← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 154

Sashe 122

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Maamah taci gaba da bayaninta babu abinda Meenah din takeji sbd jinta ya dauke dip har suka gama suka miqe suka fice bata motsaba bata dagoba bata kuma sake cewa komaiba.

Bayan fitarsu ta miqe ta shige dakinta ta rife kanta a ciki haka fammah ta wuni ita daya cikin tsananin damuwa da jin tashin hankali itama ta koma dakinta ta rufe kanta.

Gap da Magrib Meenah ta fito daga dakinta ta fice kai tsaye bangaren Hajiyan Samad ta nufa ta nufa idanuwanta basa gani sosai tsabar jan da sukai.

Tana shiga hajiyar na zaune da abun wuya a wuyanta daya kumbura tana ganin Meenah ta miqe tsaye da sauri tana kallanta da daukan wani decor na glass dake gurin dan kuwa yau itama a shirye take da aika Meenah din lahira idan ta tabata.

Samad ne ya shigo wanda shima yanayinsa ba sauki ta kallesu duka su biyun tana bude baki kai tsaye tace fada mata yanda akai auren Fleet da SANAAH.

Hajiyar na jin hakan ta dan ajiye abin hannunta tana kallan Samad wanda kai tsaye baiyi tinanin komaiba ya kalleta yace

"SANAAH tawa ce tin farko kuma haryanxu bazata zama ta kowaba"

Wani irin kallo meenah ta masa hakama hajiyarsa sbd sam baida tinani dan haka tai wuf ta amshe zancen da cewa

"Fyade akai mata sbd ubanta ya rufa mata asiri ya aurawa mijinki wanda aka taru kaf dinsu suka boye miki tareda baki ita kika ringa yawon duniya da ita tana kwanar miki da miji.....

Wani mugun numfashi meenah ta fitar jikinta na sake daukan rawa daya saka hajiyar cigaba da zuba mata maganganun dake zarar mata da kwakwalwa gabaki daya dan haka bata baro bangaren ba sai dare.

Karfe daya da rabi na tsakar daren ta fito kai tsaye ta nufi bangaren mommy da dukansu suke ciki kowa baccinsa yafara nisa sosai sbd lokacin.

Wani tafasa da quna da hayaqi kanta yakeyi batajin zata iya numfashi idan bata raba mutanen da suke bangaren gabaki daya da duniya ba dan haka petrol din hannunta ta fara zubawa a kofar bangaren har zuwa baya ta buga ashana kawai tana jefawa fammah datake zuwa dakinta akai akai dubata dan tabbatarda bataiwa kanta illaba dataga bata gantaba ta fito cikin tashin hankali dan zuwa bangaren Dad dinta sai kuwa ta ganta da gudu ta qaraso tana ambatar sunanta da karfin gaske.

Wuta kuwa a bangaren take ta kama gadan gadan sbd sosai ta zuba petrol.

Hajiyar Samad data kwana da shirin babu alkhairi ko sauki a yanayin dataga meenah din kuma a yanda ta zare da jin abubuwa ta tabbatarda a daren meenah bazata rasa abinyi ba dan haka a kunnenta fammah ta kwada kiran mum din dan haka zumut tayi ta taso ta fito.

Wuta tagani da wani irin zafi ta iso gurin tana kallan wutar na ci tafara wani mazari tana son wutar tashiga ciki sosai tafara cin wanda suke ciki kafin tayi ihun ceto sbd so take akan idon hakeem dr fammah taci wuta ta tafi su huta.

Imaran da baiyi bacci ba a lokacin shine yafara jin kaman motsi sbd wutar tafara girma sosai dan haka kai tsaye ya fito yana sako kai ta sama ya fara ganin wutar take ya qarasa fitowa da tsananin sauri Hajiyar Samad na ganinsa ta dora hannu akai tafara ihun wuta da karfin gaske tana nuna meenah wadda fammah ke kokarin janyewa.

Ihunta ya saka securities fitowa da saurin gaske sunayowa ciki take hanayiya ta tashi.

Dad kaman daga sama ya ringa jin ihun wutar hajiyar na cewa

"Innalillahi Meenah ta kona Dr fammah kurmus.....

Bai san ya akai ba sai samun kansa yayi yana fitowa da wani irin mummunan tashin hankalin da rayuwarsa bata taba shigaba yana nufo bangaren dake ci da wutar sosai....

Isowansa tayi daidai da isowan Fleet a asalin futan hayyaci shima yana tinkarar wutar kai tsaye idanuwansa a rufe kaman yanda na Dad din suke a rufe zasu fada Imran da securities suka riqesu da tsananin karfi hankali tashe

Umma ma tini suka fito Samad na isowa kai tsaye yayi kan wutar yana kwala ihun kiran SANAAH idanuwansa a rufe hajiyarsa ba shiri ta saki zaninta tana yi kansa a haukace da ihun kiran sunansa.
#MAMUH
09033181070
[17/06, 10:29 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

122
Cikin tsananin daga murya mai karfin gaske Imran ya bawa securities dinsu da suka qarasa isowa da gudun gaske umarnin su taru su saka karfin gaske su riqe Fleet wanda karfinsa yake kokarin fin nasu gurin kwacewa dukkanin jikinsa na wata irin zabura da karfin gaske yana kiran sunayen Mum da Maamah da SANAAH wadda yakejin sedai wutar ta kone harda shi daya iya kallan su rasa rayuwarsu a ciki.

