya mata harta qware itace take ja takai kanta makaranta da duk inda take so.

*******Rayuwa ta sauya sosai sbd lokaci yaja sosai shekaru sun qara tafiya wanda a ciki ne Yaya Al'amin ya gama karatunsa harya fara koyan aiki acan batareda ya dawo ba sbd son tsayuwa da kafafunsa da nasa sunan hakama yazo ya gansu ya musu hutu har so biyu amma sam baa jeerahs ya sauka ba a hotel mai kyau da tsada yake sauka ya gama hutunsa ya komawarsa.

SANAAH KHALIL rayuwarta tafi sauyawa akan ta kowa sbd a yanzu ba iya Sanah bace Ms SANAAH KHALIL ce wadda kyanta,tsarinta,class dinta da wata irin ilimin daya ratseta daban yake,
Hutu da gata yayi mata ratsar da komai nata fizgan hankalin duk wanda zai kalleta yakeyi,

Gata da daular datake zubawa ba iya Nigeria kadai ba take zaune suna fita kasashe sbd ko gurin yaya Al'amin zuwanta kusan uku hakama umrah ma suna zuwa itada mommy wani lokacin ma da ita da mommy da Ummah.

Kauna da tsananin biyayyar dake tsananinta da Dad sun dake karfi sosai dan kuwa babu daren da ba itace mai kai masa tea da snacks ba ta gaidasa dan da dare ne ma ya koma lokacin zuwa gaidasa,

Karatunta yayi nisan datake gap da kammalawa sbd dan tana final year dinta,

Hajiyar Samad itace wadda ta bayyanarda tsanarta a fili a kanta wanda ya saka sam bata ma shiga ko bangarenta kwata kwata iyakacinta da ita gaisuwa idan sun hadu ko a hanya ko a harabar da kowa zai shiga motarsa ya fita.

A daidai wannan lokacin aurenta dayake kanta data manta dashi kwata kwata a rayuwarta sbd tin daga lokacinda akaisa baa sake maganarsa ba har ayau dayake kusan shekara uku zuwa hudu bata taba damuwa ba sbd hakan ma shine daidai a gunta bata buqatan kowane namiji a rayuwanta haka tafi mata.

Yaya Al'amin da mommy ne sukaso su damu amma suma ganin karatu takeyi hakama hankalinsu su duka a kwamce sai suka aje damuwar sukaci gaba da rayuwarsu a walwala.

A daidai wannan lokacin ne Allah ya hadata da wani sabon lecturer dinsu dayazo program na shekara daya a qasar daga Srilanka amma mahaifinsa dan Nigeria ne.

Da farko basama wani shiri sbd yawan zuwanta late daga baya kuma rashin shirin ya koma mutunci da shiri daga karshe ya kamu da wata irin sonta mai zafin gaske da kuma tsananin son aurenta.

Bai bayyana mata soyayyarsa ba sbd kai tsaye aurenta yakeso kuma batareda jan lokaci ba dan haka mahaifinsa ne ya nemi Dad dinta kai tsaye wato Sir jeerah da nemawa dansa aurenta.

maganar ta girgiza Dad sosai anan ya gane irin kuskuren watsi da maganar auren da sukai su duka dan haka kai tsaye ya basu hakuri da sanar musu tanada aure akanta already da wannan ne kuma cikin bacin rai da zafin daya cikasa akan maganar auren da Duk shekarun nan Raheem bai taba masa ba ya dauki wayarsa ya kirasa kiran da baya buqatan komai sai son sanin matsayin auren.
DAWOWA LABARI.
#MAMUH
09033181070
[05/05, 10:19 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
Chapter 45 · 0% Book details