← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 154

Sashe 121

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu tsananin zafin gaske suka gangaro mata ta kife kanta tana kasa riqe kukanta tafara rero wani irin kuka mai tsananin gaske da ratsa zuciya tana jin kirjinta na tsananin zafin da bazata iya daukaba,

Mutane biyu datake tsananin so a rayuwanta meyasa zasu mata haka?
Meyasa Dad bazai fada mata SANAAH matarsa bace?
Meyasa SANAAH bata fada mata Dad dinta shine mijin da akete cewan tanada shi ba??
Yanzu tayaya zata iya kallansu bayan abinda sukaiwa Mum dinta da tafi jin radadin abinda Mum din ke ji wadda tasan bazata taba iya barin SANAAH ba saita rabata da duniya ko illatata.

Mommy data rasa abinyi ko fada tana jin irin kukan da fammah din keyi ga wani irin kunyar fammah din da kusan itama fammah din tafi kunya ta zauna gefenta tana dan dafata ahankali da bude baki tana bata hakuri da rarrashinta da wata irin kulawa da damuwa.

Har asuba suna cikin wannan mugun yanayin har sukai sallah suka zauna jigum jigum gari na qarasa wayewa fammah din ta fito a sanyaye tabar bangaren ta nufi bangaren mahaifiyarta tana fita suna dawowa da SANAAH din.

Ko data isa bangaren taji tsit babu motsin Mum kai tsaye dakinta ta nufa ta bude tajisa a rife ta kalli kofar sai taga key a jikin kofar ta waje dan haka da sauri ta bude key din tana budewa.

Mummunan faduwa gabanta yayi ganin halinda dakin yake ciki sbd babu abinda bata fasa ba ta buga da kasa.

Rawa jikin fammah ya fara ta shigo dakin gabaki daya tana jefa idanuwanta koina bataga Mum din ba zata juya a rikice futa nemanta taji anbude kofar bathroom din dakin ta juyo da sauri saiga Mum dinta fito idanuwanta da fuskanta sunyi wani irin jan da basu taba yiba ta zubawa fammah idanuwanta da suka sake fammah fara hawaye da sauri tareda tahowa da wani irin sauri ta rungumeta tana cewa

"Mum dan Allah kifi karfin zuciyarki kada ki illata kanki"

Ahankali ta daga hannuwanta da basuda karfin ta rungume fammah din wasu hawaye masu tsananin zafin gaske suna gangaro mata ta ja wani numfashi mai karfin gaske sbd yankewan da numfashinta ke son yi tin jiyan tana riqesa dan kaman ma attack takeson samu amma karfin halinta yaqi bari.
#MAMUH
09033181070
[16/06, 3:23 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

120
Janta fammah tayi suka fito dakin kaman mara gani komai na jikinta a sake yake batada kowane sauran tinaninta da hankalinta sbd ta kasa yadda itace mijinta fleet dinta yake kwana da wata macen bayan ita,
Itace Fleet dinta ya hada jiki da wata macen,
Itace Raheem din data gama tabbatarda nata ne ita daya har qarshen duniya yau cikinsa ya bayyana a jikin wata ba ita ba kuma wai yarinyar datake tareda ita a matsayin yarta da sanin kowa kuma.

Dakinsu fammah ta kaita ta zaunar a kan kujera tareda komawa dakinta ta dauko mata kayan sakawa ta kawo mata sbd ruwa ta sakowa kanta ta jiqa kanta gabaki daya.

Da taimakon fammah ta sauya mata kayan sbd komai nata bata iya motsawa da kanta,
Sallah fammah ta sakata yi wadda ta tabbatarda bata samu yinta ba tana idarwa suka zauna sukai shiru babu me iya cewa komai kowa ya sake shiga tinani mai zurfin gaske.

