← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 154

Sashe 58

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
Suna shigowa bedroom din mai girma sosai da shima komai na tsarinsa irin na yanda Ms Meenah din zata iya rayuwa ne irin wadda ta saba da ita ta turai da jin dadi da rashin hayaniya cak SANAAH ta tsaya a tsakiyar dakin tana kasa motsawa tareda dagowa idanuwanta cikin slow ta saukesu akan Mum wadda itama ta dakata daga zaman datake kokarin yi tana zare nadin veil din abayar dake nade akanta tana sauke nata idanuwan akan SANAAH wadda taji tana kasa isa gareta sbd jin nauyi da kallanta a matsayin mai laifi mai girma a gabanta.

Tasowa Mum din tayi tana nufo SANAAH tareda kasa dauke idanuwanta akanta tanajin kirjinta yayi nauyi da kuma mamakin irin yanda SANAAH din take a zahiri sbd komai nata a zahiri daban yake da kyansa da ajinsa da tsantsar tsaftarta da kafafunta da hannunta kadai da duke qal zai tabbatar maka da hakan taja wani numfashi mai nauyi ta fitar ta bude baki murmushin na mamaye fuskanta da farin cikin ganinta ta washe baki tana dan ware Hannuwanta ta iso ta rungume SANAAH din tana cewa

"Masha Allah yau dai gani ga Baby SANAAH,my babies nayi kewan ganinku a gabana musamman ke da ban taba gani a zahiri ba i love you girls"

Numfashi mara sauti SANAAH ta sake tana jin nauyinta na sake shigarta ta daure ga rungumeta tana bude baki tace

"Mum sannu da isowa muma munyi murnan isowanki" ta qarasa maganar da murmushi tana juyawa ta kalli fammah wadda farin cikinta yake karuwa sbd daman tanason Mum da SANAAH su samu shaquwa da kauna me karfi irin wadda takeda ita da Mommy sbd tabbas idan zasu tafi da SANAAH takeson su tafi America itama.

Ahankali qamshin turaren fleet da ko a haukace take bazata taba kuskuren jinsa ba taji kaman yana fitowa Ahankali daga cikin SANAAH sama sama yana shiga hancinta ta dan dagota tana kokarin basarwa sbd ta tabbatarda irin qamshin ne dan ko a hauka bazata taba kawo kamshinsa ba a jikin wani guri bare SANAAH dayake tamkar yarsu da suka haifa ko dan sbd fammah kuma gata babyn Nasir dan haka ta sake jin dadin ganinta ta saketa tana tambayarsu mommy sukace bata ma tashi ba so batasan sun isoba.

SANAAH silalewa tayi daga nan ta koma da cewan zata je ta duba aikin Safiya,

Tana baro bangaren taji kaman ta fito daga kurkuku dan haka tana tafiya tana sauke ajiyan zuciya da jin nauyin da kanta yayi yana ragewa.

Tana isa bangarensu ko kitchen bata leqa ba ta wuce bedroom dinsu.

Cire kayan jikinta tayi da kamshinsu ya sauya mata sbd debo kamshin da sukai nasa ta fada toilet tayo wanka tana fitowa cikin kayan shan iska ta shirya ta fito ta nufi kitchen da safiya take kokarin kammala komai harma ta jera wasu a inda zata tura takai.

Sama sama ta danyi breakfast a kitchen din ta koma dakinta ta kwantawanta take wani baccin da bata samu yiba ya dauketa.

Koda fammah ta baro bangaren iyayenta barinsu tayi su huta sbd zasu gama komai ne da wanka su kwanta su huta yanda ya kamata da baccin da basu wani samuna tukuna suyi breakfast idan sun tashi.

Ko data zo baa gama aikinba dan haka itama a kitchen din taci abincin sama sama tukuna ta wuce dakin Mommy wadda ta gama shirinta kenan dan batama fitowa daga bedroom dinta sai tayi wankanta ta shirya fes tukuna.

Gaidata tayi tareda hayewa gadon mommyn babu jimawa bacci mai nauyi ya dauketa itama.

Qara mata ac mommy tayi tareda rufa ta kashe mata hasken dakin ta juya ta fice tana daukan wayarta dake ringing Al'amin ne yake kiran.

Karfe sha daya da kusan rabi dukkaninsu suka tashi Fammah ce tafara tashi taxo dakinsu ta tube ta shiga wanka tana fitowa motsinta ya saka SANAAH tashi itama ta bude idanuwanta ahankali ta dorasu akan fammah din wadda babu kowace shakka kyakkyawace datake da asalin zallan kyau na sirkin jinin Larabawan Morocco dana Hausa fulanin Nigeria duk da babu abinda zata nuna mata a kyau da kyan fata da lafiyayyar fatar hutu da fizgan hankali dan ma kuwa tafita tudu da cikar kirji duk da kusan komai na jikinsu daya ne dan size kusan daya ma suke amfani dashi tafiya da lamba bibbiyu ne a sama da qasa amma tsawonsu kusan daya ne daidai amma ayau tana kura mata ido ne da kallan zallan kyanta da ayau idanuwanta suka ga asalin inda ta debo kamanninta da babu abinda ta baro na Dad dinta data ke ganin idanuwansa cikin nata har lokacin tanajin dana sani da takaicin zuwan datai bangaren kwata kwata.

Fammah data lura da yanda SANAAH take kwance jiki a mace ta zuba mata ido da alaman tsananin kaunarta gareta tasowa tayi tana dauko kayan da zata saka tana cewa

"Yaya dai Baby SANAAH"

Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda girgiza kai batareda ta bude baki tayi magana ba tukuna ta tashi zaune tana dauke idanuwanta daga kallan fammah din ta sauko daga gadon ta nufa bathroom ta shige.

