← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 154

Sashe 144

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wanda yaci karo da hajiya dake kwance cikin jini rikicewa yakeyi ga Samad dake wata irin haukar datai muni dan wani watsi yayi dasu Maamah din yana damqo meenah wadda bakinta bai mutu ba tace

"Wallahi bazan goge video dinkaba sai kowa a jeerah da duniya ya gama ganin yanda ka sadu da matar dan uwank.......

Daidai nan Fleet da baya gani sosai ya iso gurin kalaman na shiga kunnuwansa maamah da bata daddaraba kuwa hannuwanta biyu ta saka da karfi tana rufe bakinta ta baya da danneta Dr Mum kuwa a haukace ta cakumo hannuwanta tana kokarin kwace wayar wadda ta riqe gam gam kaman ranta tana ihu da tsinewa dik wanda yake gidan albarka tana haukace musu gabaki daya.

Mommy ce ta saka hannu tana taya Dr Mum kwace wayar wadda taqi sakar musu ba tsammani sai ganin Fleet sukai a gurin wanda hannu kawai ya miqa mata yana sauke idanuwanta da suke jajir wata wutar masifar da bai taba ji ba tana ci a jininsa ya bude baki da wani sautin daya saka kowa tsayawa cak cikin mugun tension da zifa yace

"Ku saketa"

Sakinta sukai Samad ma jikinsa ne yake wata rawan gaske duniyarsa na kamawa da wuta gabaki daya ya sake motsawa yafison ya shaqeta ta mutu har lahira a rasa me bude bude wayarta sedai take imran ya masa wani mugun riqon daya ringa wata fixga yana haukacewan shima gabaki daya.

Riqe wayarta tayi gam tana tana kallansa da jajayen idanuwanta da har wani ruwa suke tsabar masifa da haukar dake cinta.

Cikin wani irin kuka da haukacewa Nabeela tace

"Video din SANAAH da Yaya Samad ne ta sake a cikin group na jeerahs shine Hajiya tace saita cire akan hakan ta kashe hajiya wayyo na shiga uku na lalace hajiya,ta kashe hajiya wlh..... wani ihun kuka take zundumawa da karfi tana cakumo hajiyar wadda take a some ba alaman rai.

Dad na Jin hakan da wani kafirin sauri ya fita yana komawa bangarensa da sauri ya dauko wayarsa yana budewa kai tsaye kuwa yaga video din amma bai bude ba ya juyo da sauri hankalinsa tashe yana jin kaman hawan jininsa zai tashi.
#MAMUH
09033181070
[25/06, 12:48 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

143
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Tin daga nesa yake cewa maza a karba wayar hannunta kafin kowa ya bude a goge ko zaa datsa hannuwnata akarbe wayar da gaggawa.

Daman Dr Mum tinda taji hakan tayi kan Meenah din tana kokarin kai hannunta ta kwaci wayar Fleet da kirjinsa ya kasa daukan numfashinsa hannu daya yakai idanuwansa a rufe ya mata riqo daya ya bude hannuwanta da ko rabin kwatan karfinsa bataiba ya cire wayar daga hannunta tareda jefar da ita gefe da karfin gaske sbd jin yake hannuwansa na son shaqarta sai ranta ya fita daga dangar jikinta amma tsananin so da kaunar dayake wa yarsa yana controlling dinsa.

Hannuwan Dr Mum na rawa ta bude wayar tana shiga abinda tafara gani ya saka jiri dibanta wayar ta fadi daga hannunta a bude video din na playing wanda idanuwan Fleet din jajir suka sauka akai sedai kafin ya gani Imran da wani irin zafin nama ya dora kafarsa akan wayar jikinsa na wata irin rawar da bai tsaya komaiba ya saka kafarsa daya yakaiwa Samad wani mammunan harbin da yayi baya ya fadi kasa jikinsa na rawa idanuwansa jajir ya dago da sauri yana kallan Dad ya bude baki zaiyi magana imran ya fizgo wata towel qarama dake dakin ya tura bakinsa yana turasa waje yaransu biyu dake kofa take suka bace dashi daga gurin.

Acan ciki kuwa Maamah ce ta dauka da sauri ta shiga ta goge da wata irin sauri tareda dubawa taga hadda Fleet din ta turawa dan haka da sauri ta goge nasa shima tana miqawa Safiya wayar tace ta konata a take.

Dad daman bai iya dake shigowa ba sbd da hannuwansa shi kansa zai iya aika Meenah lahira dan haka ko abinda ya shafeta baya son sake gani har abada.

Cikin kuka mai karfi daya zo mata da wata irin wuta a kirjinta tace

"Idan kun goge video bazaku goge abinda ya faru cikinsa ba har abada wanda yake gaskia ne"

A lokacin ne Dad ya shigo ya kalli Fleet wanda ya bude baki zaiyi magana ya katsesa da cewa

"Matarka gaskia take fada Tabbas Samad yaso lalata rayuwar SANAAH wanda hakan ya saka na aurar da ita gareka,
Wannan shine gaskiyar da haukarta take bata ta fada maka dan haka ni yanxu na fada maka ka sani,
Idan hakan wata matsalar ce da zaa kalli yata da wata fuskan a yanxu basai anjima ba ina son ka sakarmun ita dan wlh tallahi ayau idan nine ubanta danake da iko da ita ta gama zama da matarka da kai"

