← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 154

Sashe 31

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

30
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Bayan sallamosa din duk yanda suka so ya sake hutawa kafin komawa kowane aikin wahala sam baida wannan lokacin yake gani sbd buri ne a kullace cikin ransa da idan bai cikasa ba zai iya mutuwa sbd baqin ciki da zafi,

Baida niya ko daya ta yafewa AA abinda yayi musu sbd ya shirya bin haqqin abinda yayi musu daga nan har kotun qoli koda zai rasa ransa saiya tabbatarda anbi musu haqqinsu koda basu da komai indai hukuma na aiki.

Dan haka koda yayi jinyar kullum da wannan kullin baqin cikin yake kwana yake wuni sbd kusan hakan ya ruguza rayuwarsu gabaki daya wadda suka debo shekaru suna ginawa cikin aminci da tawakkali da gwagwarmaya,

Ga mommy yanzu ta riga ta rasa lafiyarta kila sbd hakan,

Ga anguwan yanzu sunaji suna gani yi akeyi dasu komai fada akeyi akan SANAAH dasu,

Karatunta ya tsaya sbd hakan sbd sam bata iya fita bata iya zuwa koina su kansu sunji sunfi nutsuwa da kwanciyan hankali idan tana gida dan haka karatunta ya samu mummunan matsalar da ba lallai qarasa shi.

Washe garin ranar da aka sallamosa din da safe yayi wanka ya fice daga gida bayan ya zauna yasha ruwan lipton din da SANAAH ta dafa masa da bread yana sha yana kallanta zuciyarsa na sake shiga duhu da dacin tsananin tausayinta dana mommy dashi kansa dan haka duk ya kallesu damuwansa ke qaruwa.

Yana fitowa gida akwai mutane a layin sosai dan haka babu inda ya tsaya yana kawowa a natse zai gaidasu ya wuce batareda ya tsaya ba sbd daman baya tsayawa zama ko fira koina bare yanzu da duka yana iya gani a idanuwansu wani kallan na daban suke masa manya da matasa da samari.

Kai tsaye babbar police station din dake central ya nufa,
Yana isa kaman yanda yaga layin karban cases tsayawa yayi yana dan tsayar da hankalinsa da tinaninsa akan abinda ya kawo sa batareda bawa kowane case dayaji anayiba mahimmanci sbd abinda yake gabansa ya wuce ya tsaya sauraro ko bawa matsalar wani mahimmanci.

Shiru yake a tsaye har layi yaxo kansa ya qarasa har gaban babbar kantar da ake karban case ba.

Numfashi me dumi ya sauke a natse ya jerowa officer din bayanin komai tareda bayyanarda haqqinsu yake son a bisu musu AA ya karbi hukuncin abinda yayi musu.

Gama sauraronsa officern yayi kafin ya sauke numfashi mai nutsuwa yace

"Menene cikakken sunansa shi AA din?
Kuma menene address dinsa da gurin aikinsa da sauran bayanai akansa?

Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalli officern yace duka bansan su ba amma dai cikakken sunansa shine ABDULSAMAD ABDULHAKEEM"

da zallan mamaki officern ya dago da duka idanuwansa ya kalli Al'amin din ya bude baki zaiyi magana sai kawai ya fasa yace masa ya basa numbern AA din ya jirasa.

Yana karban numbern miqewa yayi yayi ciki zuwa office din babbansu.

Ya jima a ciki kafin ya fito ya kalli Al'amin yace ya taso ya biyosa.

Tashi yayi yabi bayansa suka shiga ciki.

Suna shiga qare masa kallo tsaf dpo yayi ya bude baki batareda yace ya zauna ba yace ya sake masa bayanin komai.

Sake bayani Al'amin yayi tareda sake tabbatarda neman adalci daidai yanda sharia tace akan AA.

"Mun karbi komai na case din zamu nemeka idan mun taho dashi nan,
Amma ka sani bazaka kai wata qarar ba sai mun tabbatar maka da mun gama komai."

Shiru Al'amin yayi sbd ganin yanda dpo yayi maganar kafin yace shikenan ya tafi.

Daga can gurin nemansa ya nufa bai dawo gida ba sai dare.

Anan ne ya sanar dasu ya saka qarar AA dan haka su sani sharia zasuyi dashi.

Tinda SANAAH taji hakan jikinta ya qara sanyi sbd a yanzu kam tasan kowa duniya zai san abinda ya faru da ita dan haka take taji ta qara tsanar shiga mutane da fita koina.

*****kwana biyu shiru shiru ba kowane bayani ko kira daga police station din dan haka sai kawai ya sake komawa dan jin bayani,

Yana zuwa kwata kwata qin basa dama da mahimmanin bayani sukai a station din gabaki dayansu dan haka ya tafi office din dpo da kansa anan ma kai tsaye dpo ya sanar masa sun watsar da case dinsa dan babu sheda babu ma hujja ko daya dan haka ya tafi kawai yajawa kanwarsa kunne daga bin maza masu kudi.

