← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 154

Sashe 103

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata yunqurowa yayi yana tasowa zaune da ita a jikinsa batareda ya saketa ba sukai wani irin fitinannen zaman da kafafunta suke rabe a jikinsa zagaye da bayansa ya saka kansa a tsakiyar kirjinta ya rungumeta da wata deep passionate yanayin da sukai shiru yana lafewa a jikinta.

Ahankali ahankali bata ankara ba tajisu cikin wani zazzafan yanayin da ya sake kasancewa da ita a lokacin wanda suna gamawa itace ta fara wanka ta fito ta tadda ankawo mata kaya doguwan riga mara ado da hayaniya mai nutsuwa a jiki ba takura ko kadan.

Shiryawa tayi da komai nasa banda Turarensa datasan kowa zai iya ganesa.

Shima cikik navy blue kaya ya fito da slippers black masu tsadan gaske sai agogonsa a hannunsa qamshinsa na tashi a cikin nutsuwa ya fito fleet admiral dinsa mai tsantsar kwarjini da kamewa.

Fitowa sukai kai tsaye babban palon gidan dake dauke da babbar dining room a ciki ya nufa da ita wanda anan ake jere abinci sbd a tare kan dinin ake cin abincin gidan yanzu da babu kowa akasan shine kadai sai baayi abincin da yawa sosai ba kaman yanda aka saba.

Abincin da zata iya ci duka aka girka na breakfast din sbd tin karfe 7 na safe imran ya kira chief din dazata girka asalin girkin jiyan da SANAAH taci a cikin gidan aka biyata kudi masu yawa.

Angama komai an jere a dining suka iso Imran na biye dashi bayan ya gaidasu a natse ya bude baki ya sanar masa Mrs jeerah taqi yadda ta tafi tama fita da mota kuma yana saka ran can gidan ta tafi.

Fleet din baice komaiba sai da ya dan gyada kansa cikin kamewa yace

"Ayi renewing tickets din"

Gyada kai Imran yayi yana juyawa yabarsu suka qarasa dining din suka zauna tafara kallan abincin tanajin nutsuwa a ranta na duka abinda zata iya ci ne ta koshi sbd yunwa takeji karfinta ya qare ta dago ta kallesa da nuna sauran yarintarta da qaramam murya tace

"Thank you"

Daya daga cikin masu aikin ne datake da kusanci dashi na kulawa dashi sosai tin da dadewa ta iso tai serving nasu take SANAAH tafara ci farin cikin a bayyane.

Kaman daga sama Mum ta shigo gidan idanuwanta jajir kirjinta kaman zai kone sbd abinda Imran yake sake sanar mata a harabar gidan shine jirginsu ya koma karfe 6 na yamma ta rasa wannan balai da masifar daga ina suka fito gashi ta kasa samun fleet zuciyarta gap take da bugawa akan hakan.

Kai bangarensa ta nufa baya nan amma yanayin dakin nasa data gani saida tsigar jikinta ta tashi taji babu mummunan asararren dare a rayuwar irin wannan data dawo tashin hankali ya hanata kasancewa da mijinta da iya inda ya kwanta ya tashi yanayin yanda ya dan yamutse gadon ya sakata jin tsantsar kewa da shaukinsa duk da a cikin masifa take dan kuwa bataga abinda zai taba sakawa tabar Morocco batareda angama bikin Zad ba.

