← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 154

Sashe 21

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan lokacin ne masu rescue suka samu bude hanyar suka iso hankali tashe suka zare karfen daga wuyan Nasir ya fadi qasa kwance Raheem yayi saurin taresa jikinta koina nasa na rawa sam sam baya hankalinsa ya rasa kansa gabaki daya.

Karfinsa ya saka kawai ya sunkuci Nasir din yana kokarin ficewa dashi ana kokarin taresa amma sam babu wanda ya iya taresa bare karban Nasir dan haka wasu suka biyo bayansa da sauri ana cewa bude Ambulance duk da sunsan kai tsaye Babu rai a tattare da Nasir din amma ba alaman Raheem jeerah yasan da hakan san haka kowa ya sake shiga damuwa ganin yanda yake gudu da gawar yana tsiyayar jini daga fuskansa shima.

Karban gawar akai da gaggawa ana kokarin basa taimako shi dayake da rai amma sam yakasa tsayawa ya kuma kasa magana har lokacin komai na jikinsa jijjigar rawa yakeyi yana nuna musu Nasir din.

Kasa riqesa kafafunsa sukai ya sake sarewa qasa akan gwiwowinsa a gurin sbd ganinsa daya dauke dip hakama jinsa take ya zube gabaki ba alaman rai a jikinsa shima.

Daukansa akai da sauri akai asibiti dasu da sauran familynsa da suma tini akai asibiti dasu da wainda aketa fiddowa dad ma an fiddosa anyi asibitin dashi.
#MAMUH

GANIN IDO
1K
VIP 5K
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

21
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Gabaki dayansu babu wanda ya farfado sai bayan tsawon lokaci dan kuwa saima tsakiyar dare sosai Dr Mum ce tafara farfadowa tana sake tabbatarda Nasir ya rasu yabarsu sai data sake yankewa ta fadi aka riqota ta fasa wani irin kuma mai tsananin tsima zuciya koina nata na mugun rawar da saida nurses din kanta suka sauke kai sbd mutuwan jiki.

Kuka takeyi sosai tana jin kaman zuciyarta zata fashe,
Kukane dayake ratsa kunnuwan duk wanda yake dakin da kusa da dakin,
Kukane dayake ratsa har kunnuwan Sir hakeem jeerah dake dakin kusa da ita yana jinsa har kirjinsa shima tareda radadin dayake yanka kirjinsa sbd kusan jinin Nasir babu wanda bai zubarwa ba a cikinsu,
Radadi ne da harsu mutu bazasu manta ba sbd yayi wannan mummuman rasuwar ne gurin cetar da ransa dana 'dansa wanda yasan bazai taba fita trauma rasa rabin jikinsa ba harya mutu ya bar duniya.

Ko da Raheem jeerah ya farka bai motsa ba idanuwansa kadai ya bude ya zubawa matarsa da fammah dasuke dakin zaune idanuwansu jajir da alama su babu abinda ya samesu.

Kukan mahaifiyarsa ne yafara ratso kunnuwansa cikin wani irin sanyin slow yana shiga kunnuwansa,

Idanuwansa cak suka tsaya basu motsawa kaman yanda ko kyaftawa sun kasa yi sai jikinsa ya sake fara rawa ahankali ahankali harya fara tsanantar da meenah ta fashe da kuka mai ratsa zuciya tana furta masa kalman hakurin daya saka hatta gadon dayake kai jijjiga yakeyi dole aka kira doctors da sauri.

Yanayinsa neman munana yakeyi wanda ya saka dole aka dinga banka masa allurai masu karfi haryayi baccin dole da wahala amma wasu hawaye masu tsananin zafi da siranta ne suka ringa gangarowa gefen fuskansa a cikin baccinsa wanda ya saka Meenah ringa zubar da hawayen itama tana shigar da hannunta a cikin tafin hannunsa ta hadesu.

Sai washe gari ya farka babu karfi ko kadan a jikinsa dan ko idanuwansa basa iya dagowa su kalli kowa,

A gurin gawar Nasir ya isa ya silale qasa a hankali yana dora kansa a gefensa ya fasa wani irin kuka mai tada hankalin duk wanda ya saurara take kowa ya janye daga dakin aka basa guri,

Kukane yakeyi wanda tinda yazo duniya bai taba ba,
Kukane dayake tayar tsikar jikin duk wanda yake kusa da gurin,
Kukane daya saka mahaifinsa dayake jiyosa sunkuyar da kai nasa idanuwan na sauyawa,
Kukane daya saka Dr Mum silalewa a qasa itama tana cusa kanta a cikin kafafunta tana yin mara sauti sbd bazata taba iya kallan fatima dake gida tana jiran dawowan danta a daura masa aurea gobe ba tace ya rasu ya tafi yabarsu har abada.

Tsit koina yayi sbd irin yanda babban mutum kamar RAHEEM JEERAH ke kuka wanda kowa ya san ma bai taba yiba kuma kila bazai taba sake yiba,

Kukane dasu kansu iyayensa sunsan ko daya daga cikinsu ke ya rasu Rear Admiral Raheem jeerah bazaiyi kuka ba.

