← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 154

Sashe 74

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin manta kincewa fammah you don't want to burn your skin,be careful"

Bude idanuwanta tayi cikin wani irin slow dayake fita da numfashinta a slow din shima sbd kowace kalmansa fitowa takeyi da iskan dayake sauka gefen fuskanta zuwa hancinta.

Motsawa tayi tanason janye hannunta sbd tsayuwan na neman gagararta kafafunta sunyi wata irin nauyi.

Ganin ta kasa zare hannuwanta a qarqashin nasa duk da ba wani matse hannuwan yayi ba ya sakata dakatawa tana bude baki ahankali ta furta

"Dr Mum ce tace na kawo"

Yanda tayi maganar can qasa qasa ya saka idanuwansa sauka akanta da kyau ya saketa yana zare hannuwansa sbd kallan fuskanta dakyau yayi magana da ita.

Yana zare hannuwansa nata hannuwan basa sauran karfin iya riqewa dan haka tray din ya tafi gabaki daya a hijabinta yana barewa.

Wani irin radadi da azaba taji ta ratseta tayi ta rintse idanuwanta da karfi tana ja baya da dan karfin daya kasa riqeta sedai shine ya sake riqeta da dan sauri yana kallan hijabinta da wata yanayin da babu wanda zai iya gane asalin na menene.

"Shit" ya fara da sautin da ko ita bata jiba kai tsaye sai jin tayi ya yaye hijabinta gabaki daya yana kallan cikinta da silk rigar baccinta ta lafe akai da ruwan tea din.

Hannunsa yakai a gurin ba tsammani taji saukansa da wani irin shoch tayi baya tana jin azaba da tashin tsigar jiki a lokaci daya.

Ganin hakan ya dago ya kalleta yaga idanuwanta tini suka ciko da hawaye.

"Kin kone?
Kina jin zafi right??

Samun kanta tayi da daga kanta idanuwanta na sake cikowa da hawayen da kalamansa suka sakasu gangarowa bama tareda da saninga ba sbd yanda yayi tambayar.

Hannunta ya kama kawai ya wuce da ita hanyar bedroom dinsa tana ganin sun shiga palonsa zai nufi bedroom dinsa da ita tai saurin son dakatawa amma yanda takeji da yanda yaje tafiya da ita tafin hannunsa hade da nata ya saka bakinta da kafafunta kasa komai suna isa bathroom dinsa dayake tsare da luxuries tako ina kai tsaye bakin ruwa ya isa da ita yakai hannunsa ya kunna ya debo ruwan a hannunsa daya ya zuba kai tsaye a gurin da rigarta ta maqale mata da ruwa a cikinta.

Wani numfashi mai tsananin karfi da rashin sauti ta sake tana rintse idanuwanta da karfi sbd azabar dataji da kuma sanyin ruwan a Lokaci daya.

Sake debo ruwan yayi a hankali da wata irin kulawa ya zuba mata yana dora hannunsa a gurin....

Sake daukewa numfashinta yaso yi ta riqe cikin karfin hali tana sake rintse idanuwanta tareda dafasa batareda ta saniba.

Hannunta ya dago ahankali ya kalla akan gefen cikinsa data dora batareda ta saniba.

Fuskarta ya dago yayiwa wani kallo idanuwanta na rintse har lokacin tana kasa budewa.

A natse ya dawo da kallansa a inda ta kone din ya miqa hannunsa daga inda yake ya dauko cream na hana skin ya tashi bayan ruwan zafi sosai yataba ko wuta....

Ahankali yakai gwiwowinsa qasa yana yana kallan cikinta cikeda kulawa a natse yakai hannunsa ya yaye rigar daman riga da wando ne a jikinta na bacci...

Bataji yayewan rigartaba sbd zafin da gurin yake mata saida hannunsa ya sauka akan fatar cikinta zuwa gurin cibiyarta ta bude idanuwanta da wani irin sauti numfashinta na yankewa da wani irin karfi...

Baya tayi sedai already hannuwansa sun riga sun zagayota a yanda yake din gabanta kan gwiwansa ya dawo da ita cikin wani slow da dan karfin da saida mararta ta hadu da fuskanta.

