← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 154

Sashe 34

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa sojan yayi ya fice daga dakin tareda jan kofar ya rufe ya koma waje sbd babu wanda zai shiga kuma koda family member ne.

Al'amin dayake tsaye a inda aka barsa dago kansa yayi ahankali a natse daidai lokacin Sir jeerah ya dago manyan idanuwansa da basu rage kwarjini ba duk da manyanci ya sauke su akan Al'amin wanda yayi qasa da kansa cikin girmamawa da mutuntawa.

Mr S ne ya bude baki yace masa ya qaraso ya zauna yana nuna masa guri.

Takowa yayi a hankali a natse ya zauna a inda aka nuna masa tareda hadiye wani numfashi.

Mr S ne ya qare masa kallo a cikin nutsuwa sosai kafin ya bude baki zaiyi magana a wani irin nutsuwa da slow Sir jeerah ya daga masa hannu yana gyara zamansa ya saukar da idonsa tsaf akan Al'amin yana bin kowane numfashinsa da fuskansa da nazari kafin ya bude baki cikin kamewa da zallar girma yace

"Kafin ka fada duk abinda yake tafe da kai ka fara tabbatarda kasan me zaka fada,ka tabbatarda gaskiyarsa,hujjarsa,shedarsa da tabbacinsa tareda haqiqaninsa nikuma nayi maka alkawarin idan ka kasance me gaskiya zan baka adalcin dazai gamsar da kai kuma gaskiyarka na nufin koda babu alaqa da ahalina zan nema maka adalcinka ko a gurin waye dan haka ka tsaya akan gaskiyar maganar da duk zaka fada,
Ina sauraranka?

Wani nauyin dayake kirjin yaya Al'amin yaji ya fara narkewa yana bawa kirjinsa samun numfashi me sanyi ya dago idanuwansa da suka qara jajir ya bude baki batareda tsoro ko shakka ba yafara cewa

"Sunana AL'AMIN KHALIL IBRAHIM kuma ni maraya ne dake dauke da nauyin mahaifiyata da qanwata hakama nine uwa,uba,da da kuma yaya a garesu....

Bayanin komai yafara jerowa akan yanda Samad jeerah ya shigo rayuwar SANAAH da yanda ya ringa musu alkwarin aure yana fasawa har zuwa inda yayi musu mummunan illar data saka jikinsa fara wata irin rawa radadin idanuwansa na tsananta yayi shiru yana jin kaman zai rasa kansa tsawon mintina kafin ya bayyanarda yanda hukuma sukaci zalinsa akan ya nema adalci da yanda a yanzu rayuwarsa data mahaifiyarsa da SANAAH take cikin hadarin da garin ke neman gagararsu sbd da gaske dai komai zai iya faruwa dasu sbd kawai sun nema haqqinsu gashi Samad din bazai taba kyale SANAAH ba.

Tsit lafiyayyan palon ya dake dauka wanda girman mummunan tashin hankalin dake tafe da maganganun Al'amin ya saka Mr S ringa fidda wani irin zufa yana dago idanuwansa da nauyi ya kalli Sir jeerah wanda yake zaune a yanda yake bai motsaba idanuwansa a kafe akan Al'amin wanda yayi shiru.

Motsi ma kasawa Mr S yayi dan yana iya jiyo tension din dake cikin niimar gurin dan kuwa a Sir jeerah wannan labarin da Al'amin yazo dashi gwara ace kawo masa labarin mutuwar Samad din yayi dan haka tension din yake qara yawa a iskar dakin har saida mr S din ya iya tattaro karfin hali ya bude baki yana kallan Al'amin yace

"Meyasa zaa yadda da abinda kazo dashi malam Al'amin?
Kasan girman abinda kake fada??

Dagowa Al'amin yayi ya kalli Sir jeerah daya sauke numfashi mai nutsuwa hankali kwance ya motsa tareda miqa hannunsa daya a gefensa ya dauki wayarsa ya saka kira kai tsaye.

Ana daukan wayar cikin kamewa yace

"Inason ganinka a yanxu"

Kashe wayar yayi ya ajiyeta kafin ya kalli Al'amin yace

"Ba damuwa malam Al'amin naji duka bayaninka ka tafi zan nemeka da kaina idan na duba cikin lamarin"

Wata sabuwan ajiyan zuciya yaya Al'amin ya sake tareda godiya ya miqe Mr S na gaba yana bayansa suka fice.

Da mota Mr S da kansa ya maidasa har gida har kofar gida ya sake basa tabbacin nemansa tareda tabbatar masa da maganar kada ta fita kota halin yaya.

Bayan tafiyar Mr S yaya Al'amin jin yayi nauyin kirjinsa ya dan sake raguwa sbd abinda ya gani a tattare da Sir jeerah to tabbas zai basa adalcin da yayi masa alkawari sbd girmansa da kwarjinsa da manyancinsa baiyi kama ko kadan da wanda zai taba iya saba alkawari ba.