Sake brush da wani wankan tayi da ruwan dumi sosai ta fito daure da qaramin towel ta nufo gaban mirror ta xauna tana dan fara shirinta.

Fammah kuwa ficewa tayi dan umartan safiya ta dauki sauran kayan breakfast din sukai sbd zuwa yanzu tasan sun tashi.

Tana isa kuwa Mum dinta ta tashi harma tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwan riga mai kyau da dan mayafinta dan haka kai tsaye fitowa sukai dining sai a lokacin ta nufi hanyar data fahimci itace hanyar master bedroom din mijinta ta ratsa hanyar qamshinsa na tashi kadan kadan a hanyar alaman dai hanyar tasa ce.

Ko data isa tana bude kofar ta shiga palonsa ta lumshe idanuwanta tana shaqar qamshinsa daya dan fi yawa kadan anan ta doshi kofar bedroom dinsa tana isa kafin ta bude ya bude kofar a tsanake sai gashi ya bayyana gabanta sanye da doguwar jallabiyar maza mara kowace irin ado ko zane plain Off white data nutsu a gangar jikinsa da fatar jikinsa da kuma tsayawa daidai jikinsa sbd batai masa fadi ma duk da a sake take hakama har qasa take sosai daidai yanda ya kamata bata daukeba tako ina.

Kasa iya riqe kanta tayi ta qara taku biyu ta saka hannuwanta ta shige jikinsa ahakali tana zagayosa da hannuwanta tareda sauke ajiyan zuciya tana shaqarsa dan shaqarsa a gunta kaman daily routine ne da idan bataiba takejin kaman batada isashiyar oxygen tsaban yanda takejinsa.

Dan shafa kanta yayi ahankali yana janyeta daga jikin nasa ya kama hannunta suka nufi kofa yana bude baki da sautinsa mai ratsa kunnuwa yace

"Yaya kika fara jin Nigeria for now??

Murmushi tayi tana yar dariya tace

"A yanzu dai ina jina am ok da komai da kuma qasar da gidan"

Dan juyowa yayi ya kalleta da idanuwansa yana dan sake murmushi mai kyau baice komaiba.

Suna fitowa Fammah data fito daga kitchen ta hanyar dining room din palon ta qarasa jera abubuwan buqata a table din sake qaraso tayi tana nufar Dad dinta wanda y sake hannun Mum dinta kai tsaye a natse yana miqa mata ta kama tana gaidasa da sake mata sannu da zuwa cikeda kulawa.

Dining din suka hau su dikansu hadda fammah din wadda itace tayi serving nasu da kalan abincin datasan zasu iya ci sosai su koshi musamman mum dinta da kwata kwata kalan cimarta daban bata saba da abincin Nigeria ba kwata kwata.

Sunyi breakfast din suna gamawa suka baro daidai lokacin ne hajiyar Samad ta shigo palon tareda yan aikin bangarenta guda biyu dake dauke da basket biyu na abincin data saka akai musu itama.

Allah yasa bai shigeba dan haka ya dan dakata suka gaisa batareda ya juyo ba dan baya wani kallansu ko iya samun sakewa da matan mahaifin nasa dan har gwara ita hajiyar Samad din yana ganeta kai tsaye amma Umma bai iya tantance kamanninta sbd babu kowace alaqar datake tsakaninsu bayan gaisuwa kawai.

Suna gama gaisawa tanata neman sake cusa kai da maganar Samad bai biyosa ba ya bata amsar yana wani aiki ne a taqaice tukuna yayi mata godiya datake dabiarsa ya fice ya shige hanyar da zata kaisa palonsa yabarta nan gurin su fammah.

Fammah ta kalla tukuna ta maida kallanta kan Mum din baki a washe da nuna farin cikin zuwansu tace

"Fammah Mum din taki da ita aka iso kenan?
Dazu tinda safe Samad ya kirani ya sanar dani ai sun sauka Nigeria ba shiri nace maza a tashi ahau aikim abincin da zasu ci idan sun iso"

Da murmushi babu wata nuna wulaqantawa saidai kamewan rashin sabo sosai tace

"Yes da Mum aka taho gatanan zaune"

Kallan mum din datake kallan Hajiyan da rashin sani kwata kwata tayi tace

"Mum hajiyan Uncle Samad ne,i mean his mum"

"Oh ok yes" ta fada tana sake fuskanta sosai da murmushi mai kyau tana kallan hajiyan tace

"Mun sameku lfy"

Hajiya na ganin hakan taji farin ciki ta sake sakewa tana cewa

"Lafiya kalau alhmdllh,ya hanya?
Ya America or Morocco zance?" Ta qarasa maganar da yar dariyar sakewa tana kallan Ms Meenah din da kyau wadda itama ba mummuna bace da kyanta sosai duk da tanda zuqeqiyar budurwa gabanta amma bata rasa kyanta da kyan jikinta ba.

Abincin Hajiyar tace akai dining a jera Mum da batasan me zasu ce ba tinda sunci abinci batareda tinanin ana dan kara ba tace

"No no ba buqatan hakan mun riga munci abinci kada a aje mayar ko wani zaici acan,thank you so much"

Wani abu hajiyan ta hadiye na takaici tana kallan bakin Ms Meenah din da jin kaman ta mayar mata da thank you dinta dan takaici amma sai ta washe baki a fili tana cewa

"Ok ba damuwa ashe harkunci abinci,
Ku maida sai anjima ko gobe da sassafe a sake musu wani"
Chapter 58 · 0% Book details