← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 154

Sashe 90

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran asuban farko akeyi koda yayiwa Imaran kiran sbd baya buqatan Dr Mum ta dubata dan kaucewa sanin abinda ya faru.

Fitowa Imaran yayi danye da three quarter wando da sweater black ya nufi mota yana da wayarsa a hannunsa yana waya da Dr bushrat wadda take kaman likita babba ta musamman a asibitin jeerahs kuma itama a cikin anguwan take dan haka kai tsaye imran ya saka aka turo masa numbernta yanzu ya sanar da ita Fleet ke buqatanta da gaggawa.

Imran na isa gate securities sunyi mamakin ganin fitowansa a daidai wannan lokacin.

Bude masa gate akai ya fice da wata speed yana waya da dr bushrat din har lokacin.

Yana ficewa securities suka kira Mr Sideeq sbd babu kowace shige da fice da ake boye masa na irin wannan lokutan.

Da mamaki Mr Sideeq din yace zai fito sallan asubar zaiji ko lfy.

Koda imran ya isa ya daukota tana gidanta kuma daman ba miji ne da itaba daga ita sai yayanta biyu da masu aikinta suka juyo JEERAHsV.

A lokacin ana kokarin shiga sallan asuba dan haka Dad jeerah na fitowa yaga dawowan Imran da Dr bushrat baiyi tinanin komaiba ya shiga masallaci Mr Sideeq ma lokacin ya iso tareda head of security na villah din suna magana.

Dr bushrat na isa ya bata daman duba SANAAH din ya fito masallaci sallar da aka tayar wadda bai taba lattin fitowa ba sai ayau din.

Koda aka idar da sallah kallansa Dad yayi a natse kaman zaiyi magana sai kuma ya bari sai da safe dan haka gaisawa kawai sukai Raheem din ya tafiyarsa hankali kwance cikeda wata nutsuwa da kamewa da steez din dayake jininsa.

Fitowa sukai Mr Sideeq yana tareda Dad din wanda ya kallesa yana kamewa a dattijonsa ya dauke kai yana maidawa gabansa da tafiya ta nutsuwa da kamala yace

"Meyake faruwa ne naga kaman daya daga motocin Fleet sun dawo da duhun asubar nan akwai wanda ya kwana a waje ne kuma naga kana magana da securities"

"No babu sunce da tsakar daren ya fita ya dawo da Dr bushrat ne tana ciki yanxu haka kuma acan bangarensa inaga taje"

Shiru Dad yayi tareda dan dakatawa cak kadan yana dagowa ya kalli Mr Sideeq din tukuna ya daga kafafunsa yaci gaba da tafiya yana wucewa ciki yace

"Ina buqatan ganinta idan ta fito kafin tabar Villah dita"

"Yes sir" Mr Sideeq ya fada yana juyawa dan baza nasa takun na isar da ita idan ta fito.
#MAMUH
09033181070
[04/06, 10:37 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

84
Dr Bushrat kuwa a lokacinda ta isa bangaren da kansa ya dauko SANAAH din a jikinsa ya kawota dakin da zaa duba ta ya kwantar mata da ita ya dago idanuwansa masu karfin gaske ya kalli Dr bushrat din kadan ya bude baki yayi mata magana kafin ya fice dan bata daman dubawan ya nufi masallaci.

Numfashi Dr bushrat ta sake a tsanake da dan mamaki dan kuwa tin bata taba SANAAH din ba kai tsaye ta fahimci meya faru..

Mamakinta mai tsanani shine na tabbatarda Fleet ne ya kwana da SANAAH din a cikin gidansa da iyayensa suke ciki batareda kowace shakka ko kiyayewa sbd batasan matarsa bace,

Amma kasancewanta ba wani kamata addini yayi ba sai bata jima a mamakinba dan tasan a yanda rayuwarsa take zallan baturen da bai tashi a hannun iyayeba sai taga kuma ba illa bane dan ya kwana da duk macen dayake so.

