← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 154

Sashe 75

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan damqe hannunta dayake karkashin nasa yayi ahankali yana bude baki baki yasake cewa

"Uhummm ina sauraranki ok?
Just tell me you say"

Mutuwa jikinta yakeyi sbd gangar jikinta ta kasa daukan deep voice dinsa dake shigarta direct cikin kunnuwanta tareda dumin dayake narkar da kuzarinta da karfin halinta ta bude idanuwanta da baya iya riqe kansa daga kallan cikinsu ta girgiza kai a hankali da rashin karfi tana rasa abin fada.

Hannunsa daya yakai ya dago fuskanta a natse ya saukar mata da idanuwansa da suna saukan mata taji saukansu tayi qasa da idanuwanta tana dan riqe numfashinta dayake fita da sauri sauri.

Wani azababben kallo ya sakar mata kafin ya sake bude bakinsa ya jefa mata wata tambayar data sake sakata girgiza kai tana dan qanqame hannunta dayake tareda nasa har lokacin.

Bakinsa ya maida kan kunnunta tai saurin qanqamesa tana janyewa da karfi fa juya masa baya har lokacin yana zagaye da ita ya sake jefa tambayar a cikin tsakiyar kunnenta take wasu hawaye suka zubo mata sbd azabtuwar datake yi da galabaituwa ta sake girgiza kai ta bude baki da tsananin sanyi da kasala tace

"I dont know pleaseee" ta qarasa da wani sanyayyan sautin daya masa wata muguwan ratsan daya manno bayanta sosai da kirjinsa suka hadu sosai cikin sanyi da slow tareda sake zagayeta da hannuwansa duka biyu daya a sama daya akan cikinta suka rufe idanuwansu a tare tana sake dan girgiza kai ahankali ahankali.

"Kina da say??

Girgiza kai tayi

"Kinada wani raayin??

Girgiza kai ta kuma yi

"Do you have someone in.....

Girgiza kai tayi batareda ya qarazaba tana qara rintse idanuwanta da karfi sbd yanda kowace tambayarsa take fitowa da wani sautin da bata taba jiba da qarin kaurin deep voice dinsa.

"Kina zabi??

Girgiza kai tayi

"Kina buqatan rabuwan aurena dayake kanki??

Girgiza kai tayi batareda tasan tanata girgiza kai ga duka abinda yake tambayaba da wanda take ganewa da wanda bata ganewa.

Cak ya tsaya da tambayar dayake jera mata su a jere da tsantsar buqatan jin amsarta da raayinta.

Kafe fatar bayanta yayi da ido sbd amsarta ta karshen data tsayar da kalamansa cak.

Juyi daya yayiwa qaramin qugunta dayake hannunsa ya birkotota suka fuskanci juna a hade sosai ya kalli bakinta dayake fidda wani moist da shining na lip balm kadan ya yiwa cikin idanuwanta da suka bude a slow wani mayen kallo kadan ya bude baki baki da sautin da bai taba kamata ace ta jisa ba yace

"Ki Amincewa raba auren??

Sake girgiza kai tayi kai tsaye batareda fahimtar tambayar ba saida taji ya dauke wuta ta bude idanuwanta ta kallesa take tambayar ta dawo mata cikin kai ta bude baki da sauri zatai magana shi kuwa daya gama kaiwa karshen jin amsarta cikin notin kansa na karshe rankwafowa yayi yana qarasa mannota jikinsa gabaki daya da hannunsa daya yayiwa fuskanta wata kamowa da hannu daya yana rufe bakinta da nata data bude zatai magana ya fara sakar mata niimtacciyar iskar bakinsa mai wani qamshin tada tsigar jiki kafin ya zira bakin cikin nata gabaki daya yana kama fatar lips dinta yayiwa wata light tsotsa kafin harshensa ya hade da nata yayi masa wata lafiyayyar tsotsa yana sake mannata a jikinsa tukuna yafara mata wani lafiyayyan kiss din daya sakata bude idanuwanta gabaki daya sedai bata ganin komai ganinta a take ya dauke sbd tsoro da jin abinda bata taba jin yana faruwa da itaba.

