← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 154

Sashe 117

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aa fammah kece kadai kika tashi?
Ina SANAAH da Mum dinki basu farka bane?
Jiya ma ko dana ga SANAAH a asibiti gurin masu awon ciki na dauka tare kuke ashe ita da Safiya ne ko ganina basuyiba Allah yasa dai lafiya?
Meya kaisu gurin masu ciki?
Waye ba lafiya??

Da mamaki fammah ta dago ta kalleta tana ma kasa daukan bayananta dan haka sai kawai ta gaidata tace ai Mum bata fitoba.

Wani zancen ta kuma kwatsawa cikin nutsuwa da rashin nuna damuwa da hikima kafin ta juya ta fice tana cewa daman zuwa tayi su gaisa da Meenah tinda suka dawo basu gaisaba.

Tana fita bin bayanta da kallo fammah tayi tana mamakinta da maganganunta marasa lissafi.

Ficewa taso yi zuwa bangaren su mommy amma kuma sai zuciyarta ta sakata juyawa dan dubo katin asibitin SANAAH dayake dakin cikin wata jakarta qarama dan ganin yana nan ko asibitin sukaje da gasken batareda ta fada mata zataje ba tinda kusan tare suke komai.
#MAMUH
09033181070
[15/06, 9:55 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

115
Mommy na isa kofar dakin Dr mum sauke ajiyan zuciya tayi a natse tareda dan bugawa kafin ta bude kai tsaye tana shiga da sallama a bakinta ta nufo tsakiyar dakin daidai lokacin Maamah data biya ta sanar da tanada magana dasu ta iso dakin na dr mum itama ta shigo tana kallan mommyn kafin ta isa ta zauna akan sofa Dr Mum na zaune akan bakin gado ta gama waya kenan da Abbu ta bisu da kallo su dika biyun tana cewa

"Lafiya dai na ganku haka a jere kaman jiki a mace"

Maamah data zauna ce ta bude baki tace

"Zainab ce tace da akwai maganar dazatai damu"

Kallan mommyn sukai duka wadda ta qaraso ta zauna a kan sofa itama tana sauke ajiyan zuciya babu batawa kowa da kanta dayake cikin nauyi lokaci ta bude baki tana dan kasa kallansu su dukan tace

"SANAAH taje asibiti yau akan ciwon datake fama dashi dashi ance ciki ne da ita tsawon wata biyu da satika"

Da wani irin azababben sauri su dukan suka kalleta Maamah dake kusa da ita dafata tayi da sauri hannunta na dan rawa tsabar rudewan jin zancen kaman daga sama abinda suka gama cirewa rai har abada dan haka kokarin bude baki tayi zatai magana sai kuma tama rasa abin fada ta kalli Dr Mum wadda tayi mutuwan zaune cikeda wani irin shock itama dan kuwa kaman bata gama yadda ba sbd Allah kwata kwata bai bata tinanin hakan ba da duba SANAAH din sosai dan haka zubawa Mommy idanuwanta tayi tsawon lokaci kafin Maamah ta yanke shirun da cewa

"Ciki dai cikin haihuwa??
Wani 'dan Raheem zan sake gani a duniya??
Ya Allah kasa ba mafarki nake ba"

Mommy Numfashi ta sauke tareda bude baki a dan sake da jiki sbd ba wai farin cikine batayiba abinda zai biyo bayan bayyanar cikin ne tashin hankalinta tace

"Yaya zaayi da cikin Sbd Meenah da batasan da aurenba haryanzu tukuna???

