← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 154

Sashe 51

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko data isa a natse cikin kulawa da saa shi kadai ne kaman yanda suka saba dan haka taji sanyi ta sauke ajiyan zuciya a boye tana bayyanarda murmushinta ta zauna a qasa tana gaidasa cikeda kulawa da kewan kwana biyu.

Amsawa yayi yana cewa

"My future chairman ta jeerahs tana gudun babanta kwana biyu sbd karatu"

Murmushi tayi mai kyau tana cewa

"Dad yau ai na kasa nataho"

"Yaya exams naku to?

"Alhmdllh,ina buqatan qarin adduarku dai"

Fira sukayi saiga Umma tashigo itama ta qaraso ta zauna kusa da Dad din tana kallan SANAAH wadda ta dago tana gaidata cikin girmamawa a sake ta amsa tana kallanta da sakewan itama harda tambayar mommynta da Fammah.

Tea din ta miqa hannu zata zuba masa dan ta tafi tinda Umma tazo.

Dakatar da ita yayi kai tsaye da cewa

"Karki zuba yau bana buqata ki kaiwa Fleet jeerah nasan zaifi buqatansa"

Shiru tayi tareda dan dagowa a slow sbd kaman bata gama gane wa yake nufi ba hakama bakinta ya kasa budewa yayi tambayar datake ganin kaman rashin Daa ce tayi ta dan haka ta maida kallanta akan Umma wadda ta washe baki tana cewa

"Maigidanki fa ake magana"
Ki tashi ki kai masa can bangarensa"

Kasa maida kallanta tayi kan Dad sbd jin yanayin yayi mata dum kanta ya sara da karfi har saida ta dan lumshe idanuwanta ta bude ta rasa abinyi ko fada ta sauke wata sanyayyar numfashi mara sauti tareda bayyanarda karfin hali ta miqa tana daukan tray din ta fice Dad ya saka mata albarka yace ta tafi.

Duk takunta daya kaman ta dauko dala ba gammo take jinsa harta fice.

Bayan ta fito iska ta dan dakata ta shaqa a natse tana jin bata buqatan bawa kanta kowace irin wuya akan auren wanda bata sansa ba baisanta hakama kaman yanda komai na auren baya gabanta tasan hakanne a gurinsa tinda yanada iyalinsa dayake so hakama itama bata buqatan rayuwa a gurinda baa buqatanta sam koma zaa mata kallan baquwa a cikinsu ko bare.

Numfashi ta kuma fitarwa hankalinta a kwance batareda jin komaiba ta nufi bangaren da bata taba zuwaba dan kuwa komai yanda suke da fammah bata taba rakata gaida Dad dintaba hakama sbd wani irin matsayi da girman da Dad dinta yake dashi a gurinta da rayuwanta ya saka ko baya ganinta bazata iya saba umarninsa ba ya saka kai tsaye ta tafin.

Ko data isa bangaren tsit hanyar babu kowa sai securities dinsa biyu dake gadin hanyar gurin suna ganinta suka kira Imran a waya dan sanar dashi daidai lokacin shima Dad ya kirasa da kansa ya sanar masa wacece SANAAH din dan haka kai tsaye yace su barta ta wuce.

Ko data iso basu tsaida ta ba hanya suka bata cikeda girmamawa ta wuce ta isa kofar kafin ta miqa hannunta zatai knocking imran daya iso ya rigata isar da hannunsa ya bude mata da kulawa da girmamawa mai girma yana kasa mata cikakken kallo na rashin Daa yana danne dukkanin mamakinsa na ganin yarinyar datake daidai fammah a matsayin matar da aka daurawa aure da Fleet da kansa.

"Thank you" ta bude bakinta a tsanake ta furta masa tana daga kafarta cikin nutsuwa ta saka a cikin palon wanda niimtaccen kamshinsa ya daki fuskanta ta dan dago fuskanta ta kalli cikin palon wanda yake tsit tsarinsa da kalar datake palon yake na turawan da basa son hayaniya.

Imran daga waje rife kofar yayi yana barin gurin ita kuwa saida ta dan yi seconds a gurin tsaye kafin ta hangi hanyar Dining dan haka ta daga kafafunta ta nufi gurin tana isa ta ajiye tray din hannunta bata tsaya komaiba kawai ta juyo tareda saka kai kofar fitowa daga dining room din wanda yayi daidai da isowansa zai sako kai shima take suka kusan wata irin haduwan data sakata yin baya da wani irin karfi tana dago fararen idanuwanta a lokaci daya ta saukesu akan wanda yake gabanta fuskanta a kame ajinta da kamewanta na bayyana gabaki daya.

