← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 154

Sashe 109

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakin mum din tayi tana fadawa jikin Dad din shima wanda ya rungumeta yana dago idanuwansa ya sauke akan SANAAH wadda ta sake wani murmushin tsananin karfin hali tanawa Mum din sannu da zuwa wadda itama ta dan rungumeta tana mata wani Kallan mamaki mai tsananin daya saka su fammah din kallanta ta bude baki tace

"SANAAH kin sauya sosai"

Murmushi fammah tayi tana dawowa gurin Mum din tace

"Tinda tazo koina bata zuwa fa tana gida kullum tana bacci"

"What?baki fita da ita bane taga qasar?
Aikuwa tinda na dawo koina zan kaita taga gari"

Dariya fammah tayi banda SANAAH da ta danyi murmushi tana bude baki tace

"Thank you"

Itace tayi serving kowannensu su ukun batareda ta bari ko inda yake ta iya kalla ba duk da a lokacinda ta isa gefensa tana serving nasa taji idanuwansa akan hannuwanta amma bata dago ba tana gama zubawa fammah da itace karshe juyawa tayi a natse zata bar gurin Mum tace

"Ina zaki kuma ke ba abincin zakici bane??

Juyowa tayi a natse ta dan sake fuskanta da kulawa tace

"No Mum azumi nakeyi yau Thursday"

Da mamaki fammah ta dago ta kalleta dan batasan yau ta tashi da azuminba dan ta dauka coffee din dazu sha zatai ashe ita ta hadawa,

dan dagowa shima da kamewansa yayi a tsanake ya kalleta amma bata sake cewa komaiba ta juya ta fice daga dakin mum kuwa cikin sakewanta tace

"Nima inason iya azumin Mondays da Thursdays dinnan amma na kasa gashinan ta huta ita tanayi"
#MAMUH
09033181070
[11/06, 9:29 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

106
Tana ficewa daga gurin kai tsaye dakinta ta koma ta zauna ahankali akan sofa tareda sauke ajiyan zuciya mai dumi da dan dafe kanta da tinda ya sara yake mata ciwo ta rufe idanuwanta ahankali tana jin wani masifaffen nauyi ya danne kirjinta taji kwata kwata a take gidan da qasar take son bari kawai Nigeria take son komawa kuma ita kadai batareda kowaba.

Su kuwa acan Dining din tinda tayi maganar datai din ya dan dago ya kalleta baice komaiba ko bayan barinta bai furta kalma ko daya ba duk da maganar da Ms Meenah ke masa shiru kawai yayi tinaninsa na tsayuwa akan kalmanta na azumin da kaf duniya shine yasan babu kowane axumin dayake bakinta sbd ko bayan asuba sunyi making love.

Yanayin fuskanta dataqi ko kallansa sam a lokacinda tai maganar ya dawo masa ya dan sauke wani boyayyen numfashin da babu wanda yaji ko yaga fitowansa yana maida kallansa akan abincin dake gabansa wanda tai serving nasa kuma daga kamshinsa kai tsaye da ganinsa ya sakasa tabbatarda itace ta girka masa duk da appetite dinsa ya dauke a take spoon ya saka yaci kadan dan ko bata kusa tinda shi tayiwa cinsa ya zama kaman dole a gunsa dan haka yanacin kadan ruwa kadai ya iya sha kadan suma ya zari tissue ya goge bakinsa tareda miqewa tsaye yafara kokarin barin Dining din wanda da mamaki Mum ta kallesa xatai magana ya katseta da rashin son hayaniya da cewa

"Zan fita office see you later"

Da mamaki Mum din ta kuma kallansa yana barin gurin sbd tasan yau kaman da gobe duka hutunsa ne.

Yana barin gurin ya fito palo har xai wuce ya dan juyo ya kalli hanyar dakinta datake rufe ya juya anatse ya wuce yana dan sake sauke numfashi mai dumi.