Hajiyar Samad ma damqar hauka ta fada gap da wutar tayowa samad daya kusan shiga babu wanda ma ya lura dashi bare ya riqo mata shi data wani irin ihu tana qamqamesa gabaki daya da hannuwanta tana jansa da tsananin karfi hankalinta na ficewa daga cikinta masu aikinta biyu da yar riqonta a rikice suka tayata qamqamesa suna jansa yana wata irin fuzgewa yana kwala kiran sunan SANAAH.

Dad ma da dukkanin jikinsa ke wata irin rawa idanuwansa na neman fitowa da asalin tashin hankalin da matiqar Dr Mum tabar duniya ayau yasan bazai rayuba dan haka ya zabi shiga kozasu rasu ya gwammaci rasuwa tareda ita akan yana gani wutar ta cinyeta yana waje dan haka wani karfin gaske yake nunawa kaman ba babban mutum ba yana kwacewa da son fadawa Su Mr Sideeq da soldiers din gidan suna riqesa yana kwala kiran Dr fammah da basu umarnin suyi gaggawan sakinsa amma sam sun kasa.

Fammah da idanuwanta sukai jajir sun ciko da wasu zafafan hawaye masu tsananin radadin abinda yake faruwa takawa da gudu ta isa gaban Dad dinta daya fice hayyacinsa gabaki daya ya tashi daga fleet Raheem mahaifinta kwata kwata data sani ya koma kaman qaramin yaron dayake kallo mutanen dayake tsananin so a duniya zasu tafi su barsa akan idonsa tafiyar dazai rasasu har abada wani ihun kiransu yakeyi yana nuna tsananin karfi amma mutanen da suka riqesa sunfi su shida sun nuna nasu karfin sun kasa sakesa.

Tana isowa gabansa da wani irin karfi ta fada jikinsa ta qanqamesa tana fasa kuka mai tsananin karfi tana kara riqesa itama dan bazata iya ganinsa ya shiga wutarba ta fara kokarin kiran sunasa amma gabaki daya ya rasa hankali da tinani da ganinsa da jinsa.

Imran ne cikin tashin hankali da tsananin sauri ya bawa sauran soldiers din umarnin buga kofar a budeta sbd wutar bata riga tayi yawa a ciki ba daga wajenne tafi yawa.

Ankira firefighters tini dan haka Imran dinne ya fara jiqa jikinsa gabaki daya da ruwan dake harabar gidan cikin wata kyakkyawar roundabout dake tsiyayar ruwa tukuna ya ja baya sosai ya tafi da wani irin gudun gaske ya banki kofar da kafafunsa amma bata bude ba.

Sauran securities din gidan da duka sauran ahalin gidan maza da maaikata kowa tini ya fito suka ringa shiga ruwan suna jiqa kansu da tsananin sauri suna zuwa da gudun gaske su banki kofar wadda ta kulle ko motsawa batayi amma sbd yanda wannan nayi ya koma baya wannan yazo da gudu ya banka shima haka suka ringa yi hankali tashe da tsananin karfi ga wutar sai qara yawa takeyi imran yi yakeyi yana ihun kada a kuskura a saki Fleet da Dad wanda karfinsa shima baiyi qasa ba ko kadan bai dena tsananin haukan son kwacewaba.

Samad ma bai dena kokarin fadawa ba cikin tsananin haukar data juyar da kansa bayaji baya ganin komai hakama hajiyarsa ihu takeyi suna qin sakinsa tana neman zarewa sbd wutar ta qarasa zafafan gaske zafinta jinsa sukeyi sosai suna wani zufan daya saka suke kasa riqe samad din da kyau ihunta da haukacewan datake yi shi ya sake saka yanayin cikin mummunan rikicewa da tashin hankalin daya fiddo Umma hankali tashe ta iso jikinta na rawa taga yanda wutar ke ciki ta juya da sauri ta kalli inda Dad yake yana rasa kansa da manta shi waye gabaki daya wuyar yake son shiga sbd wadda take ciki data fi masa rayuwarsa.

Jin tayi kanta ya sara yana mata wani mugun nauyi har saida jiri ya dan debeta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa muryansa harta fara toshewa sbd karfin yanda yake kiran sunan Dr fammah din wadda acan ciki dikkaninsu sun fito cikin tashin hankali daga dakunansu sbd hayaqi da wani irin zafin daya saka jikinsu wata mummunan zufa take fitarwa kaman ruwan sama sbd azabar zafin wutar.

A palo suka hade hankalin kowannensu a tashe suna kasa isa kowace kofa sbd wutar tariga ta shigo ta zagaye koina.

Dr Mum ce ta riqe SANAAH wadda Maamah ta kamo ta fito da ita jikinta na tsananin rawa hakama ko gani sosai basayi ga karfinsu dayake neman qarewa sbd tari da hayaqin dayake shiga huhunsu zamewa SANAAH tayi a gurin ta yanke jiki ta fadi sbd batada lafiya daman sai ita tafara fara somewa.

Mommy ma fara kasa jan numfashi tayi ta durqushe a gurin tana dafe kirjinta jikinta na kakkarwa
Kafin dukkaninsu su qara shiga mummunan tsoro da tashin hankali Maamah ma zubewa tayi a gurin Dr mum datai kokarin kama dukansu karfinta kasawa yayi itama ta zube gurin tana dafa kowannensu da girgizawa tana ambatar sunansu tafara tari sosai bata ganin komai sbd hayaqi da wani irin azababben zafi,

kofar da ake bugowa da tsananin karfi da tashin hankali ya fara sauka kunnenta ta dan daga idanuwanta ta kalli gurin duk da bata ganin komai ta motsa tanason isa gurin kofar duk da akwai wuta sosai amma ta kasa motsa koda hannunta tana kokarin somewan itama.
Chapter 122 · 0% Book details