Sashe 140
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rintse idanuwa yayi yana jin kalman na ratsa har kirjinsa da wani kaifi sbd baitaba iya karya ba bare ga mutumin dayake uba kuma uban daki a gurinsa basu taba yiwa juna boyo ba dan haka yayi shiru ya kasa furta kowace kalma sbd daga karshe dai fammah jeerah ta zama macen data yanke duk wata iyakarsa ta riqe kansa daga kowace macen.
Dad jin shirunsa take yaji wani sanyi da nutsuwa sun saukar masa dan haka yayi masa sallama kawai yana saka kiran Fammah wadda kusan itama abun dayane son juna ne yake neman kashesu amma sun kasa yadda sbd kaucewa fitinar dake cikin hakan.
Kwana Dad jeerah yayi da maganarsu aransa wadda a yau din da zaa maida aurensa daa kusa suke babu abinda zai hanasa hadawa dasu a daura auren batareda shawara da uwarta ba wadda kowa ya sani bazata taba bari ayi auren ba dan haka sbd fidda kowa a cikin rikicin shi zaije da kansa italy ya fuskancesa matiqar suna son juna zai daura musu aure acan sedai ta dawo da auren a fuskanci uwarta da auren.
Da wannan ya bar maganarsu har suka iso Nigeria,
Koda suka iso Umma na asibiti antafi da ita ciwo ya taso mata sosai na hawan jini a daren dan haka bayan isowansu da tsakar dare sosai ne sosai kowa bangarensa ya nufa da sassafe kuwa Dad asibiti ya tafi da Mr Sideeq dubo Umman wadda tayi nisa sosai dan sosai takejin jikin.
Shi kansa ganin yanayinta damuwa sosai ya shiga ya jima a asibitin harma saida ta farka suka gaisa ya mata ya jiki daga nan tayi karfin halin tayasa murnan aurensa da aka mayar da adduar fatan alkhairi ga auren yayi mata godia yana hanata doguwan maganar datake kokarin fada akan cewan sbd aurenta suka rabu gashi yanxu Allah yayi taga sun maida aurensu wannan nauyin ya sauka akanta.
Murmushi kawai yayi mata na bata fatan samun lafiya kawai.
Sai yamma sosai ya koma gida a lokacin ma su Dr Mum bata saniba sbd tana bangarenta tareda SANAAH wadda anan take tareda ita sbd su maamah da mommy suna bangaren Meenah datake cikin tsananin karfin halin iya tarbansu musamman ganin da SANAAH aka dawo wadda kallo daya mata taji haukarta na neman kuncewa sbd tsananin balai da masifar datakejin tana cin jininta.
Fleet kuwa bangarensa ya sauka kai tsaye wanda baima tsaya neman Meenah dinba wadda haryanxu bayajin yanada time din magana da ita akan laifinta da bazai taba iya yafewa na sakawa iyayensa da daya ta haifesa daya ta shayar dashi wuta.
SANAAH kuwa tinda suka dawon itama ta sauke idanuwanta akan meenah taji wani nauyi da zafin jiki ya rufeta mai tsanani sbd sanin yanzu dole kallan Fleet zatai da matarsa a kwanakin take taji inama bata dawo ba tayi zamanta a gurin fammah.
Ana magrib aka komai na abinci bangaren Dr mum da zaa kai bangaren Dad saiga waya daga asibiti Allah yayiwa Umma cikawa take gidan ya shiga wani irin tashin hankali da damuwa mai tsanani ta rashin wanda shi kansa Dad ya dokesa dan haka dole asibitin ya nufa tareda Mr Sideeq harma da Alh tsohonsu da shima rashin ya shigesa.
#MAMUH
09033181070
[24/06, 10:28 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
139
Koda su Dr Mum suka samu labarin rasuwan Umma dukkaninsu jikinsu sanyi da tsananin tausayi da fatan Allah mata rahama da sadata da malaikun rahama sbd dai babu wanda ya taba ko sainsa da ita tanada boye abu a ranta da dannewa duk kuwa yanda zatajisa ko hajiyar Samad duk fitinarta tin suna da kuruciya ma Umman bata biye mata sbd gabaki daya rayuwar auren tasu su dukan a rikice take batareda sunsaniba sbd wanda suke auren ruhinsa bai taba zama a gurinsu ba kawai aure yakeyi dan cika sunnar maaiki amma zuciyar da ruhin basa nan.
Ita Dr mum ma da ba saninta tayi ba kwata kwata tinda bata taba zama da ita ba kawai a yanxu ne dan zuwan nan datai take dan ganinta a bangaren Hakeem shima bawani riqe kamanninta taiba sbd basa wani kallan juna dan haka batasan komai akanta ba bayan cewan itace matar Hakeem kadai dayake tareda ita.
Numfashi ta sauke ahankali da sanyin jiki tareda tausayin Hakeem din wanda ya rasa matarsa dan haka batai bacci ba kusan itama a zaune ta kwana sbd sanin Dad din yana can asibitin cikin damuwan da bama zai iya dawowa gidan ba saida safe kila.
A daren ma dole haka duk me wani damuwa ko tashin hankali ya saurara sbd rashin wanda akai dan anjima baayi rashina a jeerahs din dan haka koina yayi tsit.
Meenah ma duk yanda taso tada tashin hankali da balai dole badan taso ba tai shiru ta lafe a bangarenta dan taje bangaren Fleet ta tadda yana asibiti tareda mahaifinsa dan haka ta koma bangarenta duk taso ace ta tadda SANAAH a bangaren da wlh sedai tayi prison amma sai anyi janaizarta da Ummah a washe garin tare.