Cikin kulawa da nutsuwa da tattalin data gani a lokacinda ya daukota daga garesa ta duba SANAAH din dakyau taga taji jiki sosai da tana buqatan kulawa mai girma sosai dan haka bathroom din dakin ta shiga ta fara hada ruwa mai zafi ta dawo ta dauketa da kanta takaita cikin ruwan ta saka kawai.

Tsantsan azaba ya dawo da SANAAH din wadda ta bude idanuwanta da suka kumbura jajir ahankali daqyar ta kalleta amma batama gane wace ba dan haka ta koma ta sake sakewa wasu zafafan hawaye masu zafi suna gangarowa daga fuskanta tana kasa motsawa duk da azaban datake ji din.

Saida ruwan suka huce Dr ta sake sauya mata wasu ta budeta dakyau a cikinsu har tsawon lokaci sai da SANAAH din ta samu dan sassauci da karfin iya motsawa da iya bude baki tana kuka.

Da taimakon dr bushrat data cire tausayi ta bata sosai ta gasu kuzarinta ya dan taho ta samu tayo wankan tsarki ta fito daure da towel kanta na tsiyayar ruwan dake bin lafiyayyar fatarta suna gangarowa da wani slow.

Daqyar take dan iya daga kafafunta ta fito ta shigo dakin wanda kamshin daya shiga hancinta duk da tana cikin wani hali sai data tantance ya shiga hancinta ta dakata cak daga inda take tana dagowa da jajayen idanuwanta da sukai wani irin laushi ta kasa kallan inda taji maganarsa na fita a wata irin nutsuwa da rashin hayaniya da Dr datai masa bayanin ba wani matsala bane ta gurxu ne gashi na farkonta dole zata galabaita tinda baa bita ahankali ba.

Wata irin kuka taji yaxo mata sbd kalaman da kunnuwan nata suka danji tsabar kunya da damuwa da tsoro da fargaban kowa da komai...

Dagowa yayi da idanuwansa da har lokacin cikin nutsatsiyar yanayi suke ya saukesu akanta ya yiwa fuskanta wata lafiyayyan kallo kafin ya maida idanuwan ga gashinta dayake digar wasu ruwa ahankali ahankali....

A kirjinta da wani ruwan ya diga akan idanuwansa ya kalla yana bin ruwan da mayun idanuwansa suna gangara da wani irin slow har suka isa gaban towel din jikinta suka gangara suka shige ya dago da idanuwan cikin wata shegiyar slow akan fuskanta data dago idanuwanta ba tsammani suka shiga na juna sbd jin kallansa na azabtar da gangar jikinta.

Yankewa numfashinta yayi da oily kwayar idanuwansa suka shiga cikin nata ta dauke kai da tsananin rikicewa da fargaba da sake shiga tsoron rayuwarta ma gabaki daya tana daga kafafunta daqyar tafara takowa sbd dr data buqaci ta qaraso.

Akan tafiyarta da kafafunta da cinyoyinta dake wani daukan idanuwa sbd haske da wani kyallin da suke ya gangaro da idanuwansa har lokacin babu kalma daya data fito daga bakinsa sai idanuwansa da suka saka room din karban zazzafan tension dan ita kanta dr jin tayi zafi na taso mata bare SANAAH da zata iya sake shiga hannunsa.

Miqewa dr tayi ta qarasa riqota ta iso da ita bakin gado ta xaunar tareda hada allurar da zatai mata tai mata a lokacin ne ya tashi tsaye dan sake basu guri ya iso gabanta ya miqa hannunsa daya akanta ya dan rankwafo kadan sai lips dinsa taji a gefen fuskanta ya sauke mata yace

"Sorry" ya juya ya fice yabar Dr da binsa da kallo kafin ta dawo da kallanta akan SANAAH wadda bata iya kowace Motsiba dik baya cikin hayyacinta ma hankalinta a rikice yake da yanda zata iya fuskantar kowa idan har aka gane halinda ta saamu kanta a ciki.

