← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 154

Sashe 135

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**********
Bayan tafiyarsu SANAAH fammah ta gane SANAAH haryanxu tanada kusanci da zuciyarta duk da abinda ya faru hakama Dad dinta yayi magana da ita ta fahimta sosai ya kuma bata hakuri da komai ya mata nasihar data sake sakata rungumar kaddara ta karbi auren nasu da SANAAH dik da tanajin wani lokaci daci sbd Mum dinta amma tana kokarin addua shedan ya hanata yin abinda zatai danasani.

Kadaici da damuwa ce ya fara dawo mata sbd yanzu Ya Al'amin sedai ya jeta ya tafi gurin aiki amma kulawansa da tattalinsa ko daya be dena ba kawai dai ya zama busy.

Kullum idan ya dawo zai kirata a waya suyiga waya yana aiki yana debe mata kewa sbd fahimtar kadaicin dayake kokarin tabata ya kuma taba karatunta.

Yawan wayan da sukeyi ya saka ta saba ko karatu zatai idan ba suna waya tana karatun ba sai taji bata iyawa hakama shi kansa yanxu waya da ita ya saka kome zaiyi sai yana yi yana kallan wayarsa,

Shaquwarsu ta fara sakawa ake mata kallan matarsa kaman yanda shima ake masa kallan ita matarsa ce gashi zuwa yanxu abubuwan dake rabasu a waya kalilan ne.

SANAAH dake Miami tana wata irin rayuwar da daga ita harshi basu taba samun kansu a ciki ta fahimci shaquwan dake tsakanin Ya Al'amin din da fammah ta fara zama kaman abinda bazasu iya rayuwa sai dashiba dan haka take tausayinsu dan alaqa a tsakaninsu kaman bame yiyu bace sbd Mum din fammah tafison tayi kukan rashinta data bari Ya Al'amin ya aureta dan haka sai batama saka zancen itama a ranta ba bare ma ya tabbata.

******
Nigeria
Can baya a ranar dasu Fammah suka wuce cikin wani samun sassauci a kirjinta na wucewan yarta Ms Meenah ta kasa barin gari ya waye ta fito cikin sauran duhun asubar ta nufi kitchen ta kunna gas tabarsa a bude batareda ta kunna ashana ba rufe koina tana rufe kofar baya da masu aiki zasu shigo ta fice daga bangaren ta nufi na Fleet wanda shima kai tsaye ta bude da password ta shiga ta nufi kitchen ta kunna gas tabarsa a bude ta fito ta nufi palonsa na kurya ta bude kofar ahankali ta taka tana isa kofar bedroom dinsa idanuwanta na yin jajir da wani irin zafi da wutar dake cin jininta ta saka hannu ahankali ta bude kofar dakin kadan bata tsaya ta tabbatarda akwaisu a ciki ba ta juya ahankali ta fice tana barin bangaren gabaki daya.

Bangaren Hajiyar Samad ta nufa wadda tana isa hajiyar na fitowa daga dakinta tana waya muryanta na dan tashi da farin cikin jin labarin Fleet yabar qasar da SANAAH daga daya daga cikin securities din gidan dayake waya da ita sosai a bakinsa takejin fita da shigowan kowa villah din.

Babban farin cikinta na jin zancen shine idan Meenah taji dika kullin haukarta kuncewa zasuyi tayita haukan da babu sauki dan haka fitowa tayi dan karyawa dan daman ita tin 7 take breakfast dinta.

Ganin Meenah na shigowa palon ya sakata kallanta da dan mamaki tana kashe wayarta sauran farin cikin a fuska bayyane sosai tace

"Aa Meenah kece da Sassafe haka?
Allah yasa ba wani kika kashe?

