← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 154

Sashe 97

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dad,is that you??
Kasan yanda nayi missing naka?
Layinka are not going through and naso zuwa gidan Abbun but SANAAH bata iya zama ita haryanzu bata sakeba ko abincinmu sam bata iya ci sai Tea"

Shiru ne ya ratsa wayar wanda ya saka fammah kallan wayar zatai magana muryansa ta ratso wayar da cewa

"Is she okay??

"Yes Dad kawai dai rashin cin abincin ne,
Yaya kake Dad?
Mum is busy amma kullum saita kira"

"Lfy kalau alhamdllh,yaya kuke?

"Lfy kalau Dad kana gidan Abbu ne ko Dad zanzo na ganka gaskia???

"Yes" yace a taqaicen da muryan ta ratsi Kunnuwan SANAAH wadda take jin kowace sautinsa dake fitowa daga wayan tana shigarta ta kasa motsawa sbd tana motsawa tasan saiya sauka a kunnuwansa.

Shi kansa dayake zaune acan bangaren yasan tana kusada famman tana kuma jinsa dan haka dukansu sukai shiru sai da Fammah ta sake cewa "Hello Dad"

Sallama yayi mata kai tsaye yana cewa ta kula da kansu su dika,

Yana kashewa kai tsaye Ms Meenah ya kira itama wadda tana ganin kiransa taji wani sanyi da zazzafar kewansa ta rifeta ta dauki wayar tana zaunawa bakin gado daman ta gama shirin bacci tana dauka cewa tayi

"Hey my love,finally zan jika,
Yaya kake?
Ya gajiya?
Ya hanya?

A natse babu hayaniya ya amsa mata yana tambayarta ya take itama tareda yaya hidiman bikin.

Cikeda zumudi ta amsa tana marairaice muryanta da wata irin magiyar da kaman zata masa kuka tace

"Fleet dan Allah ko so dayan nan ne ka cika wannan Al'adar tamu tin ta kakanni sbd bayan Zad banda wani makusancin da zaka mun hakan ka taho cikin villah dinnan idan yaso ranar da aka kammala ka tafi,please please My love"

Idanuwansa da sauya mintina kalilan da suka wuce na wayar da yayi dasu fammah ya dago a hankali da wani irin slow yana yin shiru kafin daga sama kaman saukan aradun da bata taba tsammaniba a rayuwarta taji yace mata gobe insha Allah yana tafen.

Wani miqewa tayi cikeda mahaukacin mamakin da batadan lokacinda ta zari abayarta ba ta zuba tana ficewa daga dakinta tana kasa yadda da abinda taji sai data fice tace

"I love you my love"

Kashe wayar tayi kafin ma taji komai daga garesa da zai saka ya sauya raayin zuwan.

Kai tsaye bangaren musamman da aka ware na manyan sirikan babban familyn masu power ta isa daman akwai bangaren da bata taba barin anshiga ba sbd shine wanda take masa tanadi tsawon shekaru na fatan yaxo bikin Zad dan haka tana bude bangaren komai na cikinsa sabo dal hakama tsari ne da akai na musamman dayake shirye da komai babu wanda ya taba sauka duk bayan kwana biyu ake budewa a gyara a rufe.

Masu aiki ta kira ta saka a cikin daren suka sake gyarawa tukuna ta koma dakinta ta kwanta tana jin kaman zata taka kan jariri.

Koda gari ya waye da farin ciki sosai ta tashi ta damqawa masu aikin komai na kulawa da bangaren Fleet din ta fice zuwa wata hadimar tana jin kanta a sama sbd a karan farko da Fleet zai nunawa ahalinta na qasar Morocco kaf matsayinta dan kuwa duk manyan da suke cikin villah din fleet shine mai asalin power din.

Fammah ma tinda ta tashi yau busy take sbd yau ne ake asalin babban event din bikin wanda zaa zubar da asalin dukiya da nuna zinari ba komai bane.

