← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 154

Sashe 49

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun dan gaji dan haka hutawa sukai sai bayan magrib suka fito palo suka zauna anata fira sunacin abincin da yanzu ake kokarin yi daidai da iya cin Fammah da Dad dinta da kullum daga nan yanxu ake kai masa abinci kuma mommy ce tinda sukaxo yanzu take musu abinci sbd shi da fammah.

Sai da sukai sallar ishai SANAAH ta hada komai na Dad taje tayi wanka tayi shirin baccinta tukunta ta dora doguwar hijab har qasa mai hannu ta fito fuskanta fresh kaman babyn da baa taba shiga rana da itaba ta dauka suka fito da fammah wadda itama take sanye da hijabin amma nata ba har qasa ba.

Suna isowa palon farko SANAAH ta dago a hankali cikin nutsuwa sbd shaqar iskan da qamshin dayake cikinsa bata taba jinsaba a rayuwanta.

Fammah kuwa suna dosar palon kurya na Dad hancinta ya shaqi kamshin Dad dinta take ta tabbatarda mahaifinta yana ciki komuma ya shigo ya fita dan haka ta saki ajiyan zuciya da jin farin cikin haduwa dasu gaban kakanta dan basu taba haduwaba haka su duka sukai fira dan ita bata taba sanin mai yake faruwaba.

Itace a gaba ta saka hannu ta bude kofar bakinta dauke da sallama tana shigowa idanuwanta akan Dad dinta wanda qamshinsa ya gama cike niimar gurin gabaki daya yana bada wata irin izza da nutsuwa ga wanda baida ita.

Murmushi ne mai girma da farin ciki ya ciketa tanufesa cikeda tsananin so tana ambatar sunansa ya dago a tsanake da manyan idanuwansa da haskensu da nutsuwan dake cikinsu ke saka mutum samun mutuwan jiki daidai lokacin SANAAH ta sako kai gabaki daya a wata irin nutsuwa da fizgan hankali tareda hasken kalan hijabinta off white daya saka kallansa dana Dad sauka akanta lokaci hannunta dauke da tray din dayake black dauke da tea set haske da kyan yatsun hannuwanta suna daukan ido akan black tray din.
#MAMUH
09033181070
[06/05, 10:05 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

47
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Cak ta dan dakata daga takowan datakeyi da dukkanin nutsuwa sbd saukan idonsa akanta na second daya dan kuwa ganinsa bai gama saukar mata ba ya dauke idanuwansa a kame yana tsayar dasu akan 'yarsa wadda take cikeda farin cikin ganinsa ta miqa masa hannunta tana gaidasa a yanda sukeyi wani lokacin.

A tsanake ya miqa hannunsa suka kama alaman gaisuwa yana bude baki muryansa ta bayyana a cikin sautin dakin ya amsar gaisuwan amonsa na isa har inda SANAAH take kokarin qarasawa gaban nata Dad din muryan ta ratsi kunnuwanta ta durqusa qasa ahankali tana ajiye tray din gabanta a natse batareda jin komaiba na daga muryan data ratseta hakama bata dagoba ta kalli koina bayan Dad dayake kallanta a natse da kulawa.

Bude bakinta tayi da nata sautin mai sanyi da nutsuwa ta gaida Dad ya amsa yana bayyanarda kulawansa akanta,

Batareda ta juyo ba sosai ta dan waiwayo ta bude baki ta gaida Dad din Fammah din.

Gyada kai yayi a taqaice yana sauraran fammah cikin tsanake dan baya cikin yanayi ba buqatan hayaniya sbd maganar dasuke yi da mahaifinsa kafin shigowansu.

SANAAH ganin Dad din yanada baqo sai bata tsaya komaiba tana zuba masa ta miqe ta juya ta fice fammah ma bata wani jima ba ta fito ta biyo bayanta tabarsu.

Dad duk ganin da Fleet yake buqatan masa ya gansa din amma sam yaqi masa maganar auren again saima godia kawai dayayi masa akan abinda yayi masa da nuna masa cewan uwarsa tafisa karfi da iko akansa.

Wannan kalaman ya saka Fleet yin shiru yana jin nauyi da girman maganar da laifinsa dan haka hakuri ya bude baki ya bawa Dad din tareda neman afuwan zai gyara kuskurensa.

Wannan halin nasa na bai taba duba girma da matsayinsa a gaban iyayensa ba ya saka Dad bai taba hada sonsa da kowaba a duniyarsa da rayuwarsa,

Tin ba yanxu ba Raheem bai taba dagowa ga duk abinda zasu fada masa ba ko zartarwa akansa,
Yana karban kowace hukuncinsu da maganarsu da nutsuwa komai rashin dadinta garesa hakama bai taba iya tsayawa maida kowace irin doguwan bayaniba ko magana iyakacinsa dasu godiya ga kowace jawabinsu da fushinsu koda fada ne kuma har yanxu daya zama babban mutum me girman matsayi da power bai taba sauyaba daga hakan a tsakaninsu dasu.