Fitowa tayi ta nufo babban palon gidan hankalinta na sake dugunzuma tana isa Dining room ta nufa wanda idanuwanta suka sauka akan SANAAH kai tsaye take taji a xuciyarta ta gama cire maganar batan SANAAH kwata kwata sai tagama jin dalilin sakata komawa daga bakin fleet dan haka idanuwanta a rufe ta kallesa daidai isowanta tace

"Fleet inaga na maka kira yafi dubu bana samunka duka sbd naji lafiyar abinda yake faruwa da zai saka a turani America baa gama biki ba,
Akwai matsala ne?
Nayi laifi ne?
Meyake faruwa ne?
Ni gaskia bazan komaba nice fa uwarsa komai nasa kuma....
#MAMUH
09033181070
[08/06, 2:04 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

99
Ajiye cup din hannunsa yayi saida ya bada wani irin sautin direwan da suka kallesa su dukan yanayinsa ya saka Ms meenah din shiga sabon fargaban abinda yake faruwa ta sake bude baki zata kuma magana ya katseta da asalin rashin rahama ko daya a fuskansa ya sauke mata idanuwansa yana kokarin daidaita bacin ransa da baya fatan su gani su dukan sbd a cikinsu ko ita Meenah din bata taba ganin asalin fushinsaba sbd yana hana bayyanarda hakan ga iyalinsa da tsantsar kame murya yace

"Are you for real?? A mother da kika kira kanki wannan shine kalaman farkon daya kamata ki gabatar da kanki a gabana??
An baki yarinyar mutane matar mutane kinzo da ita kinzo baki tarar da ita ba and kinzo gabana yanzu kina maganar bikin????
Are you okay?

Wani asalin mamaki da sabon tension ne taji yana rufeta daga tsaye ta juya ta kalli SANAAH wadda idanuwanta suka ciko da hawayen fargaba da tashin hankali itama ta dawo da kallanta akansa ta bude baki tace

"Na ganta ne lfy kalau babu abinda ya sameta shiyasa banyi maganarta ba amma ai......

Wani bacin rai ne ya kuma rufesa ya miqe tsaye kawai sbd bayason cigaba da sauraranta dan babu alaman hankali a zancenta dan tafiyarta tafi mata rayuwar SANAAH ya kalleta da idanuwansa da suka sauya yace

"Ki tabbatarda kin shirya yau sai kin bar Morocco umarni ne ba raayinki ba"

"What" ta fada da karfi tana shiga gabansa tana kallansa da tashin hankali tace

"No you cant do this to me fleet,me nayi ne?
Tayaya zakace ta nafi nabar hidimar bikin Zad itama SANAAH da kake magana ai ba barinta nayi ba na aiko Maleek ya kawot.....

Bata qarasaba ya juyo da wani irin kallon da sai da tayi baya kadan maganarta na yankewa ya bude baki yace

"Da aure akanta kike turo wani daukanta?
Kinsan ita wacece?
She is......

Wani irin rikitaccen kuka SANAAH ta sake a gurin hankalinta na mummunan tashi da abinda zai fada din ta dago ta kallesa idanuwanta jajir tana jin zuciyarta neman bugawa tana masa kallan da kai tsaye ya dauke idanuwansa daga kansu su dukan yana barin gurin sbd zasu iya basa bugawan zuciya ransa a matiqar bace.

Mum bayansa ta biyo batareda tabi takan SANAAH ba sbd a yanzu ta abar maganar tafiyarta da babu inda zata takeson ayi.

Yanajin Meenah din a bayansa yasan daman zata biyosa yau zai sanar da ita abinda ya kamata ta sani daya dan tasan limits dinta a wasu abubuwan bayason yayi tashin hankali da ita a gaban SANAAH ya sakasa ya baro gurin bai fada acan ba.

SANAAH datasan Abinda zai iya faruwa rawa jikinta ya dan fara cikin tsoro da shakkar tashin hankali da rashin sanin yanda zata fuskanci fammah dama mum din a yanzu matiqar ya fada ya sakata karban wayar mai aikin cikin tsananin damuwa ta saka kiran Dr Mum wadda tana dauka ta sanar da ita zai sanar da Mum

Wani tashin hankali Dr Mum ta hadiye cikeda sarawan kai sbd kuskure ne babba hakan dan wlh Meenah zata iya kisan SANAAH din ba kowa gwara abari a dawo ayi gaban iyaye da kowa.