******koda dare yayi ko gani sosai Raheem din bayayi kuma a daren ya buqaci bin daren Asuba ya isa Nigeria da gawar rabin jikinsa da zai kaiwa mahaifiyarsa da matarsa wainda suke can suna tsananin jiran dawowansa dan daura aurensa a gobe.

Dad bai hanas tafiya ba a yanayin dayake ciki dan yasan shine dole zai binne dan uwansa da hannuwansa,

Komai na shirin tafiya da gawar ya kammala a daren dan haka asubar fari jirginsu ya daga zuwa Nigeri batareda dad ba sbd bazai iya tafiya ba a lokacin dan duka kafafunsa a dunqule suke.

Karfe daya na rana girjinsu ya sauka a Nigeria motocin jeerahs ne da katuwar ambulance suka taho airport suka daukesu zuwa gidan bikin kai tsaye.

Koda suka isa akwai mutane sosai nata kaida kawo a waje da cikin gidan,

Ganin motocin jeerahs din a jere sun fara tsayawa kofar gidan ya saka aka fara murnar ango ya iso.

Babu wanda ma hankalinsa yakai akan ambulance dan haka cikin gida tini labarin isowan angon ya iso musu suka har sabon farin ciki da murna.

SANAAH dake dakin Maamah tana duba wayarta datake lafta masa kira sbd tasan daman dole yana hanyar dawowa dan haka so take yana sauka ya kunna wayarsa kiranta ya fara shigar masa dan haka tinda ta tashi take kiransa akai akai ba daga kafa tanajin tsananin son jin muryansa da har wani bugawa zuciyarta ke yi.

Baazo da Dr Mum ba sbd batada visar zuwa kuma ba lokacin nemawa dan haka Morocco aka koma da ita sbd acan zaafi saurin samar mata da isa Nigeria.

Mommy zainab ce ta fara cin karo da gawa daga fitowanta palonta take jiri ya dibeta tana kallan fuskan Raheem datake jajir yana riqe da gaban daukan gawar.

Dafeta akai ta baya sbd jirin daya debeta yana kokarin zubar da ita musamman rashin ganin Nasir da yanayin Raheem take tasan Gawar ba kowa bane face Nasir dan haka idanuwanta sukai luuu ta zube a gurin.

Ihun da aka sake bayan zubewanta ne ya saka Maamah dake palonta miqewa tana ajiye wayarta data kunna tin jiya a kashe tana taku biyu zata nufi kofa Raheem ya sako kai kansa qasa sbd kila har abada bazai iya sake hada ido da maamah ba ko iya kallan fuskanta ba sbd Nasir ya rasa ransa ne sbd shi..

Cak Maamah ta tsaya tana qin kallan gawar ta zubawa Raheem idanuwanta dake kokarin sauyawa zuciyarta na sauya bugawa ahankali ahankali.....

Ajiye gawar sukai tsakiyar palon Raheem ya durqusa qasa jikinsa ba kuzari ko kadan ya miqa hannuwansa dake rawa sosai ya kama kafafun Maamah wadda takejin kafafun nata na kasa daukanta hakama kirjinta yayi nauyi ya tsaya cak ta rintse idanuwanta ahankali ta bude hannuwanta na fara rawa ta bude baki da wata irin muryan data saka SANAAH tasowa ta fito daga bedroom cikin wani irin sanyi da slow,
Tace

'Nasirrrr ne??????

Kasa bata amsa yayi ya kankame kafafunta da karfi jikinsa na tsananta rawa sesai Ummah da suka taho da itane ta bude baki cikin sanyin jiki da jimami da tsananin tausayi ta sanar da ita Nasir ne ya rigasu gidan gaskia tareda jero mata bayanin abinda ya faru.

Shiru tayi hakama gurin tsit yayi sai kawai Maamah din ta daga hannunta daya ahankali ta dora akan kirjinta ta dafe tana kokarin riqe numfashinta dayake kokarin yankewa ta dafa kan Raheem da hannunta ke tsananin rawa tace

"Raheem kayi hakuri Allah yaji kansa yayi masa rahama ya kuma karbi baquncinsa,na yafe masa duniya da lahira.'

Bayan hakan data furta bata iya cewa komaiba ta dafa kujera ta zauna ahankali hannuwanta na wata irin rawan data saka jikin kowa tsananin mutuwa masu fasa kuka kuma suka fasa.

Babu wanda yasan daga inda SANAAH ta fito sai akan gawar aka ganta ta saka hannu ta bude kai tsaye tana ganin fuskansa ta tabbatarda Nasir dinta ne dan haka a gurin ta zube akan gawar gabaki daya babu numfashi a tattare da ita.

Kanta akai da sauri cikin gaggawa aka dauketa tareda yin waje da ita zuwa dakin mommynta ana cewa ayi gaggawar kawo ruwa.
Chapter 21 · 0% Book details