← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 154

Sashe 116

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Imran ne ya shigo batareda ya juyoba ya katsesa a natse daga abinda ya shigo fada masa yace

"A nemi Dr bushrat taje yanzu ta duba abinda yake damun Baby SANAAH"

Gyada kai Imran yayi yana cewa ok ya juya ya fice yana daga wayarsa dan neman Numbern Dr Bushrat din dayasan yayi saving a waya tin last time.

SANAAH kuwa jin abinda ya fada ya saka hankalinta sake tashi gashi ta kasa iya barin Dr Mum ta dubata ta tsaya akan mura ce ke damunta sosai hakan sbd batason a dubata kaman yanda Mommy ma take shakkar a dubata din.

Kokarin nuna ta warke tafara yi duk da jikin yana qin yadda da hakan sam gashi ta kauracewa Mum da fammah sosai da dr mum zaman daki takeyi sbd tsoron abinda zasu iya gani a tattare da ita kasancewansu duka likitoci.

Fammah tsananin mamaki da tausayin SANAAH din takeji ganin yanda take fama fashi sam taqi yadda kowa ya dubata hakama taqi zuwa asibitin da Fammah ta matsa sai sun tafi din.

Mommy da safiya da ita ne a cikin wata irin fargaba wadda duk suka rasa sukuninsu Mum kuwa kwata kwata hankalinta ya karkata akan mijinta da yanzu take jin kaman suna nisa dan haka ta sauya shawaran tattarawa tabar fammah ta samesa a Miami dan kuwa hadda tsananin kewansa tana ji da buqatansa dan haka hankalinta baya kan SANAAH da ciwonta sam tanata kokarin nemawa kanta tafiya zuwa Miami batareda sanin kowaba.

SANAAH duk inda tashin hankali yake tana ciki wanda ahankali su Maamah suka fara ganewa musamman mutane da batason shiga sam da a tsarge take gidan tako ina sbd manyan dake zagaye da ita.

Yau tinda yace zai aiko a dubata ya sakata shiga muguwan damuwa da fargaba dan haka daga karshe kasa jiran zuwan Dr bushrat tayi zata sameta asibiti ta dubata acan inda babu kowa dan haka tin kafin fammah ta shigo bangaren batareda sanin kowaba tabar gidan itada safiya itace mai tuqa motar wadda daga ita har safiya a cikin fargaba suke sbd safiya tsoro da tashin hankalin datake ciki shine Mum din fammah zata iya kashe SANAAH akan hakan batareda kowane tinani ba sbd silar tsananin tsanar datake tsakaninta da Hajiyar samad yanzu sbd maganar kishiya ne kadai gashinan ta tsaneta babu balai da masifar da bata kirawa hajiyar sbd hakan wanda tasani da zata samu dama ko kan hajiyar zata iya bi da mota sbd kadai tayi maganar Fleet da qarin aure.

Ko mommy da suka baro gida a cikin zullumi take tana fatar allah dai ya saka ba ciki ne da SANAAH ba kafin tarewanta ko Dad batasan da wane idon zasu kallesaba ga tashin hankalin Meenah da basuma san daga ina lamarin zai fara ba gwara ace babu komai har sai an sanarwa meenah anyi tarewa.

Suna isa Dr bushrat din na fitowa harabar asibitin zata nufi motarta ta tafi JEERAHsV din sbd kiran da Imran yayi mata akan sakon Fleet.

Parking sukai kusa da motarta tana ganin bumbern da sunan jeerahs ta dakata saida SANAAH din ta bude motar ta fito a natse sanyeda dogon hijabi har qasa idanuwanta sanyeda glasses data hana bayyanarda kumburin idanuwanta data sha kuka gurin waya dashi din.

