Sashe 10
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maqota ya shiga da sauri ya kirawa dattijiwar gidan ta taho da gaggawa ta fada dakin fatiman da yake cikeda wata irin kura sbd jimawan da akai babu kowa a cikinsa.
Cikin matsanancin wuya da azaba fatiman ke naquda me wahalar gaske tana ambatar sunan Allah a zuciyarta hakama da yi musu addua itada yar uwarta fammah tareda yayansu sbd tasan fatima kam bata hayyacinta bazata samu daman addua a lokacin haihuwa ba.
Bata haihu atake ba saida ta wuni tana fama da azabar nakuda mai nauyi kafin Allah ya sauketa ta haifo 'da namijin da khalil aka miqowa shi a hannunsa.
Karban jaririn Khalil yayi idanuwansa jajir da hawaye sbd tinawa da abinda yayansa Ibrahim ya fada daya kirasa akan haihuwan cewa yayi Allah ya rabasu lafiya kawai ya raya mata duk abinda zata haifa.
Khalil nada zuciya dan haka baida niyar sake kiransa tinda daman koyaushe akan fada suke akan irin yanda ya zabi duniya yabar matarsa dan yanzu watansa kusan tara harda kwanaki bai waiwayota ba.
Da taimakon dattijuwa barakah fatima ta kimtsu bayan haihuwan dan kuwa sai data tabbatarda ta taimaka mata tayi komai ta shirya ta ta shirya babyn wanda cikin ikon Allah komai na mahaifinsa ya dauko wanda yake sak da qaninsa khalil dan haka saima kusan duka hasken khalil da kammanin khalil suka bayyana a fuskansa sbd kamar khalil da babansa.
Babu yanda zaiyi haka ya cire yan kudadensa dayake kasuwancinsa yaje ya siyo kayan sakawa kala biyu da dan abubuwan buqata da abinci me kyau ya kawo mata.
Daqyar ta iya cin abinci duk da ta haihu lafiya kalau sumul amma zuciyarta na cikeda damuwan son sanin halinda fammah take ciki dan haka tin kafin ma fammah ta dawo hayyacinta tanason kasancewa a gurin.
Shi kansa khalil tinda tai masa bayanin baasan ta taho ba sai baida niyar hanata komawa inda zata samu kulawa me kyau sosai itada babyn kawai dai yace ta jira ta sake samun karfi da lafiya.
Karban babyn ya sake yi yayi masa adduoi da huduba tareda ambatarsa da suna MUHAMMAD NASIR.
shiru fatima tayi tana maimaita sunan a zuciyarta tana sauke numfashi da ajiyan zuciya sbd ta tabbatada dai 'danta ne ita kadai bada babansa Ibrahim ba.
Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangaro mata tanajin wani irin daci da zafi suna danne kirjinta na rayuwar data samu kanta ace ko mijinta da shine kadai danginta yayi watso da ita,
Idan abaya ta zauna a jeerah villa ba goyo tayaya yanzu zata zauna da goyo?.
******
Anyi nasarar aikin ciro babyn Dr fammah,
Babyn da dukkanin familyn jeerah suke jira,
Babyn da wasu daga cikinsu sunfi damuwa dashi,
Babyn daya fito duniya da dukkanin tsananin kauna daga ahalinsa da iyayensa...
Alh babba Ahmed jeerah ne ya karbesa a hannunsa ya rungumesa kafin yayi masa wasu irin adduoi da kiran sallah kafin ya ambaci sunansa da ABDUL-RAHEEM HAKEEM JEERAH.
Kowa a familyn murna da farin cikin samuwar Raheem sukeyi hakama masu jiran fidda labarin tini suka fidda amma har lokacin mahaifiyarsa tana cikin mummunan halinda Allah ne kadai yasan menene matsayin rayuwarta dan kuwa mahaifarta ta fashe ta watse wanda hakan ya saka hankalin abokan aikinta likitoci mummunan tashin yanda zasu iya sanar da ahalin jeerahs da ita kanta fammah din wannan mugun labarin idan ma ta samu rayuwarta kenan to anyi arziki.
Da gaggawa aka sake shiga da ita wani sabon aikin wanda ya saka kowa nutsuwa murna ta dakata tukuna.
#MAMUH
#RAHEEM HAKEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#JEERAHS
GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
10
*_HARGITSI_*
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t
*********
Duk wannan tashin hankalin da tsananin da dr fammah ta shiga tin kafin haihuwa zuwa bayan haihuwan captain hakeem jeerah bai samu damar zuwa ba duk yanda yaso zuwan babu ko yar qaramar hakan dan haka yana can cikin matsanancin tashin hankali da damuwa amma duk da hakan ya iya dannewa ya fuskanci aikin dayake gabansa mai mahimmancin da zai qara daga matsayinsa zuwa sama.
Iyayenta kam lamarin yayi musu shigar bazatan da zuciyar mahaifiyarta ta kasa dauka saida aka kaita asibitin da dole likitoci suka riqeta dan haka ba damar zuwa ga yarsu duk yanda suke cikin tsananin damuwanta da babynta.
****aikin da akai mata me tsananin hadari da taka tsantsan ne an dauki lokaci me tsayi sosai kafin aka fito da ita tsakiyar dare zuwa private dakin hutun da zata zauna.
Likitoci da nurses sun gama komai akanta sun fice sun bawa familyn daman shiga amma babu kowace irin hayaniya da ake buqata.
Sun shigo da yawansu sun tsayu akanta cikeda addua da fatar warkewanta.
Har asuba su Ummah na dakin tareda ita kafin gari ja fara haske suka tattara suka koma gida aka bar mutum daya a cikin masu aikinta dan kulawa da ita kafin anjima.