Akan kyakkyawar fuskarsa datake fidda wani irin hasken asalin kyau da kwarjini da wata irin kamewa da izza tareda girman da dole ka sadda kanka idan ka kallesa idanuwansa da suke da wani irin haske da saka faduwan gaba shima sun sauka akan fuskanta kai tsaye yana kallanta a karan farko na rayuwarsa kaman yanda itama karan farko kenan da idanuwanta masu kyau da girma suka sauka akansa.
##MAMUH
#HIS FIONA
#BEST LOVE
#AGE GAP LOVE
#CRAZY COUPLE CHEMISTRY
#FLEET RAHEEM JEERAH
#SANAAH KHALIL
#MEENAH WAHAB
#SAMAD JEERAH
#DR MUM
09033181070
[07/05, 10:06 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

49
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Kamshinsa ne ya rikida niimar gurin tareda shiga hancinta direct sbd yanda suke kusa wanda ya sakata dauke fararen idanuwanta daga kansa ahankali tana dan sake ja da baya cikin nutsuwa da sake dagowa a natse ta bude baki ta gaidasa sbd basa girman mahaifin Fammah cikin sauti mara hayaniya ko fitowa sosai.

Shima dauke nasa kallan yayi daga fuskanta datake kokarin bayyanar masa da kamannin da har abada bazai manta ba amma bazai iya mata kallan tsaf ba sbd kasancewanta yarinya sosai a gurinsa dan haka ya amsa gaisuwanta a taqaice tareda qarasa shigowa dining room din yana kallan table batareda ya sake kallan inda take ba itama data so fadan Dad ne ya aikota sbd clearing tinanin ganinta a nan amma ganin hakan sai kawai taji ma babu buqatan bayanin dan haka ta fice kawai bama tareda yaji ficewan nata ba sbd rashin hayaniyarta ko a gurin tafiya.

Tana fitowa daga bangaren taji ta sake cire lamarin auren kwata kwata daga zuciya da kanta dan haka ba damuwan komai ta isa bangarensu ta fada bedroom fammah dake waya da Mum dinta ta dago tana kallanta da kulawa tace tazo ta gaida da mum din.

Bataji komaiba cikin girmamawa ta dan bude bakinta ta gaidata a matsayin Mahaifiyar Fammah kuma itama kaman uwa a gareta.

Suna gama wayar karatunta suka fara yi da fammah suna shiga wata firar akan karatun bar lokaci yaja suka kwanta.

Washe gari Fammah dataje bangaren Dad dinta taga tray na teaset din da SANAAH take kaiwa Dad a kan dining din Mahaifinta tayi mamaki amma kuma sai tayi tinanin daga gurin Dad dinsa ya taho dasu sai ta tattara ta koma dasu bayan ta jere masa breakfast dinsa.

Bata jira ya fitoba sbd time na fitowansa baiyiba dan haka ta juya ta fice sbd tareda SANAAH zasu fita yau.

Tana komawa shiryawa tayi sukai breakfast a dining su biyu kawai sbd mommy ba yanzu zata fitoba itama.

Ficewa sukai da motan SANAAH zuwa school.

Exams din safe tayi tana fitowa suka sake shiga wata a jere daga nan ta gama ta ranar dan haka kai tsaye shopping din dazasu ke buqata suka wuce.

Siyayya sukai sosai ta abubuwansu na mata da kayan hausa da Fammah din take shaawa su atampa kawai batason lace tace zai dameta so laces din da suka siyo baifi guda uku ba suma masu tsadan gaske ba nauyi ba ado da yawa suka bayar fashion house a dinka suka zube makudan kudi suka dawo da sauran siyayyansu ta tarin undies dasu kayan shafarsu.

Fammah da daddare dataje gurin Dad dinta ta sanar masa siyayyan dinkin da zaayi mata tayi baice komaiba ya qara mata kudi sosai duk da yasan ba lallaiba ne tayi amfani da kayan tinda komawa zasuyi.

Kwana biyu tin daga ranar da SANAAH taje bangaren a bisa umarnin Dad bata sake zuwa gurinsa ba da daddare ta sauya da yamma take xuwa ta gaidasa ta dawowanta dan sam kwata kwata bata buqatan haduwa da mahaifin Fammah dan yanxu wata shaquwa da kusanci ne yake shiga tsakaninsu da bazata iya ma tina auren Dad din fammah ne akantaba.

Fammah ta saki jikinta sosai ta sabu dasu da samun nutsuwa da jin dadi sosai da farin cikin zama acikinsu sbd ta taso daga Dad dinda sai Mum dinta take rayuwa dasu a gida sai masu aikinsu da tsakaninta dasu umarni ne amma anan gashinan tana sakewa hadda safiya datake mai aiki fira da wasa da dariya sukeyi sosai da ita sbd abinda taga su SANAAH nayi da ita kenan,

Samun shaquwansu da kusancinsu dayake qara gaba sosai shine sbd dukansu su biyun babu me kowace kawa ko aminiya a rayuwarta,

SANAAH bata taba yin aminiya ko kawaba duka karatun datai iyakacinta da course mates nata mutunci shikenan hakama Fammah rayuwanta batada qawa ta musamman sai abokan karatunta itama,
Chapter 51 · 0% Book details