Kwacewa takeson yi amma jikin babu inda yake iya motsawa sbd irin riqon dayayi mata kirjinsu a manne yake hakama wani irin kiss dayake mata yana hada kowane irin digon yawun dayake bakinsu suna zamowa daya cikin slow da wata irin qwarewa da motsa kowace daskararriyar jinin dayake jikinta.

Dan haka ta kasa motsawa bare iya kwacewa saida taji tana neman rasa kanta gabaki daya ta iya bude ido ta zame bakinta ahankali tana kasa dagowa komai na jikinta a mace ta juya baya da sauri batareda ta waiwayoba ta daga kafafunta daqyar kaman jiri zai dibeta ta nufi kofa da sauri ta fice qamshin jikinsa dana bakinsa duka tashi sukeyi a jikinga.

Tana fitowa palo hijabinta ta dauka ta saka hannuwanta na dan rawa bata tsaya tattara kayan dasuke zube a qasan ba ta nufi kofa ta fice kirjinta na bugawa kaca kaca ba daidaiba.

Tana isa kofar bangarensu jin tayi gabaki daya bugawan zuciyarta ta qarasa rikicewa.

Saka kai tayi ta shiga tana kokarin daidaita bugun zuciyarta da ake iya ganin yanda kirjinta ke sama yana qasa kota cikin hijabin...

Tattara karfin hali da nutsuwanta tayi ta shigo tana kasa kallan kowa a cikinsu tai sallama ta wuce hanyar bedroom dinsu a natse.

Dr Mum ce ta bita da kallo tinda ta shigo harta bace batareda itama tace komaiba kafin ta maida idanuwanta akan Meenah da har lokacin fira take hankali kwance ta bude baki tace

"Ki tashi kije dare fa yayi sosai kin manta kinada miji ne"

Dariya Meenah din tayi tana cewa

"Da fammah zamu jira tinda naga kaman SANAAH ta wuce yanxu ta dawo"

Takaici ya saka Dr Mum mata fada kadan kafin tace ta tashi ta tafi su sun taho daga bayan.

Miqewa tayi ta bar bangaren.

Tana fita fammah na shigowa sbd Dr Mum din data kirata tace ta dawo su tafi su kwanta dare yayi.

SANAAH tana shiga dakin Mommy kayan jikinta dake qamshinsa sosai ta zare ta sauya wasu kayan da hijab tana gama sakawa Fammah ta shigo tana kallanta.

Dagowa tayi ta kalli fammah itama so daya saita kasa qarawa ta dauke idanuwanta da suke cikeda sanyi da kasala har lokacin tayo gurinta.

Fammah bata ce komaiba sbd ta saba da shawagan SANAAH din ta dauka itace ta tashi dan haka fitowa sukai a tare sukai musu saida safe suka fice har Lokacin SANAAH bata iya kallan kowa a cikin su Dr Mum din har suka fice.

Suna fitowa ta lafe gefen Fammah tana sauraron famman daketa zuba har suka isa bangarensu sabo suna shiga ta wuce bedroom da sauri sbd motsin fitowan mum dake shirin wucewa bangaren mijinta.

Tana shigewa komai bataiba gado ta haye ta kwanta tana yin shiru a lafe hannunta na kan cikinta dayake mata dan sauran zafi kadan.

Bacci ne ya dauketa da abubuwa dayawa cikinta data kasa sanin ina rayuwar yanzu zatai da ita.

Washe gari tinda safe ta silale tabar bangaren dan kada ma ace atafi breakfast.

Gurin su mommy tayi tana isa dukansu basu tashi ba gashi kusan 9 ta wuce dan haka daman tayi wankanta tana sanye da riga da skirt na atampa masu kyau ta nufi dining da aka gama shiryawa bata zauna ba daga tsayen ta dan bude tana saka wasu abubuwan abakinta tukuna ta bar nan tayi kitchen.

