← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 154

Sashe 115

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Dr Mum,Ni kune naketa kewa Allah"

Mommy dake jinsu batace komaiba sai dariya da murmushi takeyi sunata fira sama sama saiga safiya dauke da qaton tray din data jerowa SANAAH din abinci akai na breakfast sbd su maamah sun riga sunci nasu.

Safiya da farin ciki take komai yau din dan jin take kaman zata taka kan jariri tsabar farin cikin dawowansu.

Ajiyewa tayi tana dan kallan SANAAH din tace

"Tarairayanki zanyi kwana biyu sbd irin kewan da na miki"

Dariya mai kyau SANAAH tayi tana kallan abincin da dan gyara zamanta kai tsaye takai hannu tana daukan soyayyar doyan da aka soya da kwar da sauce din hanta takai bakinta ko fork bata daukaba kawai fara ci tayi tanajin tsananin kewan abincin kafin ta dauki milk tea mai kauri da aka hado dashi tafara sha tana cin doyar.

Fira sukeyi hankalinsu kwance da farin cikin ganin sauyawan SANAAH alaman bata sha wuyan komaiba a tafiyar.

Mommy kuwa kallan abincin da SANAAH ke kokarin cinyewa tayi cikeda dan mamaki kafin takalli SANAAH din wadda ta cinye doyan tas da tea din harma da qaton apple hankalinta kwance Mommyn ta zuba mata ido sbd sanin sam SANAAH batada wani cin abinci.

Safiya ma datazo kwashe kayan kallansu tayi da mamaki da kasa yin shiru tace

"Kai kai kin cinye duka,kinyi kewan abincina kenan" qarasawa tayi da dariya da jin dadi tana juyawa.

SANAAH kuwa miqewa tayi tabar gurin sbd jin jikinta ya mutu gabaki daya bacci taji tanaji ta koma dakin Mommy ta kwanta take kuwa ta sake komawa bacci.

Su fammah ne da mum dinta suka shigo bangaren suma bayan sun huta dakyau sun samu isashen baccinsu sunyi breakfast dinsu acan.

Da walwala suka shigo aka sake musu barka da dawowa cikin kulawa tukuna mum ta zauna fammah kuma daki ta samu SANAAH ta tada ita nan safiya ta samu gama abinda takeyi ta shigo dakin da murnanta ta zauna cikinsu tana bajewa da labari da fira kala kala.

Sai da sukai azahar tukuna SANAAH ta shirya ta fito da tsarabar wani tsadadden turare da agogo data siyowa Dad ta nufi bangarensa tareda fammah.

Yana ganinsu wani farin ciki da jin dadi ne sosai ya shigesa ya kalli SANAAH wadda babu alaman damuwa a tattare da ita ko kadan dan haka yaji dan sassaucin irin mugun zafin daya dauka yana sake jin anyi iya wanda zaayi angama tinda har fleet din ya qara gaba gurin harkokinsa batareda yaxo ya fuskancesa ba bayan yasan yana nan yana jiransa sbd ba qaramin daukan zafi yayiba.

Fira suka zauna sukai sosai wadda ta saka SANAAH jin ta sake samun nutsuwan dawowanta cikin gatanta,

Tsarabarsa ta basa ya amsa yana yabawa sosai da sake jinjinawa kewansu da yayi su biyun.

Bayan duka gama firarsu da walwalansu numfashi ya sauke me sanyi dake cikeda nutsuwa da kulawa ya kalli fammah ya bude baki yace

"Fammah akwai abinda a rayuwa yake zuwar ma mutum batareda tsammani ba kuma a gurin ubangiji ba komai bane yana cikin auna imaninka da bude maka wata hanyar dabbaka ayyukanka na lada da nuna karfin imaninka,

Akwai wanda ubangiji yake amfani dashi dan gwada imaninka da karfin tawakkalinka,
SANAAH taki ce da ki sani har abada bazata taba yin abinda zai zama cuta a gareki ba hakama komai zaki fuskanta akanta inason ki kasance mai aiki da iliminki na addini da bani girmana gurin shawara dani kinji Doc???