Ya rufe idanuwansa ahankali batareda ta ganiba ya bude ido wani slow ya dago ya kalleta itama shi ta kalla idanuwanta na cikowa da wasu hawayen ta bude dakyar ta furta

"Please"

Dauke idanuwansa yayi daga fuskanta yakai fuskansa cikinta har saida lips dinsa sukai wata haduwa da fatar qasan cibiyarta ya bude bakinsa ya fara hura mata wani iska a gurin wanda ya sakata kasa riqe hawayenta suka gangaro.

Sake kai yatsun hannuwansu biyu yayi akan fatar ya sake shafa mata cream din cikin slow din daya sakata dora hannunta akansa da sauri tana sake bude baki zatai magana ya sake hura mata wata iska a gurin daya sakata kasa magana sbd riqe kanta daga sautin dazai iya fita ba daidaiba.

Cigaba da hura gurin ya sake yi idanuwansa na kan fatar cikin nata datake fara tas sai jan data dan yi kadan na zafin cibiyarta ya zubawa ido yana ganin yanda numfashi yake sauka a cikinta yana saka cibiyar motsawa ahankali kadan ya dago kansa ya kalli fuskanta data kasa bude idanuwanta kwata kwata ya miqe tsaye ahankali kirjinsu ya hade da juna ahankali wanda yaji yanda kirjinta sukai masa wata irin ratsa da gugar data sakasa sauke ajiyan zuciya mai sauti tareda futar wani numfashi mai zafi akan fuskanta ta bude ido a kasalance ta kasa kallansa tana ja da baya kadan sedai tafin hannunsa na kan cikinta har lokacin sai ya riqota da hannunsa daya ta baya ya sake dawowa da ita da dan karfin data fado kirjinsa ya mata wata kyakkyawar runguma yana sakata tsakiyar kafafunsa cikin wata nutsuwa da kwanciyan hankali da tinani kala kala akansa gameda komai daya shafeta da aurenta dayake hannunsa da iyayensa.
#MAMUH
09033181070
[15/05, 11:52 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

69
*NOOR COLLECTION*
09035841194
Best luxury shop da zaku samu kayan da zaa san kun saka sitirar alfahari masu best quality kamar su;
ABAYA'S
JALLABIYA
SNEAKER'S
KAYAN YARA
NEW BORN BABIES ITEMS
MAYAFAI (veils)

Hakama ko ba abinda muka lissafo ba ana iya turomana orders din wasu abubuwan idan anaso,

Our addresses sune;
EGYPTIAN ADDRESS: NEW CAIRO.
NIGERIAN ADDRESS: Zaria, low-cost, prof Adam sa'id resident.

PHONE NUMBER:
+234903 584 1194
+234 704 420 4680
Whatsapp.
LINK, https://whatsapp.com/channel/0029Vaoa1YN77qVImYa4ZF02

*********
A daidai wannan lokacin ne ita kuma fammah ta gama hada nata tea din ta nufi bangaren kakanta dan kai masa.

Tana shiga da tray din a hannu karan farko da wani ya kawo masa tea dinsa ba SANAAH ba tinda ta fara kawo masa dan haka a tsanake yana dan duba wayarsa ya kalli fammah cikin kulawa da sakewa dan itama yar gaban goshinsa ce yace

"Likita tau kece kika kawo,ina 'yata??

Ajiyewa tayi tana zaunawa qasa ahankali da sakewa sosai a fuskanta ta gaidasa tukuna tace

"Dr Mum ta aiketa takaiwa Dad shine ni tace na kawo maka naka"

Dagowa Dad yayi ya kalleta a natse da jin kalamanta yayi dan shiru kafin ya sake murmushin manya mai sanyi ya ajiye wayarsa yana cewa

"Ita mahaifiyarki tana tareda su Dr din kenan??

