← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 154

Sashe 118

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maamah kuwa da Dr Mum ta bata tabbacin cikin Sallah tayi ta nafila ta ringa yiwa Allah godia ranta fes dan haka suka shiga wata walwala da farin ciki abinsu wanda Mum ma data shigo taga alaman ana cikin farin ciki sai itama tahau farin ciki a sake tana jin nata farin cikin itama na tafiyan datake kokarin tabbatuwa tata zuwa ga mijinta.

Fammah data fara shiga rudu akan abinda yake faruwa kasa riqe kanta tayi zuciyarta nata shiga tinanin abinda yake faruwan data kasa ganewa dan haka ta zauna a tareda SANAAH wadda bata samu dan sauki ba sai yamma sosai tayi wanka Maamah ta kawo mata abinci da kanta ta sakata taci kadan ta bata magani wanda fammah bata gani da kyauba amma ta tabbatarda kaman su folic Acid ta gani dan haka kirjinta yayi wani mummunan faduwan data kasa dauke idanuwanta daga kan Maamah din harta fice da maganin a hannunta bata bari ta ajiyeba.

Kasa juyowa Fammah din tayi sbd tsananin nauyin da kowace gaban jikinta tai mata ta bude baki tace

"SANAAH meyake faruwa?
Menene ciwon dayake damunki??
#MAMUH
09033181070
[15/06, 12:37 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

116
*_NOOR COLLECTION_*
09035841194
07044204680
Yar uwa kina neman inda zaki siya best,classy and luxury
ABAYA'S
JALLABIYAs
SNEAKER'S
KAYAN YARA
NEW BORN BABIES ITEMS
MAYAFAI (veils)
da idan kika saka sai kallake an tabbatarda kin saka luxury kuma kayan alfarma unique da basu zama ruwan dare a koina ba,
To ki tabbatadda a gurin NOOR COLLECTION luxury shop kika siyawa kanki da maigidanki da yaranki komai 100% tested and trusted.
Ana iya turo orders din wasu abubuwan idan anaso NOOR COLLECTION zasu nemo su kawo muku babu banbanci a saukin kudi ma kudai kawai ku riqe NOOR COLLECTION bazakuyi dana saniba.
EGYPTIAN ADDRESS: NEW CAIRO.
NIGERIAN ADDRESS: Zaria

**********
Shiru SANAAH tayi tareda kasa cewa komai duk da zuciyarta na tsananin son sanar da fammah laifin datai mata amma bakinta ya kasa furtawa dan haka ta sauke numfashi mai sanyi tareda kallan fammah din wadda ta juyo ta kalleta da dukkanin idanuwanta tace

"Ba komai"

Shiru sukai su dukan wanda ya sake saka zuciyar fammah cikin wani irin nauyi da jin rashin sukuni da nutsuwa taji tana kasa hana kanta fara dawo da maganar hajiyan samad cikin kanta dan haka ana yin sallan magrib ta SANAAH ta kasa sakewa a gaban fammah din karshe kasa dauka kirjinta yayi ta yanke shawaran zuwa Dad duk da bata jin dadi sosai har wani jiri take ji mai dan tsanani amma dole tana son zamewa idanuwa da kallan fammah.

Sallan ishai sukai suna gamawa ta ta dora doguwan riga mai fadi dosai akan kayan jikinta da mayafi ta silale ta fice zuwa gurin Dad.

Fammah data kasa riqe kanta kwata kwata daga abinda zuciyarta take turata ga bangarensu ta miqe ta nufa kirjinta na wata irin bugawa da sauri tana son hana gangar jikinta da zuciyarta binciken amma ta kasa.

Dakinsu ta nufa tana shiga bangaren tana isa kai tsaye closet ta wuce ta nufi wardrobe din da kayan SANAAH suke a jere ta kalli kayan hannunta na dan rawa takai ga kayan tafara dubawa bugun zuciyarta na tsananin karuwa tana daga kayan gabaki daya saiga jakar datake nema ta tsaya cak tana kallan jakar idanuwanta na dan nauyi kaman yanda kirjinta yake nauyin.