Shiru yayi idanuwansa jajir jininsa na wata irin tafasa da kunar da idonsa har gani sika rage ya miqe ya fito.

Bai koma gida ba kai tsaye wata police station din ya nufa ya sake saka wata qarar wadda ita anan take ma sukai rejecting din case dinsa suka koresa.

Bushewa yaji zuciyarsa nayi sbd abinda yake shirin tabbatarwa na power ake shirin nuna masa ko me.

Wata station din ya nufa wadda acan ma korarsa sukai,

Bai hakura ba sbd jin yana sake rasa hankalinsa akan lamarin haka ya ringa yawon station a ranar gabaki daya baije gurin kowane aiki ba har dare yana yawon da rayuwarsa ke shiga tashin hankalin abinda yake gani.

Sai dare ya dawo sosai a matiqar gajiye da damuwa me tsanani da mutuwar jiki da wani irin nauyin kirji ga bakinsa a bushe komai nasa ya bushe.

A yanayin dayake ko abinci bai iya ci ba haka ya shige ya rufe dakinsa ya zauna ya fasa wani irin kuka mara sauti yana dafe kirjinsa radadi na gewaye har gangar jikinsa.

Su kansu mommy jikinsu mutuwa yafara yi da yanayin case din dan haka Mommy tace masa su hakura kawai da safe amma bai iya hakura ba haka ya dake bazama yawon kowace station.

Station din daya isa ta hudu a ranar Rufesa ma sukai kawai suka masa dukan tsiya tareda rufesa cikin rashin imani sukace sai anmanta dashi ko zasu sakesa.

Su mommy dake zaune gida shiru shiru ba Al'amin har dare yayi sosai dan haka hankalinsu ya tashi mommy ta kasa barin SANAAH taje ta nemansa saidai suka fita tare a daren.

Dayake sun san case din dayake yawon yi sai kawai suka fara yawon stations a daren nemansa suma.

Dare yafara yi sosai dole suka dawo gida cikeda damuwa da tsoro har gari ya waye suna zaune batareda sun rintsa ba.

Karfe takwas na safe suka sake ficewa suna yawon da duk station din da sukaje kusan sai an gane sune masu qarar da Al'amin din ke yawo da ita.

Basu samu station din dayake ba sai yamma sosai gap da magrib kuma aka qi barinsu ganinsa dan haka anan suka kwana waje suma cikin tashin hankali da damuwa.

Washe gari da safe wani sabon dukan akai masa akan saiya janye karar kuma kada ya sake yawo da ita amma yaqi amince da hakan,

Duk azabar da suka ringa gana masa sam bai janyeba sbd ya shirya mutuwa akan haka amma indai akwai inda zaa karbi qararsa da korafinsa to tabbas zaije.

AA da kansa yazo station din ya tabbatar musu da koda zaa raba Al'amin da duniya ne ayi da abari zancen ya fita sbd gwara yayi ajalinsa daya bari ya fidda abinda zai taba martaba da sunan ahalinsa dayasan akan hakan mahaifinsa ya gwammaci ace mutuwa yayi ya bar duniya daya bata masa sunan da duk duniya take girmamawa da shakka.

SANAAH data gansa a lokacinda ya fito taso zuwa rokonsa akan a saki yaya Al'amin din sun janye kowace qarar amma sam yaqi barin ma ta iso ya bar gurin sbd idan ya ganta a gabansa ya kalli idanuwanta zai iya rasa control na kansa akan zazzafar soyayyarta bayan a yanzu yana cikin siradin da zai gwammaci batar dasu gabaki daya har ita akan maganar nan ta fita ta isa kunnuwan mahaifinsa da zai iya harbesa da bindiga akan hakan.

Mommy ce ta qasqantar da kanta tana kuna ta roki manyan officers din da case din yake hannunsa akan cewa sun janye tayi musu alkawarin bazata bari Al'amin ya sake kai qara kowace irin hukuma ba tukuna suka amince zasu sakesa.

Gida akace su tafi zaa kawosa har gida.

Bayan tafiyarsu sai da ya kuma kwana yaci wata irin azaba a hannunsu kafin suka sakosa aka kawosa da motar yan sanda a wulaqanci a gaban yan anguwa da suka ringa yada wata muguwar zunden.

SANAAH ce da kanta ta fita ta kamosa suka shigo gida yana takawa daqyar sun sauya masa kamannin da ko kuka dasuka gansa kasa yi sukai sbd bushewan kunci a kirji.
Chapter 31 · 0% Book details