Saukowa Dad din yayi tareda yafe masa sbd laifin duka nasu ne dan haka zaiga irin gyaran da zasu dauko su dukan uzuri daya ne yanzu yayiwa tarewan SANAAH da bazaiyi magana ba Al'amin daya roki abari sai yana nan ya dawo hakama yanzu baa gama tanadar gurin da zata tare dinba zai bari a shirya a natse.

Sun jima sosai a tare har dare sosai tareda Dad din kafin ya baro bangarensa ya nufi nasa Imran na biye dashi yana sanar masa anyi canceling tafiyarsu daya kamata ayi a jibi sai zuwa wani satin tinda bai gama ganin Dad ba.

Suna isa imran ya bude masa kofar palon yana jenyewa gefe saida ya shige ya janyo kofar ya rife bayan yayi masa saida safe.

Kai tsaye hanyar palonsa ya ratsa yana daga wayarsa dake ringing Ms Meenah ce.

Daga wayar yayi yana tafiya zuwa bedroom dinsa,

Da sautin muryansa mai kasheta akansa ya furta

"Yes Mrs Raheem"

Yanda ya ambaci sunan nata ya saka a koyaushe take qara ji da tabbatarwa da kanta ita kadaice Mrs Raheem har duniya ta nade bazata taba iya jin wata ta amsa sunan Mrs dinsa ba zata iya rasa ranta tsabar baqin ciki.

Numfashi ta sauke cikesa kewansu tana cewa

"Inaga zuwa next week zan taho Nigeria nima coz ban taba dadewa haka ba batareda ku ba,
Duk tafiyanka da kakeyi kana dadewa batareda mu ba Fammah na tareda ni bamu taba rabuwa ba sai wannan karan so inajin kaman bazan iya ba gwara na taho"

Bai bata amsa ba sauranta kawai yakeyi yana zaunawa a kan lafiyayyar sofa dake makeken bedroom dinsa.

Itace tayita masa fira yana sauraronta da bata wasu amsar a taqaice har suka gama ya miqe yana kashe wayar gabaki daya ya ajiye ya nufi babban closet dinsa dayake a jere da sitirar sakawansa da sauran duka abubuwan amfaninsa da kamar ba tafiya zaiyiba sbd yanda aka zubar da dukiya aka sake zuba masa komai haka zai gama kwanakinsa ya tafi yabarsu.

Zare komai nasa yayi yana daura blue towel a qugunsa mai fadi da karfin dayake bayyane sbd haryanzu dayake da budurwar 'ya jikinsa a kame yake da wani irin karfi kaman matashinda yake cikin lokutan karfinsa da lafiyarsa.

Fatarsa sai daukan ido takeyi sbd fresh da lafiya tareda hutu babu alaman kowace irin wahala ko rashin lafiyar jiki a tattare dashi sai tabo guda uku dake jikinsa na biyu a bayansa daya na harbin bullet daya na yanka mai dan tsayi sai guda daya a gefen cikinsa shima na bullet wanda suke na gwagwamaryar aikinsa da babu mai irin matsayinsa dayake kai babba baida ire iren wainnan tambunan a jikinsa wainda suke ke sake tabbatarda irin jarumtar dakake da ita a fagen yaqi.

Toilet dinsa mai girman gaske ya shiga yana zare towel dinsa ya jafa a inda yakamata ya ajiye yana qarasawa tsakiyar shower ya sakarwa kansa ruwan dumi da suna sauka kan fatarsa suka gangarawa cikin sauri suna sauka sbd rashin datti da gartsin fatansa.

Take tsadaddiyar qamshin body wash na LeLabo ya fara tashi yana gauraya toilet din cikin sanyi da dumi mai dumama fata da ciki.

Koda ya fito daure da wani towel din jikinsa baya wani tsiyayar ruwa sbd ya goge jikinsa da gashinsa da wancan towel din shiyasa ya sauyo wani sabo ya fito har lokacin fatarsa fidda qamshin Lelabo body wash takeyi a sanyaye.

Cool body spray na Dior ya saka a jikinsa ya saka underwear dinsa da suma suke kaf designers brand daban daban masu tsada a jere kaman bana mutum daya ba.

Fararen silk pyjamas ya saka ya gama shirin bacci yasha ruwa kadan ya kwanta a tsanake sai kuma da safe.

****SANAAH washe garin bata zuwa school dan haka basu tashi da wuri ba sai da rana t fito suka tashi suka fito kowacensu sanye da kayan bacci SANAAH na waya da Yaya Al'amin ta iso dining din wanda tini suka fara cin abinci sbd Fammah sam batason yunwa ko kadan.

Ta jima tana waya dashi sosai kafin ta gama ta fara cin abincin tana gaida mommy suna magana da fammah.
Chapter 49 · 0% Book details