Wani kallo Dr Mum tayi mata batada energy sam sbd yanda zancen cikin ya daketa ta bude baki tana kallan mommyn da kyau tace

"Yaya zaayi kikace zainab?
To kodai kema bakida lissafin ne kaman Meenah da har kike iya tambayar yaya zaayi,
Yanxu dai ni ina buqatan son duba SANAAH da kaina da kyau na tabbatarda zaman cikin tukuna na fadawa Meenah da kaina dan gwara ta sani dan renan ciki kam ya zama dole a bayyane ba kowace boyo"

Wayarta Mommy kasa tayi da kanta tana yin shiru har Maamah ta miqe tana jin wani irin tsallen da kirjinta ke yi da zuciyarta ke bugawa tana fatan itama ayiwa SANAAH din sabuwar dubawa su tabbatarda idanuwansu ko zata samu jin abinda ya tsayar mata da komai cak ya watse cikin tsantsar godewa Allah da asalin farin cikin da suke jin ba iya dan SANAAH da Raheem bane hadda kaman dan Nasir ne suke ganin kaman zasu gani sbd mutane biyu dayafi so ne a kaf duniya zasu haifar masa 'da ko yar da dayana duniya zaifi kowa so.

Fitowa Mommy tayi tabaro dakin tana komawa dakinta inda ta tadda SANAAH da safiya dake kokarin hada mata dan tea cikin kulawa da tsananin tausayi da mutuwan jiki ga dukansu itama guri ta nema ta zauna a dakin batareda tace musu komaiba ta dauki wayarta tana saka kiran Al'amin da basu taba boyewa juna komaiba tana tinanin fada masa ko kuma barinsa yaci gaba da aikinsa cikin nutsuwa kada ta damar dashi duk da tasan bazaiji komaiba tinda an nuna masa shi cewan SANAAH din ta jima da tarewa sbd hanasa damuwan zamanta gida har lokacin.

*******fammah kuwa tana shiga dakinsu inda jakunkunansu suke a jere ta nufa ta fara duba jakar SANAAH din datasan takardunta suna ciki taga bata ganta ba dan haka ta dan dakata tana tinanin da gaske hajiyar uncle Samad din take kenan SANAAH taje asibiti ko me??

Wani irin nauyi kirjinta yayi kanta ya sara da dan karfi ta fitarta wani numfashi mai dumi da fitarda kowace irin tinanin yadda da kowace maganar kowane dan adam mara kyau akan SANAAH dan haka tayi kokarin yakice tinanin a kanta ta juya ta fice daga dakin tana jin takaicin Hajiyan Samad din dataso saka mata wani mahaukacin rashin tinanin wai SANAAH a gurin awon ciki.

Tana isa bangaren su Mommyn kai tsaye dakin mommy datasan SANAAH na ciki ta nufa.

Tana shigowa dagowa Mommy tayi ta kalleta tana dan kokarin sakewa da faraarta tana amsa gaisuwanta tana tambayar Mum dinta.

Gurin SANAAH din fammah ta kalla wadda ta dago ahankali ta kalli fammah din jikinta babu kuzari ko daya idanuwanta suka si cikowa da wasu irin hawayen data kasa riqewa ta sauke kanta daga kallan Famman tana dan lumshe idanuwanta ta rufe.

Mutuwa jikin fammah yayi itama taji duk damuwa da haushin kanta ya rufeta data iya bin maganar Hajiya harta je bincika dan haka ahankali ta tako ta iso gurin SANAAH din ta zauna a gefenta tareda kwantawa jikinta ahankali tana cewa

"Allah ya baki lafiya My Baby SANAAH"

Wani irin nauyi da damuwa ce ta sake dirowa SANAAH din ta sake rufe idanuwanta tana dan kwantawa jikin fammah din itama batareda ta iya cewa komaiba.

Fammah dataji wani irin zafin zazzabin dayake jikin SANAAH din mai tsanani qara rungumeta tayi tana shafa bayanta ahankali tana mata sannu.

Safiya ficewa tayi daga dakin tana barinsu ta nufi kitchen inda ta tadda mommy tana aiki ta saka hannu suna aiki kowannensu shiru ga abin farin ciki amma tsoro ya hanasu bayyana hakan kuma tsoronsu duka akan abinda zai samu SANAAH ne da bazasu so komaiba.