Da kulawa da sakewa tareda girmamawa Dr ta kalleta tana cewa

"Patient din tawa ce ta taho da kanta bayan can nayi gurin dubaki,
Yaya jikin?
Mu shiga daga ciki to"

Ciki sikai SANAAH na dan bude baki da sanyi tace

"Alhamdllh naji dan sauki"

Office din Dr bushrat din suka nufa tana kokarin sake tambayar jikin SANAAH din da dan karantar yanayinta tin daga nan dan haka suna shiga ruwan sanyi ba sosaiba ta dauko mata daga fridge tazo ta zauna suna fuskantar juna tace

"Menene matsalan?
Gashinan dai i can see you look pale and anxious when last kika samu period naki??

Qarasa mutuwa jikin SANAAH yayi da tsananin gaske ta dan dago idanuwanta da sukai jajir ta kalli dr din ta bude baki tace

"I cant remember"

Numfashi dr bushrat ta sauke tana cewa

"Taso muje na duba wani abu"

Miqewa SANAAH tayi daqyar gabobinta ba karfi ko kadan tabi bayanta.

Anan suka bar safiya tsawon mintina masu tsayi sosai kafin suka dawo office din suka zauna idanuwanta sun sake fadawa da sauyawa tayi wani irin sanyi koina jikinta cikin damuwa mai tsananin gaske take ciki dr ta kalleta cikin lura da yanayinta dan haka sai batai wani dabbakawa ba tace

"SANAAH ciki ne dake kusan wata biyu da kwanaki"
#MAMUH
09033181070
[13/06, 2:08 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

114
Wani amai ne ya taho mata da karfi da tsananin sauri dr tayi toilet din cikin office din da ita tafara yinsa cikin galabaita da tashin hankali.

Daqyar ya dakata suka fito jikin SANAAH din na dan rawa.

Ruwa da wani dan magani ta dauko ta bata tasha ta danji sauki sauki ta kasa cewa komai itama dr din kasa cewa komai tayi sukai shiru safiya ma zuru tayi.

Dr ce ta yanke shirun da cewa

"Kada ki saka damuwan komai a ranki fa sbd Kinga yanayinki a yanxu sakawa ranka fargaba ko tashin hankalin koma menene zai iya saka cikin a hadari harma dake so pls be very very cautious"

Magani ta dauko mata na masu ciki su folic cid da sauransu ta bawa Safiya ledan ta rakosu har mota.

Tana barin asibitin Dr Bushrat da sukai alkawarin duk abinda ya samu SANAAH zata sanar masa tin wancan lokacin daukan wayarta tayi kawai tai masa sending sakamakon da scanning datai mata.

SANAAH kuwa kai tsaye gida ta nufa zazzabi me karfi na rufeta driving dinma cikin tsananin karfin hali tayisa suna isa ko parking batai daidaiba ta tsaya daidai nan motar hajiyar Samad tayi parking a gefen tata motar suka fito kusan a tare hajiyar na waya idanuwanta suka sauka akan SANAAH wani mummunan shock ya shigeta ta tabbata kenan SANAAH dince ta gani a asibiti tareda Dr bushrat sun shiga dakin scanning ita kuma taje duba wata yar kaninta data samu miscarriage.

Rikicewa tayi a take sbd kallo daya tayiwa SANAAH din wadda suke kusa batama tsaya lura da hajiyarba ta wuce ta ga alaman mai ciki a tattare da ita kanta yai mugun sarawa zufa ya keto mata dan kuwa wlh bazata yadda da Raheem ya amsa auren SANAAH ba bare ciki sedai idan wani gurin akayo matashi wanda wlh saita tona duniya taji idan kuma na Raheem ne wlh sai duniya taji shima batasan lokacinda a rikice bakinta ya furta

"Yanzu SANAAH dince da ciki kokuwa gane gane nakeyi na shiga uku"

Samad da kaman saukar tsawa yaji zancen jin yayi kansa ya dauke wuta dip ya bude baki muryansa na sarkewa da shock din da bai taba shigaba a rayuwarsa yace

"SANAAH danake jira ce da ciki ko kuwa wata SANAAH din???

