← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 154

Sashe 41

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****Da daddare yau bayan takai masa tea Nasiha mai bada nutsuwan datake rasawa Dad din yayi mata ta kuma samu nutsuwan sosai ta fito jiki a mace ta nufi bangarensu.

Shiru koina sai haske koina da security cameras dake daukan koina a hanyoyin gidan.

Tafe take tana tinanin yanda zataci gaba da rayuwa a cikin tsoro da shakkar Samad har takusa isa bangarensu taji an fizgota baya da karfi tareda rufe bakinta ruf ya dagata sama ya juya da ita.

Bata taba shiga mafi girman tsoro da firgici tareda ficewa hayyacinta lokaci dayaba sai lokacin dan haka ta fara wata irin fizga da karfi tana kokarin kwacewa da neman bude bakinta amma kwanjin gaske na zamowansa kakkarfan namiji ya bude mata gabaki daya yana tafiya da ita.

Bangarensa dayake can nesa gefe daban ya nufa da ita tin bai qarasa isa ba ya saka bakinsa ya kama rigar jikinta ya fizgo da karfin gaske ta yage daga saman tana dan bayyanar da saman kirjinta dan haka ta saka karfin da batajin ma tasan nata ta fizge da karfi tareda kwallara wani irin ihun mai karfin gaske daya ratsa wasu gurare na gidan.

Damqota ya sake yi da karfi tareda shaqeta da karfi yana danneta jikin kofar palonsa dayake kokarin budewa ya kasa dan haka tin anan ya qara saka hannu ya qarasa yaga rigar jikinta yana bugata jikin kofar da karfi hannuwansa na rawa ya qarasa bude kofar yayi ciki da ita wanda yayi daidai da biyowan Safiya ta hanyar zata wuce bangarensu na masu aiki taga abinda yake faruwa da gudu ta juya ta koma ta sanar da mommy jikinta na rawa sosai dan itama tsoro taji duk ya rufeta.
#MAMUH
09033181070
[01/05, 12:00 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

40
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Mommy da zancen ya daki kirjinta da mummunan karfin gaske kasa tashi tayi daga zaunen datake idanuwanta suka fara nauyi dakyau ta iya bude baki ta safiya tace ta sanar da Dad.

A rikice safiya ta fice tana kama hanyar da tinda take aiki a jeerahs bata taba xuwaba sbd baa barinsu zuwa can bangaren da wani babban bangaren da shima babu ma wanda ya taba zuwa ance na dayan 'dan Dad dinne wanda baya qasar tsawon shekaru.

Safiya bata samu isa bangarenba sbd batama san ina zata bi ba sai kawai tayi bangaren hajiyar Samad din hankali tashe tana kaiwa Hajiyar na fitowa da waya a hannunta kaman ta sani zata nufi bangarensa sbd sai ayau taji hukuncin da Dad ya yanke masa dan haka take cikin tashin hankali itama.

Safiya na ganinta ta bude baki cikin rikicewa tace

"SANAAH ce Sir Samad ya tafi da ita mommy tace na sanarwa Dad.....

Hajiyar data ji saukan zancen kaman saukowar aradu ture Safiya din tayi da karfin gaske tana jifa da wayarta tayi bangaren nasa da tsananin sauri da gudu gudu sbd balai da masifar da zai janyo musu idan yayi nasarar bata SANAAH ta sani har aurenta ya qare kenan har mahadi ya bayyana.

Safiya ma bayanta tabi da gudu sai kuma ta fasa ganin ba dad zaa sanarwa sai tayi bangaren Umma wadda take zaune a natse a palonta tana kallan wani shirin sharia da akeyi a tv na black Americans.

Mai aikin bangaren ce ta budewa safiya kofar datake bugawa.

Iso tayi mata har gurin umman wadda ta juyo ta kalleta da dan mamakin ganin mai aikin Mommy a lokacin.

Da tsoro Safiya tafara wa Umman bayani tana jin kaman ma Samad ya gama lalata SANAAH idanuwanta cikeda hawaye.

Umma tasowa tayi da bayanta daga jikin kujera tana jin mamaki da fargaba itama me tsanani na abinda zai biyo bayan wannan balain na Samad daya debo dan haka wayarta ta dauka tana son saka kiran Dad amma sai ta fasa ta miqe tsaye kawai tayi bangarensa da sauri.

Koda ta isa yana zaune shiru yana shan tea din sa SANAAH ta kawo masa babu inda inda ta sanar masa da abinda safiyar tazo ta fada mata.

*********Koda Hajiyar Samad ta isa yanata kokarin qarasa yaga kayan jikin SANAAH din tareda shaqeta tana neman ceton rayuwarta data mutuncinta,

Kusan zarewa zanin jikin hajiyar ya kusa yi ya fadi sbd mugun firgitan datai tayi kansa da sauri kafafunta na hardewa tsabar rawa ta damqosa da karfi tana kiran sunansa da karfin gaske.