Mommy jin cikin SANAAH ya fita itama taji damuwa da sanyin jiki duk da ganin SANAAH din a kwance kaman babu sauki a tattare da ita haka ta tafi kitchen kusan tafi ma safiya dan karfin hali haka sukai aikin breakfast suka gama babu wanda ya fito breakfast din kowa yana daki tsit ba motsin komai kusan duka JEERAHsV dinma shiru tayi.

Sai guraren 11 na safe Maamah ta fito taje ta hado tea mai kaurin gaske ta kawowa SANAAH wadda ta farka amma bata motsaba daga kwancen ta bude idanuwanta wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga gefen fuskanta.

Tayar da ita zaune Maamah tayi tareda kamata ahankali zuwa toilet suna shiga ta hada mata ruwan wanka masu tsananin zafin gaske ta fito.

Batada karfi ko kadan harma da jiri jiri take gani dan haka ta ahankali ta shiga ruwan ta zauna tana sunkuyar da kanta kuka na zuwar mata mara sauti tana fara rerowa kirjinta a cunkushe.

Ta jima sosai a ciki kafin ya fito ta zauna ahankali safiya tana dakin ta kawo mata kayan sakawa sai kuma ga Maamah itama da tea da magani.

Bata iya shan tea din ba kadan ta dan sha aka bata magani tasha daidai nan Dr Mum ta shigo dakin dubata jikinta a matiqar sanyaye zuciyarta ba dadi sam ta kalli SANAAH din wadda itama ta kasa kallanta ta zauna gefenta tana dubata cikin kulawa da bata hakuri sosai akan abinda ya faru.

Bacci ta koma suka fice daga dakin ana gama sallar azahar dr mum da Maamah suka fice zuwa bangaren Meenah sbd ko fammah bata fitoba bare ita.

Suna ficewa shi kuma a daidai lokacin ya iya fitowa ya tinkaro bangaren ya shigo safiya na ganinsa da girmamawa sosai ta gaidasa ya amsa yana bude baki da wata muryansa datai kauri sosai babu rahama ko daya har lokacin a fuskansa ya tambaya inda SANAAH din take.

Dakin Maamah ta sanar dashi cikeda girmamawa bai kalletaba ya wuce dakin.

Koda ya shiga bacci takeyi dan haka ajiyan zuciyan da bai saukeba tinda ya sauka kasar ya sauke ahankali tareda zuba mata idanuwansa da suka fara sauyawa wata wutar radadi na taso masa yana jinta cikin jininsa amma bazaiwa Meenah din komaiba a yanxu zataci darajar yarsu da kuma laifin da akai mata duk da shi laifin zubar da cikin zaibi ta kansa ne daga lokacinda ya samu cikakken bayanin abinda ya faru tin daga farko sbd zai tabbatarda ta karbi hukuncin laifin nata.

Takowa yayi ahankali cikin nutsuwa da kamewansa data kame sosai sbd babu kowace walwala a tattare dashi.

Cikin nutsuwa ya zauna a sofan datake facin din gadon yai folding hannuwansa yana zuba mata zafafan idanuwansa da zafinsu shi kansa yakeji sbd radadin dayake cikinsu.

Bai dauke idanuwansa daga kanta ba yana jin ciwo da radadin dayanzu tana dauke da gudan jininsa haryanxu,

Ahankali cikin bacci taji nauyin idanuwansa akanta ta bude idanuwanta ahankali cikin sanyi da rashin kuzari suka sauka akan fuskansa datake kallan tata ya dan sauke wata ajiyan zuciyan ahankali tareda motsawa ya dawo gabanta ahankali tareda durqusawa ya dora tafin hannunsa daya akan nata ya kama ahankali tareda bude baki yace

"Hi" daqyar muryansa a shaqe.

"Yaya jikinki?
Yaya kike feeling yanxu?

Sake dan hade hannuwansu yayi ahankali yana kallan cikin idanuwanta da suka ciko da wani irin hawaye tana kallansa ta kasa bude baki sai daya daga hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali tareda kasa cewa komai sbd abinda yake ji ya dan dauke idanuwansa daga cikin nata sbd jan da sukai zasu iya bata tension sabo.