A rikice hankalinta na sake tashi tace

"Allah yasa cikin shege ne a jikinta dan idan na Raheem ne bugawa zuciyata zatai na shiga uku"

Kashe wayarta tayi tana sake shiga tsananin mamaki da rikicewa tayi cikin gida.

SANAAH kuwa sbd sanin kowa yana palon su mommy ya sakata juyawa ta nufi bangarensu Fammah ta nufi dakinsu ta zare takardun asibitin daga jakarta ta saka a cikin wata qaramar jakarta ta maida cikin kayanta ta ajiye ta fito nufi bangaren suna shigowa kuwa fammah ta amsa jakarta tana dubawa da tsokanar inda taje.

Bata iya cewa komaiba ta wuce ciki tana dan boye damuwanta.

Daki suka nufa fammah na biye da ita tana magana kai tsaye bathroom ta shige.

Tubewa tayi ta sakarwa kanta ruwa tareda fashewa da wani irin kuka tsawon lokaci kafin ta fito.

Safiya ce ta kawo mata abinci a tray ta ajiye mata tareda juyawa da maganin data shigo dashi bata ajiyeba ganin fammah a zaune.

Zaunawa tayi bayan ta shirya ta kasa cin abincin da aka ajiye tareda kasa kallan fammah tai shiru tana dan kwantawa kadan bayan tayi sallah.

Kasa hakuri fammah tayi ta kalleta da bada dukkanin nutsuwa tace

"Akwai abinda yake faruwa dake wanda bansan menene kike kasa fada mun ba,
Akwai wani abin ne?
Menene matsalan?
Can you pls tell me right now sbd dai duk kin sakani damuwa wlh"

Girgiza kai tayi tana sake kasa iya kallan famman.

Shiru sikai daga nan fammah ta miqe ta fice daga dakin.

Tana fita mommy na shigowa kallo daya tayi mata ta nemi guri ta zauna bata ce kala ba dan a fuskan SANAAH din komai dai ya bayyana.

A daki ta wuni har dare bata kuma fitowaba sai da daddaren harta kwanta ta dauki wayar Mommy a karan farko rayuwanta ta saka kiransa kaman bazaa dagaba sai aka daga kiran tana jin muryansa ta fasa masa wani lafiyayyan kuka tana cewa

"Ni mutuwa ma zanyi sbd bansan ya zanyi da rayuwata ba"

Kalamanta suka sakasa yin shiru sbd tin dazu sun kasa samun wayar Dr bushrat dan haka miqewa tsaye ya sake yi kansa na balain sarawa da abinda ta furta masan ya bude baki zaiyi magana sai kuma kawai ta kashe wayar gabaki daya dan ko magana bataso.

Bin wayar yayi da kira yaji shiru dan haka ya saka kiran Imran yana dauka kai tsaye yace ya siya tickets din tafiyarsu.

SANAAH kuwa kwana tayi kukan gaske koda gari ya waye da wani sabon ciwon ta tashi wanda ya saka Mommy yanke shawaran sanar dasu Dr Mum dan haka kai tsaye dakinta ta nufa.

Hajiyar Samad ma da babbban tashin hankali ta tashi kaman zata dora hannu akai ta zunduma ihu sbd Samad ya haukace a lokaci daya ya zare ya siya ticket din dawowa.

Batajin zata iya barin ya dawo yayi abinda zaa aikasa lahira tsakanin ubansa da Raheem dan haka gwara ta tada balai a gidan dazai hana a abinda samad zai dawo yi fitowa dan haka bangaren Ms Meenah ta isa tinda tanata kiran Samad din tin cikin dare bata samu ta tabbatarda yana hanya kowane lokacin jirginsa zai iya dawowa.

Tana isa bangaren bata tadda Meenah ba fammah data fito daga bedroom dinta tafara gani cikin sakewa da nuna hankalinta a kwance yake tace
Chapter 116 · 0% Book details