Dakinsa ya koma ya shirya cikin wasu kayan ya kira Imran akan wainda sike tsananin son ganinsa yau aka sanar dasu ba dama shirya zai gansu.

Koda ya fito Imran harya daka an juya kan motocinsu suna tsaye jikin motocin suna jiran fitowansa.

Yana sako kai Imran ya bude masa motar wadda yana isowa a cikin kamewa da nutsuwa shiga kawai yayi da wata isa take aka rufe suka ja motocin suka fice.

SANAAH dake dakinta zaune taji ficewan motocin data tabbatarda shine ya fita dan haka taji kirjinta ya dake nauyi ta sake jin ta tsani qasar gida takeso.

Su Mum kuwa suna gamawa sbd jin tana azumi sai basu nemeta ba dan kada a damar da ita suka zauna palo suna firarsu da firan bikin da aka qarasa babu su da sauran hidimar data riqe Mum din bata dawoba harsai yanxu.

Hankalinsu kwance da farin ciki suketa firarsu har lokacin sallah yayi.

Sallah tayi tin kafin Fammah ta shigo ta kwanta sbd jikinta daya fara mutuwa da wani irin yunwar datake jin kaman zata mace amma taurin zuciya da abinda takejin ya hanata ko iya fitowa.

Baccin wahalalliyar yunwa ne yadauke ta wanda ta dan jima tana yinsa kafin ta farka ta dauki ruwan robar dake dakin nata tasha kadan take taji kaman zatai amai ta miqe ta lallaba tayo alwala taxo tayi sallan laasar tana idarwa fammah ta shigo dakin taxo kusa da ita ta zauna tana kallanta da kulawa taga yanda tayi wani irin laushi tace

"Ai an kusa shan ruwa"

Lumshe idanuwanta tayi batateda ta iya barin Fammah din taga idanuwanta ba da tsananin damuwa da wata irin azabace take cikinsu.

Fira famman ta ringa mata cikeda kulawa da rage mata lokacin har kusan time din shan ruwan ta fice.

Kitchen taje ta hado mata fruits da yan abubuwan da zata fara shan ruwan dasu ta kawo mata ta juya ta fice ta koma kitchen din dan bata umarnin a hado mata a abincin a kai mata daki.

Fammah na ficewa fruits din ta kalla idanuwanta na cikowa da wasu hawayen da batasan ma sun tahoba.

Gangarowa sukai ta saka hannunta a natse ta dauki tissue ta goge tareda miqewa ta fada bathroom tayo alwala tana fitowa ta zauna taci abincin da aka aje mata zuciyarta ba dadi sam jikinta ma duka a mace tsakanin karya da gaskiya takai axumin da babu shi.

Da daddare zasuyi dinner bai dawo ba itama data sakawa ranta ta gama zama Dining a cikinsu tace ta koshi dan haka ko fitowa bataiba tana sallan ishai dinta ta kwanta.

Fammah ganin yanayin nata na yau da bata ganewa komaiba ya sakata xuwa dakinta suka kwana a tare wanda SANAAH na buqatan hakan dan damuwa ce take cikinta sosai dan haka xuwan famman tayi kokarin hanata shiga gabaki daya.

Da safe ko data tashi sam bata fito ba da dan zazzabi tace ta tashi dan haka ko Mum sedai tazo dakinta ta dubata tai mata sannu.

A dining harsukai breakfast suka gama bai ganta ba hakama a dishes din dake jere babu ko daya dayake da tabbacin ta saka hannu a aikinsa dan haka tea zalla kadai yasha kadan ya miqe yayi musu sai anjima ya fice.

Sai kusan rana ta fito a shiryenta ta nufi kitchen a ciki taci abincinta tana gamawa ta fito dauke da guava drink dinta da roban ruwa biyu ta koma dakinta tai zamanta acan.