Katseta Meenah din tayi da wani kallo da idanuwanta da har wani ruwa suke tarowa sbd jan da sukai ta bude baki tana qarasowa tace

"Ban kashe ba amma ai dole kowa zai mutu tinda mutuwan na kan kowa,
Wata mutuwan idan anyi duk yanda ake qinka ai bazaace kaine kayiba tinda baa ganka ba"

Wani kallo hajiyar Samad din tai mata tana juya zancenta da sam bai mata ba ta juya tana nufar dining da masu aikinta yan wahala tinda duhun asuba suke fara aiki tace

"Me kike nufi ne?
Kinsan dai yanxu kada ki kuma gwada kisan wani a gidan nan dan kuwa babu alkhairi a kowace aikin dan barazana ce ga nawa dan dani kaina"

Wani baqin ciki da zafin samad dinne ya taso ya danne kirjin Meenah din sbd yanda yake tsananin son SANAAH shima babu abinda bazata iya masa ba dan haka bata kalli Hajiyar ba tai shiru tana fatar a samu wanda zai kunna wuta a tsakanin bangaren biyu tasan wutar bazata bar har bangaren Samad ba.
#MAMUH
09033181070
[22/06, 2:57 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

134
Dakatawa hajiyar tayi sbd jin zuciyarta gabaki daya ta juye da wani fargaba da zuwan Meenah din bangarenta tinda sassafen dan haka ta juyo tana sake kallanta taga yanda idanuwanta sukai muni sbd ja tasan babu abinda zai saka Meenah magana da hauka bayan jin tafiyar Fleet dan haka ta bude baki tana kallan cikin idanuwanta tace

"Kinsan FLEET da SANAAH sun bar qasar ayau din suma?"

Wani irin kallo Meenah ta sauke idanuwanta akan hajiyar tana mata idanuwanta na cikowa da wasu azababbin hawayen wutar dataji ta kama a kirjinta ta girgiza kai tana bude bakinta dayake yanke magana tace

"Bai tafi koinaba suna can kwance gas yana huda kowace iskar da suke shaqa"

Da sauri Hajiyar ta kalleta tace

"Gas kika saka musu??
Me kike nufi??
Wlh baya nan sunyi tafiya ya tafi da ita sun tafi yawon duniya"

Girgiza kai Meenah tayi da karfi tana jin tinaninta na kasa dauka zatai magana hajiyar Samad dataji hankalinta na tashi da barin jikinta tsabar neman rikicewa tace

"Gas naji kin ambata?
Kunna musu zakiyi kokuwa harkin kunna din??

Cikin zafi ta gyada kai tana cewa

"Me zaki musu?
Zaki sake zuwa ki fasa ihun neman cetone kaman yanda kikai wancan karan?
Karki manta duk abinda nayi yanxu tare muke....

Da wani sautin dayake tafe da tsantsar baqin ciki da tashin hankali hajiyar tace

"Kin kunna dai kenan kike nufi???

"Eh kuma....

Hajiyar bata jira sauran zancenba ta tureta da karfin gaske tana nufar kofa ko takarmi bata iya sanin yaya ake sakawaba sbd yanda idanuwanta suka rufe a take duka jikinta wata muguwar rawa yake dauka bakinta na furta

"Allah ya debe miki albarka Meenah ya kuma debewa larabawan kasarku gabaki daya tattalin arziki,irin masifa irin balai"

Da gudun gaske ta isa bangaren Samad dake kusa hanya daga bayan na Fleet.

Tana isa hannuwanta har rawa suke ta bude kofarsa ta fada tana shiga dakinsa ta nufa tanajin warin gas yana ratsowa har nan dan haka ko gani bataji ta fada dakinsa daidai fitowansa wanka kenan daga shi sai gajeran wandon daya saka ta damqi hannunsa tana janyosa da karfi tana cewa

"Yi sauri kowane lokaci bomb tashi zaiyi  a bangaren nan"

Kwace hannunsa zaiyi tai masa wani mahaukacin riqo tana janyosa da daga harshenta cikin tsananin tashin hankali

Rigarsa ya janyo tana jansa yana sakawa ta fito dashi shima a lokacin yaji warin Gas sosai dan haka da kansa ya cira kafafunsa suna barin gurin da gudun gaske.