Sake gasata da towel da wasu irin ruwan zafi Dr tayi a iya gurin kawai kafin ta dora mata da magani take ta dan sake samun kuzari kadan amma zazzabi ma take jin kaman zai dawo mata.

Sallah tayi daqyar tana gamawa dr ta kwantar da ita a gado ta rufeta take bacci mai karfin gaske ya dauketa.

Kashe mata wuta dr tayi ta fito tana duba time lokacin haske yafari sosai dan karfi bakwai ta dan gota.

Bata samu ganin Fleet dinba dan haka ta nufo kofa kai tsaye tana fitowa Imran yana waje tsaye yana waya yana jiran fitowanta.

Da hannu ya nuna mata hanya yana wucewa gaba tana biye dashi yana waya har lokacin cikin nutsuwa da qwarewa a aikinsa dan komai nasa kusan akan aiki ne dan haka ko yanxu kaman ma wayar conference ce bashi daya bane.

Itama wayarta ta fiddo tana duba time da kokarin saka kira sai ga Mr Sideeq ya qaraso gabanta suna gap da isa motar da aka juyawa Imran din kanta tini dan yana fitowa shiga kawai zaiyi yaja.

Kallan Mr Sideeq tayi tana sake fuska da sanayya sosai tace

"Ah ah Good morning Mr Sideeq"

Shima a sake da kulawa da mutuntawa ya gaidata yana cewa

"You here da sassafe haka?
Tin jiya ma Sir jeerah ya buqaci ganinki amma tinda gaki a yanxu can you pls.....

"Yes yes Allah yasa dai lafiya Sir da kansa yake nema" ta qarasa maganar da sakewa da murmushi imran Mr Sideeq ya kalla da kulawa yace da kansa zai maidata.

Da girmamawa Imran ya kashe wayar dayake yi ya kallesa yace

"No zan jira ta gama da Dad din then na maidata"

Ba damuwa" Mr Sideeq din yace sbd yasan babu yanda Imran zai taba iya wasa da umarnin ko aikin Fleet din duk da yasan sbd Dad ne da kansa ya buqaci ganin Dr din shiyasa ma yabarta tafiya da babu wanda ya isa yayi hakan duk duniya.

Kai tsaye palon Dad din na farko Mr Sideeq din ya iso da Dr wadda tana ganin sir jeerah din ta qaraso da girmamawa ta gaidasa a tsanake.

Amsawa yayi yana nuna mata gurin zama ta zauna tana sake gaidasa da yar sakewan datake tsakaninsu dan mijinta kafin ya rasu shine babban likitan familyn kaf wanda sukeda kusanci sosai.

Yaranta da suma kusan duka likitocin ne ya tambaya yana dan shiga da ita firar aikinta tana basa amsa suna firarsu kaman yanda suka saba kafin ya kalleta da kyau ya jefa mata tambayar data sakata dagowa ta kallesa sbd batasan yaya zata amsaba tinda aikin daya kawota kaman sirri ne hakama a tsakanin likita da patients sirri ne da ba kowa ake fadawa ba.

"Dr inada mara lafiya ne da naga an dauko ki da duhun dare?
Akwai me matsala ne?

Dan shiru tayi tana dan kokarin kaucewa amsawan kai tsaye.

Sake jefa mata tambayar "Akwai matsalar kenan,akwai wanda ba lafiya kenan sosai?" yayi ta sauke ajiyan zuciya tana hana bawa zancen babbar mahimmancin da zaiji nauyin zancen tace

"No Sir Babu wata matsala ko mara lafiya sosai Ms SANAAH ce ba lafiya na dubata kuma gaskia da sauki dan tama samu bacci"
Chapter 90 · 0% Book details