Dan shiru fammah tayi na mamkin kalamansa da babu kalma ko daya data gane saita karshen dan haka kai kawai ta gyada masa ya maida kallansa kan SANAAH wadda jikinta yayi tsananin sanyi tayi wani iri damuwarta na bayyana sbd a yanxu a halinda suka samu kansu da auren da yake gap da bayyanuwa fammah ce damuwanta,fammah ce kunyarta,fammah ce abinda zuciyarta da idanuwanta da rayuwarta suka tsantsar jin nauyi.

Sallamarsu yayi yace su tafi.

Suna fitowa fammah ta kalleta tareda bude baki tace

"Ke kin fahimci abinda grandfather yake nufi??

Wani nauyi kirjin SANAAH ya dauka ta sauke wani numfashi mai zafi tana dan dakatawa daga tafiyar da sukeyi zuciyarta na yanke shawarar sanar da ita da kanta dan karban kowace hukuncinta da zata samu sassauci idan taji daga bakinta....

Kasa budewa bakinta yayi yai mata wani mugun nauyi idanuwanta sukai jajir sai kawai ta juya ta kama hanya tana kasa cewa komai ta kama hannun fammah din wadda ta fahimci da maganar da SANAAH taso fada amma ta fasa.

Hakanan jikinta yayi sanyi itama ta kasa tambayar SANAAH din komai har suka isa bangarensu Mommy suka shige.

Daki suka shige acan sukai firarsu da safiya data gama aikinta sharp sharp tazo gurinsu suka ringa fira SANAAH na lafe gefen fammah din har lokacin damuwarta bata warware ba sbd da alama Dad akwai matakin dayake kokarin dauka sbd maganar da yayi musu din.

Har dare suna bangaren sai kusan 9 suka tafi banda SANAAH din wadda yauma bata bisu ba dan batajin ma zata sake zuwa bangarenba kwana dan nauyin dataji yana shigarta a yanxu na daban.

Sa daddare zazzabin data saba dashi ya dawo ga damuwa haka kawai dataji ta rifeta dan haka da zazzabin mai karfi ta kwana koda gari ya waye ko fitowa kasawa tayi a daki ta wuni kowa na mamakin ciwon tinda lafiya kalau ta kwanta.

Mommy data fara shiga tinane tinane tashi hankalinta ya fara yi dan haka ta sakawa SANAAH din ido sosai wadda gadan gadan zazzabi kuwa ya zama nata.

Yau da daddare bayan kowa ya shige ta fito ta tafi kitchen indomie takeso dan haka tana shiga safiya na nan bata riga ta wuce daki ba kallanta tayi tana cewa

"Yawwa safiya dafamun indomi me yaji safiya dan Allah"

Safiya kuwa cikin jin dadi ta fara dafa mata tana mata fira ita kuma ta zauna tana saurarenta da dan kokarin biye mata.

Dafa mata tayi ta zuba a plate ta ajiye tana soya mata farin kwai kafin ta gama SANAAH ta dauko indomien tafara ci cikin jin dadin yajin tana sake jin dadin firar sbd yanda dahuwar tai mata dadi.

A wani plate ta juyo mata kwan wanda tana ajiyewa gaban SANAAH din kamshinsa ya shigeta take wani amai me karfi ya taho mata ta tashi ta isa fanfo tafara zubasa mai karfin gaske daya saka Mommy data fito daga dakinta jinsa tayo kitchen din tana kallan Safiya data tsaya kan SANAAH din cikin damuwa da kulawa tana dan shafa bayanta ta maida kallanta akan SANAAH din wadda ta dago a matiqar kasalance tana wanke bakinta da fuskanta.

Sarawa kan Mommy yayi ta zubawa yatsun hannuwan SANAAH din dake wani daukan ido sbd tsananin hasken da suka qara da shaawa ido bakinta baisan lokacinda tace

"SANAAH ciki ne dake ko me??"
##MAMUH
09033181070
[13/06, 2:07 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

113
Wani mugun rikitaccen aman ne ya kuma kufcewa SANAAH din sbd mahaukacin tashin hankalin maganar mommyn da hatta safiya sai dataji kaman fitsari zai kufce mata ta matse kafafu da sauri tana kallan SANAAH din.