Hannu ta miqa ta dauko jakar tareda budewa kai tsaye idanuwanta suka sauka akan takardun da suke dauke da sunan asibitin jeerahs din ta sauke ajiyan zuciya mai karfi data fito da bugawan zuciyarta.

*****kafin wannan daren kuwa gap da Magrib jirgin Samad Jeerah ya sauka batareda sanin hajiyarsa data wuni a tsaye cikin tashin hankali da tsoro da fargaban isowansa datake zargi,

Babu wanda yasan da zuwansa dan haka ba wanda yaje daukansa airport mota kawai ya hawo ya iso JEERAHsV idanuwansa jajir kaman wanda ya iso a caje sbd yanda idanuwansa sukai dole ma glasses ya saka ya rufesu duk da yamma tayi.

Securities na ganinsa da girmamawa sukai masa barka da sauka suna boye mamakinsu na ganinsa da motar kasuwa.

Yana shigowa mai tsaye uwarsa batasan da zuwansa ba bangarensa ya nufa wanda yake fes sbd duk bayan kwana biyu shima uwarsa ke sakawa ana zuwa gyara bangaren sbd hana qura da yana zama dan haka babu inda yakeda kura koina fes.

Haske kadai ya kunna ya jefar da kayansa ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa hakanan yakejin kaman jininsa na konewa kwakwalwansa na rasa lafiyarta sbd a iya saninsa tsawon shekarun SANAAH na nan a matar da har abada yadan Fleet bazai taba kallanta a maceba sbd babu qarin wata macen a rayuwarsa data iyalinsa ta ina tayaya hajiyarsa zatace ciki a jikin SANAAH?
Wane namijin ne ya isa ya tabata kokuwa wane namijin ta yadda dashi bayan shi bata yadda dashi ba,

Yabarta ne kaman ajiya ga auren dayake kanta har zuwa lokacinda Dad zai gaji da jira ya raba auren amma yanzu kam bazai iya jiran ba.

Hajiyar na zaune a palo da daddaren bayan ta gama sake danna kiransa bata samu taji an bude kofar palon kai tsaye an shigo ta dan juya dan ganin waye sai kawai ganinsa tayi da sauri ta miqe tsaye tana jefar da wayarta ta isa gurinsa tana cewa

"Wai dawowan kayi kenan Samad?
Innalillahi,
Me kake tunani?
Menene a cikin kanka?
Wace masifar zaka kuma jawomin bayan wadda na shiga ta mutuwan aure da girmana?
To bari kaji na fada maka Samad wlh tallahi babu ruwanka da SANAAH ko da cikin aure ne a jikinta kona shege koma ne menene babu ruwanka da ita"

Wani kallo ya mata da idanuwansa da suka sauya cikin baqin ciki mai tsananin gaske yace

"Idan kina ambatar cikin nan da bakida tabbas akansa kaman zan zare nakeji dan haka ki dena fada.....

Katsesa tayi da karfin gaske da cewa

"Wallahi cikine a jikinta kuma ko zaka mutu bazan bari ka tinkareta ba dan bazaka saka kanka a masifar da zata shudar da labarina a jeerahs ba batareda naga karshensu ba bayan haka so kake ubanka ya kasheka?
Ba shi ba ko Raheem a yanzu kasan zai iya daukan mataki akanka sbd matsayin SANAAH a gurin yarsa dan haka tin kafin ma mu raba hali maza maza a cikin daren nan inason kabar gidan nan ka koma inda ka fito..

Baqin cikin daya gama rufesa hanasa kuma magana yayi ya juya a tsananin fusace zai fice ta riqe hannunsa tace

"Tafiyar zakai ko yaya??

Juyowa yayi gabaki daya ya kalleta idanuwanta na qarasa bayyanarda zallan fushi da baqin ciki yace

"Zan fuskanci Dad din da kaina bayan na tabbatarda abinda kike fada dan kuwa wlh tallahi saina dauki ran ko wanene yayi mata cikin kafin itama ta fuskanci asalin waye ne"

Turesa hajiyar tayi da karfi tana sake cakumo sa tace

"ashe bakada hankali ko?
Ashe hauka ka fara bansaniba?