Kashe wayar tayi tana nemo wayar Fleet din a take ta saka kiransa.

Bai dagaba yana wani irin fada mai zafi da meenah wadda taqi yadda da tafiyarta shikuma abin baqin cikinsa da takaicinsa babu komai daya tabata bayan tafiyar dan haka yana buqatar farfado da ita daga rashin tinaninta yana bude baki wayar Dr mum din dabai dauka ba ta sake shigowa bai dauka sbd baya buqatan taji yanayin dayake ciki Meenah kuwa cikin sauri takai hannu akan wayar ta dauka tareda ambatar sunan Mum din zata fara fada mata komai sbd a saka ya barta sai Dr Mum ta katseta dacewa

"Basa wayar"

Miqa masa tayi ya karba yana daidaita kansa da nutsuwansa ya juya gaidata a tsanake.

Amsawa tayi tareda cewa

"Kasan Dad dinta yana nan yana jiranmu so kayi hakurin barin saika dawo masa da ita lafiya tukuna ka sanar da matarka yarinyar bata iya tashin hankali ba"

Wani zafi ne yaji ya taso yana tafasa jininsa ya kashe wayar tareda juyowa ya kalli Meenah din baice komaiba ya fice.

Kasa motsawa tayi sbd yanayin daya shiga ya sake sakata jin hayaqin kanta duka ya sauka ta shiga fargaba da shakka mai tsananin gaske.

Fitowa tayi ta sake komawa cikin gida ta tadda SANAAH zaune a palo zuru.

Karfin hali tayi ta qaraso gurinta ta zauna tana cewa

"Meya faru ne SANAAH??

Kasa dagowa ta kalleta SANAAH tayi ta dan bude baki tace

"Ba komai jiyan da aka tafi ne ba kowa dazasu taho sai aka taho dani"

Ajiyan zuciya ms Meenah din ta sauke tana cewa

"Kada ki damu da abinda ya faru America dinma dake zamu tafi ai acan ba hayaniya zakiji dadin zama na kwanakin da zamuyi kafin mu koma Nigeria."

SANAAH da gabanta ya dan fadi dan itakam bata iya zuwa koina kuma gida kawai takeso dan dagowa tayi ta kalli Mum din daidai nan kafin tace aa fammah ta shigo palon tana ganin SANAAH ta iso da gudu ta rungumeta.

Rungumeta itama SANAAH din tayi tana sauke ajiyan zuciya na samun nutsuwan da sukunin data rasa na abinda yakusan faruwa ayau din.

Ms Meenah din bata daddara ba Abbu ta kira a waya wanda cikin saa kuwa yace mata yana hanyar isowa gida sun dawo.

Farin ciki taji ita kuwa fammah waya ta buga kai tsaye aka kawo musu kayansu da ita da SANAAH daga can gidan aka ringa jin nutsuwan anga SANAAH din wadda kowa ya yadda da cewan sbd anbarta Fleet ya tafi da ita gidan kakanninsa din.

Koda Abbu ya dawo fleet daman shine ya saka aka dauko fammah aka kawowa SANAAH din shikuma ya fice.

Wanka Mum tayi ta shiryawanta tsaf tanason tafiya gida gurin hidimar amma tanason tafara ganin abbun ya saka a soke tafiyarta tukuna.

Sai da Abbun ya huta sosai bayan sallar azahar har yaci abinci yana hutawa yasaka a kirata din tazo tinda yasan tanata jiransa.

Zaunawa tayi gabansa bayan ta masa sannu da zuwa ta fayyace masa komai tana rokonsa dan Allah ya saka abarta ta qarasa.

Nasiha Abbun ya mata amma ta nace da roko dan haka yace shi ya barta ta qarasa bikin amma SANAAH da fammah su zasu tafi America din su zauna acan kafin ta gama duka abinda takeyi ta samesu acan daga can sun koma gida.
Chapter 103 · 0% Book details