Amai SANAAH ta ringa kwararowa dukkanin jikinta na wata irin kyarma da asalin tashin hankalin da bata taba shiga ba a rayuwarta dan har saida takai bata iya yunkurawa safiya da hannuwanta ke rawa sosai sbd tashin hankali itace ta taimaka mata ta wanke fuskanta suka juyo a tare mommy data kasa motsawa daga inda take tsayen itama kallansu tayi hankalinta na qarasa tashi da abubuwa daban daban a cikin kanta wainda suke babu mae sauki dan kuwa bayan babban tashin hankalin da Ms Meenah zata nuna musu na rayuwa Dad kansa ya riga ya yanke hukuncin raba auren wannan karan da gasken gaske yakeyi ga kuma fammah ga kuma duniya bayyanar cikin kawai zatashi batareda tinawa ma aurenba bare asan cikin na waye kuma dai koba komai ciki kafin a karba aure da tarewa? Ina zasu saka kansu da duka wannan tashin hankalin wanda basu taba tsammanin zuwansa babban fatan yanzu dai Allah yasa babu abinda ya hada SANAAH da ciki a yanxu.

SANAAH da kanta ke juyawa sosai tsabar shock da tashin hankali kasa daukanta kafafunta sukai ta zame zata zube qasa safiya ta riqota tana kallan Mommyn a tsorace da fargaba tace

"Mommy bafa ta da komai"

Wani kallo mommyn tayi mata tana maida kallanta akan SANAAH din tace

"Allah yasa hakan ne sbd babu wanda ya shiryawa hakan"

Sake shiga mummunan tashin hankali SANAAH tayi tana rasa tinaninta ko daya dazai bata ikon tinanin ma a wane babin take dan haka da qyar su mommyn suka kaita daki tana kwantawa wani mugun zazzabi mai karfin gaske ya rufeta wanda dole ya saka Safiya kwana dakin tareda su sbd amai ta ringa yi cikin daren kafin safe tayi wani mugun laushi ta firgice gabaki daya.

Maamah ta aiko safiya ta kawo mata wayarta da Raheem din ya kira yana nemanta bata iya wata magana ba tana jin muryansa kuka ta fasa masa ahankali sosai kawai.

Shiru yayi tsigar jikinsa na tashi gabaki daya daga inda yake dan haka ya miqe tsaye daga zaunen dayake a hankali tareda isa bakin windown dakinsa dayake Miami iska ta ringa ratsosa tana rage wani zafi da zufan dayaji yana tsatsafo masa a take.

Cikin wata sauti mai nutsuwa data ratsata ya kira sunanta sukai shiru su duka biyun tsawon seconds kafin ya sake ambatar sunanya yana cewa

"Are you okay?
Lafiya dai?
Akwai matsala ne?
Me yake faruwa?
Bakida lafiya ne?

Shiru tayi tana kasa cew komai hawayenta na tsananta gudu jin hakan ya sakasa bude baki baki yace

"Ina famma?

Sai a lokacin ta iya bude baki da rashin karfi tace

"Tana can bangaren"

"Ok bara na kirata naji abinda yake faruwa"

Katsesa tayi ahankali da cewa

"Bata saniba fa,kuma babu komai banda lafiya ne kawai"

"Kawai???? Yayi maimaicin kalman tata ta karshe yana fidda wani numfashin dataji sa har cikin wayar ya riqe kansa dan ba qaramin tabasa kukanta yayi ba yace

"Ok shikenan ki huta Dr zatazo gidan ta dubaki"

Bai jira gardaman da zatai masa ba ya kashe wayar yana jefarwa akan sofa da saka hannuwansa duka biyu aljihun wandonsa yana sake tsayuwa a gaban iskan datake ratsosa sbd basa daidaici.
Chapter 115 · 0% Book details