A cikin bangaren su Dr Mum kuwa tini gas din yafara shiga koina yana shiga cikinsu sosai take oxygen yafara kokarin yanke musu dan haka da wani irin tashin hankali da yajin idanuwa suka fara fitowa a palon sukaji abinda yafi karfin hankali dan haka tini Dr Mum ta zube kasa tana wani irin tarin dayake neman tafiya da ranta.

Maamah ce ta kamata da sauri itama tana jin numfashinta na yankewa ta fara kokarin miqar da ita.

Mommy da Safiya da suka fito ma da gudu Mommy tayi kitchen tana toshe hancinta sbd numfashinta daya fara yankewa.

Safiya kuwa kofa ta isa ta bude da karfin gaske tana dawowa ta bude windows tana jin jiri kaman zai zubar da ita ta fito da gudu ta fita cikin ihu ta nemi jaama wanda ihunta da neman agajinta ya saka securities fitowa sa sauri suna yowa nan daidai nan hajiyar Samad dashi suka fito da gudu suma take kowa ya fahimci abinda yake faruwa.

Da gudu akayo nan.

Mommy tini ta kashe gas din Amma bata iya fitowa ba da kanta sbd jiri da toshewan numfashin daya zubar da ita.

Dad jeerah dake kwance yaji ana ihu da hayaniya sarawa kansa yayi yana rintse idanuwansa da wani irin nauyin kirji sbd da alama an kusa kashesa da bugawan zuciya a cikin gidansa dan haka saukowa yayi yana zira jallabiya ya fito tinda dai baiji ana ambatar mutuwan Dr ba kaman wancan karan.

Koda ya iso tini aka fito da Dr Mum wadda numfashinta yake ya kewa kaman mai asthma.

Da tsananin mamaki da shock yake tambayar kafin ma a basa amsa yaji gas din dan haka take ya bada umarnin koina kada a kunna wuta a villah din.

Bangaren Raheem aka nufa da tashin hankali sbd jin yana fitowa harda tacanma.

Daqyar aka iya shiga aka kashe ana bude koina shima tareda sauke kowace labule sbd ya futa yabi iska da kyau.

Jikin Dr Mum rawa yakeyi sosai tana sake rasa numfashinta dan haka kai tsaye bangarensa yayi da ita yana sakawa aje da gaggawa a kawo masa doctors.

Umma dake bangaren ta shigo kawo masa breakfast kenan ta tadda Dr Mum a palonsa tana taimaka mata gurin dawo da numfashinta ta hanyar huta mata wani iska mai sanyi daga bakinsa zuwa fuskanta yana jin kaman ya sakata jikinta ya basa iskan bakinsa dakyau amma hakan ba dama.

Cak Umman ta tsaya daga inda take a tsaye da kaya a hannunta tana kallan Hakeem din da idanuwanta da sukai jajir tana jin wani nauyi na danne kirjinta wanda ya jima a kirjinta ba tin yanzu ba akan alaqar Hakeem din da Dr fammah.

Doctors biyu ne akai gaggawan tahowa dasu dake anguwan sbd dr bushrat ta riga tana asibiti.

Dubata sukai aka dawo da numfashinta daidai suka tafi aka barta a palon kwance cikin da wata irin rashin kuzari.

Dad na shigowa bayan ficewansu zaunawa yayi ya zuba mata manyan idanuwansa da sukai jajir sosai wani radadi da zafi na danne da kirjinsa dayakejin dukkanin riqewa da jarumtarsa ta shekarun tin kuruciya suna tsinkewa daya bayan daya har karshe ya bude bakinsa da wata murya mai tsananin kauri da bayyanarda radadin da kirjinsa yake ciki na abinda ya farun wanda rashin mallakarta ya saka yake kasa bata wata kariya da gaggawan datake tasowa a rayuwarsu idanuwansa a cikin nata ya saka da wannan strong voice din yace
Chapter 135 · 0% Book details