Fixgewa yayi da karfi yana juyawa yace

"Kece kika fara cinnamun haukar sbd kece kika zabi sanar dani abinda kika gani"

Kofa ya tinkara ta bisa da mummunan tashin hankali ta riqosa tana tsayawa gabansa tashin hankalinta na bayyana gabaki daya ta bayyanarda tsananin tsoronta tace

"Kayi Hakuri kada ka tafi ta koma dakinka gobe zamuyi magana da safe"

Bai kalletaba ya kwace yana futa kofar palon ta biyosa a tsananin rikice tana rokonsa amma sam kaman bada shi take ba dan haka a zafafe tasha gabansa tareda daga hannu ta sauke masa lafiyayyan marin daya sakasa tsayawa cak yana dago idanuwansa da sukai mummunan ja sbd bacin rai da wani sabon radadin baqin ciki ya kalleta zaiyi magana kenan idanuwansa sukai wata sauka akan SANAAH data fito bangaren Dad wanda yake conference meeting a laptop bata samu ganinsa ba.

Bata lura dasu ba sai data kawo daf dasu a harabar gidan dan haka ta tsaya cak gabanta na wata irin mummunan faduwan data sakat kanta muguwar sarawa mararta tai wani nauyi a take.

Hajiyar Samad dinma cikin mummunan tashin hankali ta juyo ta kalli SANAAH din itama take taji hankalinta ya kara tashi ta saka hannunta da sauri ta riqe hannunsa daya tana hanasa motsawa daga inda yake zuciyarsa na wata irin harbawa da azababben zafin ganin SANAAH din a gaban idanuwansa da wata irin sauyin dayake tabbatar masa da maganar hajiyan.
#MAMUH
09033181070
[15/06, 12:38 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

117
Fammah da hannuwanta suka bude takardar asibitin data ciro jakar SANAAH wani irin sarawan da kanta bai taba yiba yayi wani jiri ya dibeta tayi baya da karfi tana zubewa qasa idanuwanta na dishi dishi ta sake karantawa tana jiqewa da zufan da tin daga cikin kanta yake fitowa.

Ciki?
Cikin haihuwa?
Wata biyu da satika?
A jikin SANAAH??

Girgiza kai tayi da sauri tana sake duba gurin sunan dayake rubuce da tsananin sauri hannuwanta na tsananta rawa taga sunan SANAAH dinnne baro baro a jiki.
Dena aiki kowane tinani da kwakwalwanta sukai ta miqe a tsananin tsoroce da kasa yadda dashi dan koma menene bata yadda da result din SANAAH bane zarginta take akan Safiya yakoma sbd ita SANAAH takai asibitin tayi amfani da sunanta dan saka a duba safiya din.

Fitowa tayi kai tsaye tana nufar kofar fita wadda tayi daidai da isowan Mum dinta bata tsaya ko kallan Mum dinba ta wuce hankalinta na da zuciyarta na neman amsa daya daga SANAAH ina cikin ya fito wakeda cikin??
Dan ko saurayin datake fira dukansu basa dashi bare wata maganar ciki ta fito.

Mum bin bayan fammah din da idanuwanta tayi kafin ta juya zata shige sai kuma ta fasa ta biyo bayanta sbd ganin yanda take tafiya kaman wadda bata hayyacinta.

Samad kuwa daidai wannan lokacin ne suka hade da SANAAH wadda ta motsa zata kebesu da sauri ta wuce ya fixge hannunsa daga na Hajiyarsa zai riqo SANAAH din hajiyar ta kuma riqesa da sauri wannan karan jikinta har rawa yakeyi ta juya ta kalli koina taga ba kowa ta bude baki jikinta na wata irin rawa tace

"Ashe bakada hankali muguwar hauka na cinka ko??
Me kake kokarin yi?
Ka tabata ace cikin jikinta naka ko???
Chapter 118 · 0% Book details