Suna dakin Dr mum ta shigo duba SANAAH din tana binta da wani irin kallan dayake bayyane da wata irin sabuwar kaunar data kasa boyuwa a idanuwanta taji idanuwanta itama kaman zasu ciko da hawayen data hanasu fitowa dan kuwa ayau indai da gaske ciki ne a jikin SANAAH burinta dana mahaifiyarta zasu cika na samun wata haihuwan a jininsu dasu Allah bai basu ba,
Mahaifiyarta ita kadai ta haifa hakama itama shi kadai Raheem din ta haifa shima sun riga sun fidda ran sun gama yadda da Fammah ce kadai kwansa a duniya da zasu gani wadda ita mace ce wani gidan zata tafi aure ta haifa musu yayan acan wainda ba nasu bane ashe sunada rabon shedar da wani tsatson nasu faga Raheem.

Irin kallan da dr mum kewa SANAAH din ya saka Fammah juyowa ahankali ta kalli SANAAH wadda tai qasa da kanta jikinta na kuma mutuwa sosai.

Kallan Fammah dr mum tayi da kulawa da kaunar datake jin tana mata da ita sa cikin SANAAH din tace

"Fammah ki bawa Rabin ran taki dan dama kadan na dan je wani guri da ita kinji,yanzu zamu dawo ba jinawa"

Kallan SANAAH din tayi da dan boye mamakinta ta saki murmushi kadan tace

"Ok Dr Mum saikun dawo Allah yasa asibiti zakuje a dubata sbd jikin nata dai lafiya taqi kuma koni naso dubata amma taqi yadda"

Murmushi Dr mum din tayi tana maida kallanta akan SANAAH tace

"Ganin takeyi kila kauna bazata bari ki dubata da kyauba"

Dariya famman ta dan yi kafin ta taimakawa SANAAH din ta saka doguwan hijab suka fice.

Suna fita Driver ne yaja su a mota sai asibitin da rabonta da ita sama da shekaru batasan iyaka ba dan kuwa asibiti ce tin asalin farko an ginata ne sbd ita sbd tayi aikinta a cikinta wadda aka sauyata gabaki daya dan kusan an rusata anyi sabon ginin da akai akai ake sauyasa komai a tsare da kyau kaman baa qasar Nigeria ba.

Kai tsaye office din Dr Akin data kira tin kafin su iso ta nufa da SANAAH din wanda shima tinda ta kira ya fito hanyar office din dan tarbanta sbd tin a shekarun baya shine likitan dayake karkashinta gashi yanxu shine babba anan din gabaki daya sai Dr bushrat a mata dan haka akwai sanayya sosai tsakaninta da Dr Akin din.

Yana ganinta da girmamawa da farin cikin ganinta ya iso ya tarbeta suna wucewa kai tsaye office dinsa.

Bayan gaisawa da yan maganganunsu na likitoci kai tsaye abinda tazo yi suka fada wato duba SANAAH din da kanta dan haka waya yayi aka kawo masa scanning machine har office dinsa anan Dr Mum din ta nutsuwa ta zauna da kanta taiwa SANAAH din scanning ta duba komai tana gamawa wani lafiyayyan numfashi mai asalin nutsuwa da mutuwan jiki ta sake zuciyarta na cikuwa da dukkanin farin cikin da rayuwarta ke nema da buqata dan kuwa daga karshe dai zata samu qarin zuriarta datake jin ba iya nan zuriarta zata tsaya ba SANAAH zata basu farin cikin da zai cika zuriarsu insha Allah.

Bataji nauyi ko wata iyakancewaba rungume SANAAH din tayi ahankali tareda kissing tsakiyar kanta tana mata addua da wata irin kauna mai tsananin tsananin karfi ga cikin ta gasken gaske.

SANAAH data sake shiga kunya da tsaka me wuya bata iya warwareba saima jin datai zazzabinta ya qaru dan haka koda suka dawo gida shigewa tayi tai sallah daqyar ta kwanta tana dunqulewa.
Chapter 117 · 0% Book details