Fammah datazo dakin suka wuni hadda Mum ma ta shigo ta dan zauna cikinsu suna fira da wayar Fammah ta kira Dr mum sukaita magana ta gaisa dasu mommy ma kafin ana maidawa Dr Mum wayar ta bude baki a natse tace

"Dr Mum inason dawowa gida"

Shiru Dr Mum tayi tareda dan shiga mamaki tace

"Lafiya dai ko?
Wani abin ya faru ne?

Dan girgiza kai tayi kaman tana ganinta tace

"Aa ina kewan gida ne kawai kuma na dade"

Sake shiga mamaki dr mum tayi kafin ta dan sauke numfashi sbd sun samu Dad yayi shiru baice komaiba haryanxu amma yanxu tana dawowa fitinarsa zata tashi dan kuwa tasan babu alkhairin dazai biyo bayan wannan shirun nasa indai Hakeem ne.

"Kiyi hkr idan kun tashi dawowa saiku dawo gabaki dayanku kinji"

Shiru tayi kirjinta na sake wani sabon nauyin dataji kaman hawaye zasu ciko idanuwanta dan nesanta kanta takeson yi dashi da matarsa.

Sallama sukai ta ajiye wayar tanajin Idanuwan Mum a kanta da mamakinta tace

"Meyasa kikeson komawa SANAAH bayan duka gamu ga fammanki a tareda ke?

Dan dagowa tayi ta kalli mum din da hana yanayinta ko daya bayyana da yar sakewa tace

"Mum wlh kewan gida nakeyi bantaba tafiya ba na dade haka"

Fammah da sam batama yadda da SANAAH din ta tafi ba jikinta ta kwanta tana cewa

"Tare zamu tafi gwara ma ki hakura kawai"

Murmushi mai sanyi kawai SANAAH din ta sake tana dan jan hancin famman.

Mum da itama sam batajin ta tashi tafiyar yanxu kokarin nunawa SANAAH tayi zamanta tayi tana son cusa mata shaawan qasar.

Zuwa yamma Mum tayi bai dan haka suna sitting room sunata shaaninsu su kuma suna daki suna tasu firar wadda fammah ce mai yi itadai tana zaune shiru tana sauraranta da binta da ido batareda tace komaiba.

Da daddare latti sukaci dinner dinsu wadda sam bata fitoba dan tini tayi tata tai shirin bacci tayi shigewanta dakin Fammah ta kwanta acan.

Yanzu kam ya tabbatarda janyewa tayi daga duk abinda ya shafesa dan kuwa ko yanzu ma babu komai daya nuna tashiga kitchen a cikin abincin da aka jere.

Ms Meenah da itama ta rasa gane yanda ya zama busy a kwana biyun maqalesa tayi a daki tanata zuba masa tambaya da son samunsa yanda ya kamata amma kusan hakan bai samu ba dan kansa dayake ciwon da idanuwansa ma sun nuna sosai dan ja sukai suna sauyawa gabaki daya.

Washe gari a dining din bayan kowa ya zauna yana isowa cikin nutswa har lokacin kansa bai dena masa ciwo mai tsanani ba zaunawa yayi a natse tareda dagowa a natse cikin rashin son ko doguwan magana sbd kamewa ya kalli Fammah ya bude baki yace

"Where is SANAAH?
Is she okay?
Data dena fitowa cin abincin tana ci acan daki??

Mum ce ta riga Fammah amsawa da cewa

"Nima har mamakin yanda ta dena zuwa table kwata kwata nake gashi tafara cewa gida takeson komawa ta gaji da nan,
Na rarrasheta fammah ma tayi amma kaman bata hakura bafa,
Ko kai Dad nasu zaka mata magana may be ta hakura pls"

Dago idanuwansa dasuka sake sauyawa yayi da wata yanayin daya saka Fammah jin tension din gurin a jikinta
Ita kanta Mum din idanuwansa ta kalla da jin wani iri amma bata sake cewa komaiba sbd ganin ya bude baki kai tsaye yace

"Tana ina ne??
Chapter 109 · 0% Book details