Bai shiga gida ba gurin aiki ya juya ya wuce sbd baida kudin dazai biya bashi da wanda zasu ci gaba da hidimar gida gwara yaje a hakan ya dan qarasa wunin ya samo ko yayane.
#MAMUH
09033181070
[29/04, 2:26 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

33
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Bai dawo gida ba sai dare kuma ya dan samu nutsuwa a zuciya da gangar jikinsa yar kadan a yanzu daya samu ya isar da qararsa inda zaa iya dubawa,
Muradinsa AA ya samu hukuncinsa SANAAH ta samu yancin fita cigaba da karatunta batareda tsoro ko shakkar ya ringa bibiyarta ba duk da dai har cikin ransa a yanxu yafi shaawan yiwa SANAAH din aure sbd shine kadai kariyar da zata samu daga AA wanda yakeda tabbacin bazai taba kyale SANAAH din ba.

Wanka yayi ya zauna yaci abinci a tareda su SANAAH din wanda sun jima basu samu hakan ba,

Maganinsa SANAAH ta bude masa daya bayan daya tana basa yana sha harya sha duka daga nan ne mommy take tambayarsa yanayin yanda yake iya aiki da yanayin nasa.

Dan murmushin karfin hali yayi yana cewa

"Ai raunikan ne kawai a bude amma ina jin saukinsu sosai"

Maida kallansa yayi akan SANAAH kafin ya maidasu akan mommy yace

"Mommy indai na samu wanda SANAAH zata samu aminci a gurinsa aure zan mata ta tafiyarta gidan mijinta kawai,idan allah yasa na samu wani aikin me dan kaurin kudi zan rokesa alfarmar taci gaba da karatu naci gaba da daukan nauyin karatun nata acan insha Allah"

Shiru mommyn tayi tareda tinanin maganarsa da itama tabbas ta ratsata dan haka ta dago ta kallesa tace

"Eh hakan ma yayi tinda dai kaddarar ce taxo mana a hakan gwara ayi mata auren kowa ya samu nutsuwa har ita dinma"

SANAAH dataji wani irin dumi da komai ya mata dum shiru tayi tana dagowa ta kalli yaya Al'amin din a natse sbd tinda yace aure ze mata to batada sauran zabi kuma ita kanta a yanzu datakeson kota halin yaya AA ya fice daga rayuwarta to zatai auren.

Yau sun dan zauna sun yi maganganu na dan lokaci sosai a tsakar gidan kafin kowa ya shige.

Washe gari ma haka ya fice aikinsa bayan sunci abincin safe a tare dukansu kaman yanda suka saba haka ya fita damuwarsa na qara raguwa dan yasan zuwa yanzu insha Allah AA yabar rayuwarsu har abada.

Shiru shiru kwana biyu baa nemesa ba kuma bai wani damu ba sbd baima saka ran zaa nemansa ba kawai dai buqatansa yasan ta biya tinda dole Sir jeerah zaiwa AA kashedi mai tsaurin da kila ko a hanya bazai fatar sake ganinsu ba.

****Acan Jeerahs kuwa a lokacinda Sir jeerah ya saukar da idanuwansa akan Samad tambaya dayace yayi masa kai tsaye wadda bai isa yayi masa karya ba ko boyo dan yasan abinda zai iya biyowa bayan karya ko boyon wanda hatta mahaifiyarsa saita shiga baqin cikin hukuncin dazai hau kansu mai munin da bazasu iya dauka ba dan haka yana gama jero masa tambayoyin da suka duniyarsa girgiza da mummunan shock dagowa yayi zufa na tsiyayo masa ya kalli Sir jeerah din da nasa idanuwan suke jajir akansa take yaji yana neman hadiye zuciya ya mutu sbd tashin hankali dan haka daqyar ya iya bude baki yace

"Eh nasansa da kuma kanwar tasa"

Shiru ya dan yi yana rasa ta yanda zai basa amsar tambayar ta biyu wanda take daidai da iya rasa ransa ya bude baki da wani nauyin bakin dake rawa zufansa na sake gudu yace

"Tsautsayi da kaddara ne suka shigo lamarin kuma babu abinda yakai ga faruwa a tsakaninmu"

Da wani karfin halin dayake neman faso kirjinsa ya qarasa zancen yana kasa dagowa ya kalli mahaifinsa.

Sir jeerah daya gama nutsar da zuciyarsa akan rashin hayaniyar da lamarin kai tsaye ya danne fushi da bacin ransa da bayyanarsa ba kyau yace

"Kanada raayin aurenta a matsayin matar da kakeso zaka daraja???

Shiru ya dan yi kansa a qasa cikeda shakkar hukuncin dazai hau kansa amma kuma can qasar zuciyarsa haryanzu bayajinta a matsayin matar dazai iya aura ga kuma wani tsananin sonta dayake cinsa dan haka ya dan dago kadan batareda ya iya kallan sir jeerah dinba ya girgiza kai a natse.

Kafesa da ido Sir jeerah yayi na tsawon mintina kafin ya bude baki ya sake maimaita tambayarsa da kyau yace
Chapter 34 · 0% Book details