Gyada kai tayi tana zuba masa tea din da cewa

"Eh amma yanxu damun koma zamu wuce gabaki dayanmu"

Jinjina kai yayi yana gane kai tsaye manufar Dr dan haka ya sake murmushin yabawa karfin halinta dan haka ya dauki wayarsa daya aje gefensa ya nemo numbernta da shine ya saka aka kawo musu layukan ya tura mata sako tareda ajiye wayar gefe yana karban tea din da fammah ke miqo masa tana masa zancen sabon bangarensu da suka koma.

Dr Mum dake zaune a palon tareda dukansu har lokacin tana kallan wani program da ake a tv hankalinta baya kan firar dasukeyi taji shigowan sako a wayarta dake gefenta.

Dan juyowa tayi ta kalli wayar taga number ce ta turo sako takai hannunta a natse ya dauko wayar ta bude sakon.

Abinda ta gani ne ya sakata dagowa ta kalli su maamah dake fira ta maida kallanta kan wayar cikeda mamaki da takaicin gane mai sakon daga maganarsa daya turo mata wadda ta sake sakata mamakinsa mai tsananin gaske.

"KINA BUQATAN QARIN LOKACI KO KUWA NA SAKO MIKI JIKARKI TA DAWO YANXU?"

sake karanta sakon tayi tareda ajiye wayarta gefenta tana hade fuska sosai da takaicin ganin sakon nasa ta maida kallanta kan tv amma ta kasa ci gaba da kallan sbd hankalinta daya rabu biyu,

Batason basa amsa ko kula duk shaanin daya shafesa amma kuma taji tana buqatan lokacin dayace zai bata din dan haka ta sake daukan wayar tana sake hade fuska sosai kaman yana ganinta ta tura masa

"I need more time din"

Tana turawa kashe wayarta tayi tareda dungurarwa gefenta tana maida hankalinta akan firar dasukeyi din tafara kokarin saka baki dan ganin yanda Meenah take firar hankalinta kwance batada alamar tafiya ga mijinta wanda badan Akwai wata macen tasa datake can ba yanxu haka da korata zatai tinda ita bata san ta tafi ba a tinaninta ta riga ta gama samunsa nata ne ita daya ba saita wahalar da kanta ba a yanxu.

Sakon na shigowa wayar Dad ya kallesa daga gefensa ya karanta batareda ya dauki wayarba.

Murmushinsa mai nutsuwa ya sake sakewa yana kai cup din bakinsa ya kurba cikin tsanaki kafin ya kalli fammah dake kokarin tashi ya dakatar da ita yana fara jero mata tambayoyi masu tsayin da zata dauki lokaci a gurinsa dan bada amsoshinsu duka dan haka ta koma ta zauna tana sake fuska da walwala tafara magana hankalinta kwance da jin dadin firar da zasuyi din.

******SANAAH kuwa datake jin kirjinta na bugawa da karfi a kan nasa kirjin dayake hade da nasa cikin wata kyakkyawar mannuwan da yayi mata a jikinsa hannuwansa na zagaye da ita sake motsawa tayi tsigar jikinta na tashi gabaki daya sbd zallan fatarsa data gadu da tata.

Shi kansa dumin fatar jikinta ne yakejin tana shiga fatarsa ahankali ya bude idanuwansa tareda dan sakinta kadan yana bude bakinsa daya kai saitin kunnenta har saida lips dinsa suka gogi fatar kunnenta ta dora tafin hannunta ahankali kan fatar kirjinsa da babu komai zata turesa nasa hannun ya sauka akan hannun nata ya bude baki da wani sauti mai yanke numfashi yace

"Ina son jin raayiki akan auren dayake kanki"
Inason saninsa ko wane iri ne"

Dakatawa tayi cak daga motsawan datakeyi na janyewa tareda qin dawowa ta kallesa sbd kaman daga sama taji zancen shima..

Shiru sukai tanajin dumin numfashinsa yana ratsa fatar kunnenta har cikinsa,

Shima nata dumfashin mai dumi sosai ne yakejin yana sauka akan fatar kirjinsa da babu kaya tana saka jijiyoyin jikinsa fiffitowa ahanki musamman na hannuwansa da wuyansa haka suka ringa bayyana suna fitowa kaman high voltage na shigarsu.
Chapter 74 · 0% Book details