Ita SANAAH ma da dan zazzabi ta kwana sbd damuwa da wannan tashin hankalin da suka shiga dan haka tana daki bata fito ba haka suka kwana tinda sassafe saiga gawan andawo gida da ita zuwa bangarenta wanda yan uwanta tini suka iso suna ciki ana kukan wannan rashin daya zo katsam.
Su Dr Mum basu fito ba suna can suna tausayawa har lokacin janaizar yayi wato karfe tara na safe aka gama aka kaita kowa ya dawo.
A lokacin ne Dr Mum ta fito tareda SANAAH wadda take gefenta cikin doguwar hijabinta har qasa suka shiga har bangaren umman sukai gaisuwa da mata fatan rahama suka fito daidai nan su Maamah suma suka shigo sukai suka fito.
Meenah da Hajiyar samad basu shiga ba sai kusan yamma atare sukaje sukai suka fito.
Dr Mum bayan fitowansu bangaren Dad suka wuce gabaki dayansu harda su maamah sbd baa zaman gaisuwa sam a jeerahs din.
Koda suka isa Mr Sideeq ne kadai sai Fleet wanda shima fitowa zaiyi ya wuce bangarensa sbd daga janazah din yana nan tareda Dad din.
Suna sako kai SANAAH ce a gaba wanda idanuwanta har sun fada sbd rashin baccin da bataiba da yunwar data tashi da ita ga abincin ma ta kasa iya ci yanda ya kamata.
Dago idanuwanta tayi ahankali jin kamshinsa daya shiga hancinta ta tabbatarda yana palon dan haka bata qarasa dagowa da idanuwanta ba dan kada ma ta gansa ta maida kasa tana qarasa shigowa palon tana nufar gurin Dad dayake zaune ya dago kansa da idanuwansa ya sauke akansu daidai zaunawan SANAAH qasa da bayyanar Dr Mum a bayanta wadda ta dago idanuwanta da sukai sanyi itama da tausayinsa na damuwan datasan dole yana ciki na rashin macen da sukai zaman auren shekaru masu yawa wanda tasan ita bazata samu wainnan shekarun dashi ba.
Akanta ya tsayar da idanuwansa ahankali cikin nutsuwa yana kallanta da sauke ajiyan zuciya mai sanyi da jin nauyin dayake danne da kirjinsa ya dan ragu sbd kansa ma tsananin ciwo yake masa.
Itama shi din take kalla da dukkanin kulawa da kauna da jin radadinsa ta qaraso a natse ta zauna akan kujeran dake facing dinsa tana dan dauke idanuwanta daga nasa tana sauke numfashi a boye kafin ta dago ta kallesa tana bude baki tai masa gaisuwa da yiwa umman addua.
Su maamah ma gaisuwan sukai masa da mommy kafin SANAAH tayi masa daga karshe tana dan dagowa ahankali ta kalli inda take ganin hasken kafafun mijinta ta kalli gurin cikin sanyin dayaji a jikinsa bata daidai ya sauke mata nasa idanuwan da sukai wani iri suma sbd rashin bacci da halinda aka shiga din.
Kallanta yayi da wata nutsuwa a taqaice yana dauke idanuwansa daga gareta zuwa ga iyayensa mata yana gaidasu sukai masa gaisuwan rasuwan shima tukuna suka miqe dukansu suka fice banda Dr Mum wadda bayan ficewan kowa dagowa tayi ahankali ta kalli Dad din shima ita ya kalla yana kasa cewa komai.
Shiru tayi tsawon mintina kafin ta miqe tana cewa zata kawo masa breakfast yaci ko yayane.
Dan numfashi kadai ya sauke bai iya cewa komaiba har lokacin ta miqe ta fice ya bita da kallo.
Bata jimaba ta dawo da breakfast jere a tray babba da safiya ta biyota dashi har palon ta karba ta ajiye gabansa safiya ta gaidasa da masa gaisuwa ta fice.
Da kanta ta hada masa komai tana zaunawa ahankali kusa dashi tareda miqa masa ya amsa ahankali yana dan bude bakinsa a natse yace
"Thank you likita"
Murmushin karfin hali ta sake masa tana dan basa qwarin gwiwa.
Ta jima sosai a gurinsa kafin ta baro ta fito ta koma sbd baqin dake son ganinsa a can palon waje dan masa gaisuwa.
SANAAH ma tana komawa daki a waya Fleet ya kirata yana kasa cewa komai sai ajiyan zuciyan daya sauke tukuna yace yaya take yaya ta kwana?
Numfashi mara karfi ta sake tanajin duk batama jin dadi ko kadan tace
"I'm missing you already"
Numfashi ya sake mai sanyi yana bude idanuwansa da sukai nauyi yana jin dole afara aikin bangarenta itama da gaggawa sbd bazai iya wannan zaman ba tana bangaren Dr Mum yana buqatan bangarenta a matsayin matarsa da zai ringa kasancewa da ita a duk lokacinda sukaso babu kowace shamaki.
Sunanta ya bude baki ya ambata da wani sauti mara hayaniya da karfi sosai mai cikeda sanyi da nutsuwa har saida tsigar jikinta ta tashi ahankali ta dan lumshe idanuwanta tana jinsa yana furta mata kalaman da suka sanyata jin idanuwanta na cikowa da hawayen kishinsa da kewansa.
Sun jima a wayar suna magana wadda saisun share seconds ko mintina baace komaiba kafin ayi magana ahankali ataqaice har lokaci sosai tukuna sukai sallama suka kashe.
Wanka yayi yayi ya fita sallan azahar yana dawowa ya kwanta baccin da baisamu daman yiba dan hutawa da kyau.