Sake tambayarta yayi yanda takeji ta dan rintse idanuwanta ta bude tareda bude baki kaman kuka zai zuwar mata tace

"Banajin dadi sam,I'm not ok,zuciyana.....

Hannunsa daya da baya riqe da hannunta ya saka ya rufe mata baki yana dan hanata maganar da zata ci karfinta yace

"Ki warke first okay?

Shiru tayi tana janyewa daga hannunsa ahankali tareda juya masa baya ahankali tana shin shiru alaman shima ya tafi kawai bata buqatansa.

Shiru yayi yana kallanta yaga alaman bata son ganin nasa hakanan dan haka ya miqe tareda gyara mata rufarta ya fice.

Yana fita bangarensa ya sake komawa baya buqatan kowa bai kuma bi ta kan Meenah ba sbd har lokacin zuciyarsa bata gama dawowa daidai ba yana tana buqatan tayi nesa dashi.

Su Dr Mum kuwa suna shiga a palo suka samu fammah da mum din tata zaune tana kokarin ganin taci abinci amma har lokacin idanuwanta a bushe suke sunyi wani irin ja bata ce komaiba bata yi komaiba kuma bata motsin komai guri daya take qurawa ido tayi shiru sai wata irin ajiyan zuciya datake saukewa mai karfi akai akai wadda itace take daga hankalin fammah.
MAMUH
09033181070
[16/06, 3:24 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

121
Zaunawa sukai dukansu babu me walwala babu kuma wanda yake cikin sakewa ko kadan.

Fammah da jikinta yake tsananin sanyaye cikin rashin kuzari da kasa kallansu ta bude baki ta gaidasu tana dan riqe hannun mum dinta cikin nata data sarqe sbd koma me sukazo fada mata ta bata sassaucinsa duk da su dukan suna buqatan sassauci daga duk abinda zasu ji ayau din.

Maamah ce ta fara bude baki tace

"Fammah yaya jikin naki?
Kada ki sakawa kanki damuwar da zata illata lafiyanki kinji ki lura da kyau"

Gyada kai famman kadai ta iya yi kafin Dr Mum ta bude baki da kulawa duk da suna cikin tsananin bacin rai da baqin ciki da tsananin zafin abinda Meenah din tayi amma kuma zasu danne sbd sun yadda da basu kyauta mata dinba na boye mata komai dan haka ta kalleta cikin larabcinsu tace

"Meenah nasan baa kyauta ba amma kisani duka komai daya faru yazo ne a bazata garemu sbd mu kanmu bamusan da auren ba sai daga baya,
Hakama shi kansa Raheem koda mahaifinsa ya daura masa aure da SANAAH din bai sanar dashi ba sai bayan hakan,
Nice na zabi boye maki sbd naso raba auren da farko kafin daga baya duka muka hakura sbd auren bame rabuwa bane,
Munyi miki laifi kuma duka kowa yayi kuskure amma ki kwantar da hankalinki sbd babu wanda zai taba wulaqantaki ko cutarki a cikinmu sbd kema 'yace da muke kaunarki kinsani."

Maamah ce ta karbi zancen da zayyane mata komai da karawa da tausarta da nasiha.

Dagowa Mum din tayi idanuwanta sun tsananta wani irin jajir hannuwanta na dan rawa ta zuba musu idanuwanta cikin kanta da kirjinta yana ci da wata irin wutar da har a hannuwan fammah tana ji ta bude bakinta dayake rawa tace

"Shekaru Kusan goma da auren da bansaniba"

Wata ajiyan zuciya ce ta kufce mata mai karfin gaske jikinta na qara rawa fammah ta qanqame hannunta a cikin nata tana dan ambatar sunanta kadan sbd bata sassaucin abinda takeji.
Chapter 121 · 0% Book details