SANAAH bata damar da fammah ba yau tabarta taji da hidiman gabanta a natse dan haka tana daki tana hutawanta da dan dube dube a ipad dinta da itace take cire mata kadaici.

Da yamma masu kwalliyansu suka iso aka fara yiwa Mum wani irin shirin daya sakata sauyawa gabaki daya xuwa asalin balarabiyanta mai kyau da wasu irin sarkokin zinari masu kyau da wayewa sosai ta fito harabar gidan tana waya zata shiga mota daidai nan motocin Fleet jeerah suka sako kai a harabar tana ganinsu take tasan shine dan haka ta fasa shiga motar tana jin wani farin cikin gaske dan haka da ta nufesa tin kafin ta isa aka bude masa motar ya sako kafarsa dake sanye da Santoni leather Oxford shoes brown ya fito gabaki daya cikin kamewa da kwarjini da nutsuwa.

Rungumesa kawai tayi a natse tana kai bakinta zatai kissin gefen fuskansa ta tina da makeup dinta da bata buqatan tai komai sbd itace takeson ta zama star.

Da farin ciki ta masa sannu da zuwa Zad da wasu manyan familyn da manyan mutanen dake aure a familyn suka iso gurinsa cikeda girmamawa da mamakin da kowa ya kasa nunawa suka tarbesa take aka kira aka qari securities a villa din sbd zuwansa wanda take kowa yafara jin wannan karan yabar tarihi sbd FLEET ADMIRAL JEERAH zai cike al'ada.

Bangarensa suna nufa wanda akaiwa gyaran musamman kana bude kofar palon wani sanyi da kamshi mai dadi ne zai bugeka.

Hanyar wucewa bangaren gabaki daya imran ya zuba securities dinsu wainda aka warewa gefe daya dayake kusa da nasa su da imran wanda dakinsa yake cikin inda suke shima.

Duk yanda takejin kewa da tsananin buqatansa bata iya tsayawa ta cusawa kanta hakan ba sbd gaskia tana buqatan tafiya sai dai idan ta dawo duk da kusan bikin na dare ne dan sai tsakiyar dare ko zaa gama sa dan yanzu haka anyi magrib amma ango baima isa ba yana gidan tinda dashi aka tarbi Raheem din.

Sallama tai masa ta fice yabita da kallo a natse sbd yasan koda yace ta tsaya kada ta tafi ba tsayawan zatai ba dan haka baima bude baki ya hanata tafiyanba duk da yanajin yanayin na buqata da iyali.

Tana barin bangeren tsaro ya qaru sbd Imran ya bada umarnin kada wanda ya wuce hanyar.

Fammah batasan Dad dinta yana Villah dinba sunata shiri angama musu makeup wadda sama sama akaiwa SANAAH batason mai yawa sun shirya cikin wata doguwan gown ta bikin larabawa ita dark maroon ne a jikinta sai fammah kuma fara da golden.

Karfe takwas da kusan arbain aka fara bikin wanda kusan kowa ya watse tsit ana gurin bikin.

Driver ne yaxo daukansu fammah da sukai na karshe tareda wasu yayan yan uwan Maman Mum su uku da sukazo bikin.

Basason takura ko kadan dan haka Mum fammah ta kira akan a aiko musu wani driver din.

Kai tsaye Mum din tace

"Dad dinki na nan villah din ku karbo motarsa daya kokuma ku taho kawai ku baro SANAAH ga Maleek nan zan aiko mata saiya daukota ita kadai inason su gaisa kafin su iso a hanya"

Fammah da bataji komai akan hakan ba tace shikenan.

Motar suka shige SANAAH da daman jin take kaman bazata iya zuwaba ta amince su tafin kawai niyarta ta komawanta ciki tinda Ammah na nan ta tayata fira kafin a dawo bikin dan kwalliyar ma damunta takeyi a fuska.