Maamah ce ta fito tana waya da ta nufo kitchen din ta tadda su tana ganin SANAAH tace yawwa gama SANAAH bari taje ta dubo kitchen din bangarenasu ko kuma Mum din tasu.

Kashe wayar tayi tana kallan SANAAH tace

"Kije ki duba kitchen dinku RAHEEM yana buqatan ko simpl breakfast ne tafiya zaiyi"

Kallan Maamah SANAAH tayi gabanta na dan faduwa da shakkar zuwa amma dole jiki a mace tace "to" tareda juyawa ta fice.

Tana isa bangaren nasu kai tsaye dakin Mum ta nufa tinda ance wayoyinsu duka basa shiga fleet din yayita kira gwara kawai ta sanar mata ta tashi taje.

Knocking tayi shiru shiru tsawon mintina dan haka ta bude kofar dakin ta shiga duhu alaman bacci takeyi.

Daurewa tayi ta isa bakin gadonta ta ambaci sunanta da nutsuwa kusan so hudu tukuna ta amsa tareda dan bude idanuwanta tace

"Baby SANAAH lafiya dai ko??

Cikin sanyi ta bude baki tace

"Eh Anyita kiran wayanki ne bata shiga shine akace nazo na fada miki Dad yana buqatan breakfast kije"

Numfashin bacci ta sake tana dan bude idonta kadan dayake cike da bacci tace

"Banfa dade da barowa ba kaina yana ciwo sosai so please Baby SANAAH ki hada masa kikai dining kinji"

Shiru SANAAH tayi tareda nemo karfin hali tace

"Mum ki.....

Katseta tayi da cewa

"Please kaina yana ciwo kawai ki kai masa kinji"
#MAMUH
09033181070
[16/05, 6:43 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

70
*NOOR COLLECTION*
09035841194
Best luxury shop da zaku samu kayan da zaa san kun saka sitirar alfahari masu best quality kamar su;
ABAYA'S
JALLABIYA
SNEAKER'S
KAYAN YARA
NEW BORN BABIES ITEMS
MAYAFAI (veils)

Hakama ko ba abinda muka lissafo ba ana iya turomana orders din wasu abubuwan idan anaso,

Our addresses sune;
EGYPTIAN ADDRESS: NEW CAIRO.
NIGERIAN ADDRESS: Zaria, low-cost, prof Adam sa'id resident.

PHONE NUMBER:
+234903 584 1194
+234 704 420 4680
Whatsapp.
LINK, https://whatsapp.com/channel/0029Vaoa1YN77qVImYa4ZF02

*********
Wani irin nauyi kirjin SANAAH yayi da kafafunta sbd tariga ta sake shiga tsaka me wuyar da bazata iya dauka ba..

Juyawa tayi ta fito idanuwanta na sauyawa da damuwa a cikinsu da sauyawan bugun zuciya sbd tin jiya har yau kunnuwanta da zuciyarta basu dena jin halinda ta samu kanta a jiyan ba shiyasa ma ta gudu sbd idanuwanta bazasu sake daukan iya ganinsa ba sbd raunin da zata iya samu.

Kitchen ta isa da kyar ta tadda masu aikin sun gama komai sun shirya a dining da tsananin sanyin jiki da damuwa ta buqaci gurin da zata hada masa komai takai.

Hadawa tayi ta koma dakinsu dan tada fammah takai amma tana zuwa dakin taga yanda famman ke bacci mai karfi cikin nutsuwa saita kasa tadata ta yanke mata baccin ta kalli fuskanta cikeda kulawa da kauna ta miqe ta juya ta fito taje ta dauko abincin ta fice tana tafiya kaman bazata kai ba.

Tana isa sai data sake tsayuwa a bakin kofar shiga palon bangaren taji tana sake shiga damuwa da mutuwan jiki amma batama san bata lokaci akan abinda tasan sai takai dan haka ta fidda numfashi mai sanyi da nutsuwa tana bude kofar ta shiga a tsanake tareda rufewa ta daga kafafunta ta tinkari hanyar dining room.
Chapter 75 · 0% Book details