Bayaji baya gani idonsa ya rufe SANAAH kawai yake buqata a lokacin dan haka ya kasa sakinta yana cigaba da damqota jikinsa.

Ihu hajiya ke son yi tsanar rikicewa amma ta kasa dan haka ta cakumo da da karfin gaske tana dagosa ta ware hannuwanta ta sauke masa wani mahaukacin marin daya sakasa zubewa qasa akan gwiwowinsa ta sake daga hannu ta saukar masa da wani tareda cakumosa ta ture gefe tayi kan SANAAH din hannuwanta na rawa ta cire mayafin jikinta ta rufawa SANAAH din tana janyeta daga qasa a rikice tana cewa

"SANAAH karki bari kowa yaji ya sani zan masa hukuncin,kada kiyi kuka,kada ki bari Dad ya sani,kada ki bari a sani martabarki zata tabu kinji,
Kada ki fada abinda Samad din yayi zaki rasa mutuncinki zaki rasa......

Bata qarasa ba SANAAH datake wata jijjiga ta zube a gurin Some numfashi bata fita daga kirjinta...

Hannuwa biyu hajiyar ta saka ta cakumota tana bude baki da sabon tashin hankali ta ambaci sunanta daidai nan Dad da kansa ya sako kai palon tareda Umma wanda tayi kan SANAAH da tashin hankali itada Safiya da mommy wanda kallo daya tayiwa SANAAH ta zube musu itama.

Ajiyan zuciya da numfashin da sautin fitarsa kadai ya saka Hajiya zubewa qasa gabansa tana fasa kukan da batasan ma ta fasa bai mai tsananin gaske.

Umma da safiya ne sukai ta SANAAH da mommy wainda aka kwasha aka fice dasu,

Kallo daya yayiwa Hajiyar batareda ya kalli Samad ba ya juya ya fuce da idanuwansa jajir wainda yaketa danne zuciyarsa daga zama makashin datake ingizashi.

Bangarensu aka koma dasu tareda kiran likitoci da gaggawa suka iso cikin daren.

Abinda aka fara dubawa da tabbatarwa shine babu abinda ya faru da SANAAH din dan haka Umma ta fito taje ta sanarwa Dad wanda yake zaune shiru komai nasa na fidda hucin bacin rai mai tsananin gaske.

Mommy kuwa shock ta samu daya bata attack dan haka tayi laushi lokaci daya..

Dad bai rintsa ba daren har garin Allah ya waye yana zaune yana jin abinda bai taba ji ba na tsananin bacin rai tin bayan na rabuwarsa da fammah idan aka cire na rashin rayukan da suka dan yi na iyaye da yan uwa.

Duk abinda Samad yakeyi yana danne daci da fushinsa ne sbd a yanxu kaman shi kadaine 'dan dayake dashi amma kuma ayanzu yakai karshen girman bacin ransa dan haka koda gari ya waye Abu na farko daya fara yankewa shine aurar da SANAAH ga wanda yasan ko hauka zata kashesa bazai taba gangancin ko sake kallanta a matsayin macen daya taba so ba bare,
Zai aurar da ita ga wanda ko bayan ya rasu aurenta garesa zai zama haramun bare mallakarta,
Zai aurar da ita ga wanda babu me sake ce masa komai ko saka masa ido zaa barsa a barta da kansa zai gudu yabarta,
Zai aurar da ita ga wanda yake uba a garesa kuma uban da bai taba hada girmansa da darajarsa da komaiba rayuwarsa hakan shine karshen nisa da kariyar dazai bawa SANAAH da ko baya duniya ta riga tayi nisa daga sharrin kowane namiji..

Baice komaiba kuma baida niyar cewa Samad da mahaifiyarsa komai sbd ya gama dasu ya gama ciresu daga cikin zuriarsa babu shi babu su dan haka koda ya kwana da wannan hukuncin nasa mai zafi asubar fari Al'amin ya kira bai ce masa komai daya faru ba ya sanar dashi zai aurar da SANAAH ga babban dansa FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH.

Shiru Al'amin yayi sbd zuwa yanzu baida kowane irin zabi akan SANAAH yabarwa Dad din duk abinda ya yanke akanta shi mai biyayya ne da fatan alkhairi dan haka yace ya amince Allah ya sanya alkhairi a auren.

Ajiyan zuciya da wani sanyi da nauyin dayake kirjinsa na shekaru ne yaji ya sauka a cikin sanyi sbd daga karshe dai bayan bawa SANAAH rayuwar da zata samu kariya da aminci shima lokacin da dansa zai dawo garesa yayi hakama da auren wadda Dr fammah bazata taba iya daga ido ta zabi rabasa ba koda rashin son hakan zai rabata da duniya da numfashinta.
Chapter 41 · 0% Book details