Cikin wani irin mummunan zafin da basu taba ganinsa a ciki ba ya juya ya kalli Maamah yace

"Wlh tallahi yau yau SANAAH ta gama zama da aurensa matiqar baisan hukunci da matakin daukaba akan haukar da matarsa keyi sbd har abada babu sauyi ko gyara a lamarinsu su dukan"

Juyawa yayi ya fice da zafin gaske zafin daya saka ita kanta meenah kallan Fleet da sauri tana baro inda take tsaye tana yowa gurinsa zatai magana ya furta mata kalman data saka duka su Maamah saurin kallansa da mugun tashin hankalinda ya saka Dr mum juyawa tabar gurin idanuwanta jajir sbd bataso akazo nan ba kodan riqe amanar Meenah dataso amma ayau meenah din da kanta ta yanke igiyar aurenta duk da ba qaramin kokari Raheem din yayiba gurin danne kansa akan abubuwan data ringa yi.

Maamah ma kasa motsawa tayi sbd jikinta daya dauki rawa harya juya da wani irin zafin da idanuwansa da fatar jikinsa sun nuna dan koina jikinsa ja yayi alamar ba qaramar wuta ce take cinsa ba.

Meenah din kuwa hannu ta dora akai zata kurma ihu sai kuma ya kasa fita tsabar abinda taji yaxo ya danne kirjinta da maqoshinta tareda danne jinta da ganinta ta silale a gurin tana kasa ko jan numfashi da kyau.

Nabeela datake cikin nata tashin hankalin itace ta bi bayan wanda suka shigo aka kwashi hajiya zuwa asibiti hankali tashe sbd jini sosai take fitarwa.

Fleet na fitowa baya gani sosai baiyi tafiyar taku biyar ba daga bangaren kafafunsa sukai wata sarewa da karfin gaske ya zube akan gwiwowinsa da karfin da wani irin gudun gaske Imran da securities dinsa suka yo kansa hakama Maamah da bata taba ganin wannan mugun ganin ba tayo kansa tana fasa wani irin kuka a karan farko na rayuwarta bayan rasuwan Nasir tana kallan fleet din wanda take idanuwansa da sukai wani munun gani suka qarasa munana da tashin hankali akai ciki dashi da gaggawa jikinsa na wata irin rawar da komai na jikinsa ke rawa yana wata irin loosing control din kansa gabaki daya.

Hana kowa shiga gurinsa akai a take harsu Maamah da dr Mum sbd babu wanda zai taba iya ganinsa a wannan halin Dad ne kadai ya shiga da Mr Sideeq sai Imran din da kuma aid din gaggawa da aka buqata daga wani babban likitan sojojin dake qasar allah yasa yana garin.

Anan aka shiga sabon tashin hankali da firgicin da baa taba shigaba musamman su Dr Mum da basu taba sheda hakanba saisu Dr da imran da securities dinsa da suke soldiers ne kadai sukasan me hakan ke nufi dan kuwa a wannan halin dayake ciki kome zai iya yi sbd haukan allurar datake kona kowace drop ta jinin dayake jikinsa.

SANAAH dataji abinda yake faruwa damuwanta da tsananin quncinta qaruwa yayi ta kasa fitowa tayi kuka tayi kuka har idanuwanta da karfinta ya kare jin takeyi tana buqatan barin kowa da komai itama sbd a yanxu anriga an sakawa alaqarta dashi tabo tabon da bazai taba gogewaba,
Kowa yaga mummunan qazantacciyar kaddararta datake boye.

Wani irin nauyi da daci kirjinta yake mata da duniyarta tayi duhu dip babu sauran haske a cikinta.

Wuni akai cikin mummunan tashin hankali tako ina a jeerahs din,

Fleet ya sakasu a mummunan tension da tsoron da basu taba samun kansu ba,
Hajiya na asibitin rai a hannun Allah,
Ga Samad bat aka nemesa aka rasa yana hannun yaran imran daya saka a ajesa batareda kowace hayaniyar ba tukuna.

Mommy ta ita kanta tashiga daki tayi kukan data jima batai irinsa ba kafin ta taho bangaren Dr Mum din ta samu SANAAH har daki zatai mata nasihar daukan kaddara sai suka qare da kukan da basu iya cewa juna komaiba har tsawon lokaci kafin ta mata maganganu masu sanyi ta fito.

Sai yamma aka samu daidaituwan Fleet wanda take lamarin ya koma masa ciwo mai karfi dan kuwa fever hadda qata fixga da jijjiga yakeyi.

Duk wannan abinda akeyi Imran raba hankalinsa yayi biyu a cikin wannan tashin hankalin ya tabbatarda ya samarwa ms meenah ticket din barin qasar a tsakiyar daren dan haka koda lokacin tafiyar yayi haka ya fito a cikin daren da mota ya tsaya cak dole saida Maamah da kanta ta fito da ita da akwatinta kaman wanda bata gani haka ta fito da ita bata hayyacinta bata iya ko magana batama san me take ba aka sakata mota baice komaiba yaja motar da speed din gaske sai a airport.

A cikin daren bai dawoba sai daya tabbatarda jirginta ya daga tukuna ya dawo gida duk da kowa yasan bata hayyacinta saita sauka kasar Morocco zata san halinda take ciki a kuma Allah ne kadai zai hana mata dawowa.
Chapter 144 · 0% Book details