Da Raheem suka tafi sbd ko an barshi bata hayyacinta da zata iya basa nono ko wani abin dan haka suka tafi gidan dashi dan aje a shiryasa.
Wuni guda ta sake yi bata farfadoba bare dawowa hayyacinta dan haka likitoci suka sake dunguma da duqufa akanta damuwansu na ninkuwa sbd akwai abinda suke tsananin gudu da kokarin hanasa tabbatuwa.
*****fatima data kwana ta wuni ta tabbatarda ta warware sosai hankalinta bai kwanta ba ta kasa samun nutsuwa haka ta shirya ta fito tareda khalil wanda ya kaita har asibitin itada babyn tukuna ya juya ya tafi.
Ko data iso dakin babu kowa na familyn jeerah dayake asibitin bayan wadda aka bari ta kula da ita dan haka jikinta ya sanyi musamman data sauke idanuwanta akan fammah din wadda duk wata rahama da kyan gani sun bar jikinta da fuskanta dan kuwa tayi wani duhu fatarta ta bushe bakinta ma ya bushe tana kwance kaman babu rai a jikinta.
Silalewa tayi ta zauna idanuwanta cikeda hawaye tana jin hankalinta ya gama tashi gabaki daya daga karshe kasa riqe kukanta tayi ta sakesa ahankali sbd tsoron daya shigeta dan kuwa haka mahaifiyarta ta koma kafin rasuwarta tabar duniya.
Sai datasha wani irin kuka sosai kafin ta iya dago fuskanta ta kalli saratu dake gefenta tsaye shiru itama tausayin fammah din takeyi sbd yanda ta kasa samun cikakkiyar kulawa da kauna daga dangin mijin daya kamata su kula da ita sbd mijinta da baya kusa.
Tambayar babyn fammah tayi
Saratun ta fada mata yana can jeerah villah an tafi dashi.
Wasu hawayen ta sake sharewa kafin ta juyo da kallanta kan fammah tana jin kaman zuciyarta zata dena bugawa sbd damuwa da wani irin daci.
Shiru sukai a dakin tsawon lokaci sai ga likitoci sun shogo tareda Su daddy da kansu da matayensu harma da Raheem an dawo dashi.
Ummah data ga fatima batama lura da goyon danyan jaririn dake bayanta ba ta dan yi mata fadan inda ta tafi tin jiyan kafin ta miqo mata Raheem wanda yake cikin lafiyayyan lallausan bargon babys me fari qal yana bacci jikinsa sanye da fararen bodysuit da hula an nadesa sosai.
Hannuwanta biyu ta saka suna wata yar rawa zuciyarta na bugawa da kaunarsa idanuwanta fes akansa tana masa kallanda da mahaifiyarsa na hayyacinta itace zatai masa ta rungumesa jikinta tana sauke ajiyan zuciya tsananin kaunarsu da sonsu su biyu shida nasir dake bayanta tana ratsota ta gaba data baya.
Ficewa tayi sbd bawa su Daddy guri da likitoci saratu na biye da ita.
Suna fita zaunawa tayi a qaramin sitting room din dake dakin ta sake dago Raheem da kai tsaye zaka san balaraba ce ta haifesa ta zuba masa ido cikeda kauna kafin ta fara rero masa adduar dataiwa danta shima.
Basu wani dauki time ba a waje akace su koma ciki sbd Raheem.
Su daddy sun gama komai kuma an gama jero musu komai na halinda fammah take ciki wadda ta rasa mahaifiyarta shikenan ba ita ba haihuwa har anaba hakama fashewan mahaifiyarta ya janyo manyan matsaloli a lafiyarta da gangar jikinta da ba yanzu ne ba itada lafiya sedai a sannu sannu lokaci zai warkar da komai.
Babu wanda ya iya cewa komai a familyn jeerah sbd lamarine daya girgiza duniyarsu da kowa ya dauke wuta.
Fitowa sukai suka bar asibitin dan komawa a san yanda zaayi a sanar da Captain Hakeem.
Ganin fatima da akasan bayan ita Fammah bata buqatan kowa ya saka baa damuba sedai aka kawo musu dukkanin abinda zaa buqata da sakewa.
Fammah bata farfado ba sai a daren ranar shima iya idanuwanta kawai take iya budewa bata iya ko motsawa me dan karfi bare tashi magana ma bata iyawa sedai kallo kawai.
Fatima ce kadai a tareda ita ko data farfado babu kowa nata babu kowa dangin miji,
Lumshe idanuwanta tayi ta sake budewa a hankali tana jin tama rasa kanta bare sanin menene takeji take cikinsa.
Likitoci suka bawa fatima daman gyarata ta dan sake shiryata aka sake gwaje gwaje da sauran abubuwansu suka gama komai suka fice.
Baa bada daman bata komaiba na ci ko sha drip ne da allurai kawai ake bata ba bata lokaci.
Raheem ma a hannun fatima take ganinsa wanda shima ake cikin tashin hankalin yunwar dayake ciki dan kuwa kuka yakeyi sosai ida yatashi.
Yanayin halinda Raheem yake ciki ya sake daga hankalin jeerahs da ita kanta fatima da mahaifin fammah wanda abubuwan sukai masa yawa ga Amminta a kwance gata a kwance babu me sauki a cikinsu.
Shi kansa hakeem dayake can sabon tashin hankalin ya shiga duk da har lokacin baa sanar dashi komaiba na abinda ya samu din me tada hankali.
Likitocin yara manya aka nema suka zo suka dubasa suka bada shawarwarin abinda ya kamata take aka siyo duk abinda sukace da madara kaman zaa bude shagonta.
Fatima aka nunawa komai da bayanin komai na yanda zata ringa basa har lokacin basu bawa tata haihuwan mahimmancin daya kamata suyi tinanin abin zai mata yawa ba.