Suna wucewa ta wuce ciki ta nufi dakin Ammah.

Fammah kuwa suna isa gurin ta kasa karbi wayar Mum dinta sbd tabarowa SANAAH tata ta saka kiran Dad dinta wanda ya sauka yana fitowa wanka kenan ta sanar masa sun baro SANAAH ya saka driver ya kawota.

Shiru yayi kafin ya bude baki yace

"Meyasa baku tafi tare ba??

"Mum tace a barta zata turo uncle Maleek yaxo ya dauketa ita kadai ya kaita zasu gaisa"
#MAMUH
09033181070
[07/06, 6:02 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

93
Shiru ne ya ratsa wayar wadda ya dago idanuwansa da wani slow da nutsuwa ya bude baki yace

"And who is dat???

Da mamaki fammah tace

"Uncle Maleek Nuh"

Baice komaiba ya katse wayarsa yana ajiyewa ya tsaya a gaban mirror din dayaje dakin mai girma batareda ya shafa komai ba ko nufar kayan da zai saka dan shiryawa.

Tsayuwan mintina biyar yayi batareda yayi komaiba idanuwansa sun sauya yanayinsu gabaki daya wani irin zufa ne daya tsatsafo masa a jikinsa kadan kadan yana gangarowa daga lafiyayyar fatarsa,

Wayarsa miqa hannu ya dauka ba kowace hayaniya sbd ko maganan bayason yi ya saka kiran Imran.

Kalma biyu kawai ya furtawa Imran din ya kashe wayar ya juya ya koma bathroom sbd wani zafi ne yake fesowa daga jininsa yana bawa gangar jikinsa jin yake bayajin sanyi ko kadan wata zazzafan zafi ne yake bin jikinsa dayake fidda wata irin zufar daya sake sakarwa kansa ruwan shower masu dan sanyi.

Imran kuwa kai tsaye yana kashe wayar fitowa yayi sanye da wasu kayan shima dan haryayi shirin hutawa,
Kai tsaye ciki ya nufa dan yasan hanya da kuma ciki sbd matiqar suna qasar to Fleet na zuwa gaida Ammah kakar Ms Meenah din.

Babban palon farkon ya iso ya tsaya a kofar yayi knocking.

Dayake koina yayi tsit babu kowa sai kai tsaye masu aikin dake kitchen suka jiyo bugun dayansu ta iso ta bude kofar tana ganinsa ta bayyanarda girmamawanta sbd tasan babban yaron Fleet ne tinda suna zuwa kuma itama ta jima shekaru a familyn tana aiki.

Gaidasa tayi ya amsa kai tsaye da sanar da ita taje ta sanar da Ms SANAAH ana kiranta.

Juyawa tayi ta nufi hanyar dakinsu taje bata ganta a dakin ba ta dawo ta nufi dakin Ammah tana zuwa kuwa ta taddata zaune a dakin dan haka ta sanar mata kai tsaye ta juya ta koma ta sanar masa ta koma kitchen.

SANAAH da sam bataso mai daukan nata yazo ba numfashi ta sauke tana jin jikinta na sake mutuwa da kewan gida da jin bata cikin kowace walwala.

Tashi tayi taiwa Ammah sai ta dawo ta fice daga dakin makeup dinta kai sanyi da kyau kaman lokacin akai mata abarta.

Tana fitowa bataga kowaba dan haka ta fito daga palon zuwa harabar gidan dan duba motar data zo din...

Kafin ta isa Imran dayake jiranta ya bayyana a gefenta yana gaidata da turanci.

Dan juyowa tayi ta kallesa kadan tana mamakin ganinsa sosai wanda har sai da hakan ya bayyana ta gaidasa itama tana jin kaman sanyi ya ratseta sbd daga karshe dai taga wani dayake na gida dan sam ta kasa sakewa da samun nutsuwa a cikin ahalin gidan.
Chapter 97 · 0% Book details