← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 154

Sashe 81

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qarasowa sukai palon Dr Mum din ta zauna tana nuna mata gefenta ta zauna ta jata wani zancen dazai sakata sakewa.
#MAMUH
09033181070
[17/05, 9:09 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

75
Lafewa tayi shiru a gefen Dr Mum din har laasar suna palo fammah ma ta kirata sun dan yi magana tsawon lokaci wanda famman ta fahimci SANAAH din tayi sanyi sosai da alama tana missing dinta dan kaman baby take indai mommy bata kusa itama datake tarairayanta bata kusa dan haka ta ringa tarairayan nata a waya ita kuma tana sake jin kewanta musamman yau din.

Data gaji da zaman bayan laasar kitchen ta nufa gurin safiya tana saka hannu a aikin daren wanda Dr Mum ta kirata tace ayi hadda na RAHEEM din.

Sbd hadda nasa din da sukai sai suka kai har magrib kafin suka gama komai aka aje a dining tukuna ta fito kitchen din tana waya da Mommy ta nufi dakin mommyn.

Karban waya Ms Meenah tayi itama SANAAH ta gaidata cikin nutsuwa da sanyi tana tambayarta taron.

Amsawa Mum din tayi tana janta da firar da dole SANAAH din take amsawa cikin kulawa da girmamawa tana kokarin boye sanyin jikinta da nauyin dataji tanaji.

Sun riqeta da fira tsawon lokaci kafin sukai sallama ta tashi ta fada toilet tayi wanka da alwala ta fito ta tayar da sallah tana gamawa sai datai ishai ta fito a natse ta tadda su Dr Mum na shirin cin abinci a dining ta zauna itama tana sake gaidasu da serving dinsu tana bawa Maamah amsar tambayar datai mata na abincin Fleet.

Wayon datai suna gamawa tasan a daidai wannan lokacin bai dawoba dan haka taje dining ta jere komai danma kada anjika ace takai dan haka da yar nutsuwa ta sanarwa maamah din ai harta kai ta aje masa.

Murmushi kawai Dr Mum tayi tana cewa

"Eh lallai sannu da kokari kin huta sbd anjima ko?

Sauke kai tayi tana rasa abin fada ta juya taje ta kawo ruwa da juice masu sanyi ta ajiye tana zaunawa.

Abincin sukaci cikin walwala da sakewa suna gamawa tayi kitchen hada shai din Dad safiya kuwa ta tattara dining.

A natse tayi aikinta ta gama shirya a tray mai kyau ta fito tana nufar daki ta sako doguwan riga mai fadi sosai da datake da zip tin daga sama har qasa akan black kayan baccinta ta yafa veil qarami akai ta fito ta sanar dasu mommy dake palo zaune suna fira ta fice da cewan ta tafi gurin Dad jeerah.

Ko data isa gurinsa shi kadaine yana ganinta farin cikinsa ya bayyana yana tabbatarda yayi kewan yar tasa kwana biyu.

Itama cikeda kulawa da kewansa ta qaraso ta zauna tana gaidasa da sakewa a gabansa sosai.

Cikin kulawa yace

"Nasan hadda kewan Likita qarama ya sakaki kasa fitowa sbd kina kewansu hadda mommynku"

Murmushi tayi mai kyau daya bayyanarda kyawunta a tsanake tace

"Ai Dad idan zasu sake tafiya zan bisu duk inde da fammah zaa tafi"

Dariya yayi yana sake janta da firar da suka kwana biyu basu yiba.

Murmushi ne sosai mai kyau akan fuskanta ta sake sosai tana cikin walwalanta sai kamshinsa taji yana shiga hancinta ta dago kai da sakewanta da murmushinta suna cigaba da fitowa sai ganinsa tayi ya sako kai cikin palon a tsanake da wata kwarjini da kamewa dan haka ta dan shanye Murmushin dayake kam fuskarta tana qin sake juyawa ta kama nutsuwanta cikin sanyi da wata irin kunyar datake shigarta da sanyi a gaban Dad din wanda ya dago ya kalli RAHEEM din da sauran murmushinsa akan fuskansa yana maida kallansa akan SANAAH din wadda tai sanyi gabaki daya a take da wata irin nutsatsiyar kunyar data kara masa kaunarta ya bude baki yana amsa gaisuwan Fleet din da maida kallansa a sake da kulawa.

Wani numfashi mai sanyi da nutsuwa ta dan ja mara sauti tareda dan waiwayowa kadan ta bude baki tace

"Sannu da zuwa,ina wuni?"

Jefa mata idanuwansa yayi wainda taji saukansu akanta ta sake qasa da kanta tana kasa dagowa ko Dad ta kalla.

Acikim nutsuwa da kamewan datake a jininsa ya amsa da sautin daya saka Dad dan dagowa ya kallesa duka a tsanake ya amsa gaisuwan.

Sallama ta bude baki tayiwa Dad din ya tsayar da ita suna firarsu RAHEEM din yana zaune yana jinsu wayarsa ma ta ringa ringing bai dauka ba sbd yana gurin Dad din.

Ta jima sosai kafin ta miqe ta sake masa sallama ta fice daga bangaren.

Tana fitowa batai wani nisa ba shima ya fito yana bayanta har zuwa kofar bangaren su tana bude kofar tajita a rufe take gabanta yayi mummunan faduwa ta dakata cak tana jin kaman zufa zai karyo mata amma ta sake kokarin bude kofar tana murdawa da turawa amma shiru da alama dai sun rufe sun kwanta.

Tanajin isowansa a bayanta qamshinsa ya shigeta ta kasa juyowa ta janye hannunta daga handle din a hankali tana tinanin wane hali take ciki ayau gashi tana shakkar bugawa tinda dr mum batason bugawan hakama bata fito da wayarta.

Muryansa taji kaman daga sama ya bude baki yace

"Kada ki damesu tinda sun kwanta"

Girgiza kai tayi batareda sanin meyasa ma ta girgiza dinba ta bude baki batareda ta juyowaba tace

"Call Dr Mum pls"

Baice komaiba ya ciro wayarsa ya daka mata kiran dan baya buqatan cewa komai.

Ringing wayar dr mum din takeyi harta yanke bata dauka ba saida ya sake kira ta daga a tsanake tace

"Yes RAHEEM"

Miqa hannu yayi ya juyo da ita ya miqa mata wayar yana kallanta da oily eyes dinsa.

Kallansa ta dago da sauri tayi tareda girgiza masa kai tana masa alaman bazata iya magana ba shi yayi.

Girgiza mata kai yayi shima yana sake miqa maga wayar wadda muryan Dr Mum ta kuma bayyana da sunansa.

Hannunta ya kama zai saka mata wayar ta janye da sauri tana cewa

"No" ahankali da sautin qasa qasa wanda kai tsaye ya sauka a kunnuwan Dr Mum.

Cikin Kalamansa masu nutsuwa yace

"Tana kofa ne ko akwai wanda zai bude mata??

Da mamaki dr mum tace

"Like seriously RAHEEM??
Are you for real??
Akan hakanne zaku kirani da wannan lokacin dana riga na kwanta?
Ku tafi mai budewan ta riga ta tafi itama sedai gobe kuma,
Allah ya tashemu lafiya"

Tana gama fada ta kashe wayarta tana fita lamarinsu.

Baice komaiba ya juya yabar gurin da kama hannunta sbd shima yana buqatan hutawa baya son kowace gardama da rigimarta.

Itama tsabar damuwa da mutuwan da jikinta yayi batai gardama jiki a mace take taka kafafunta.

Suna isa bangaren bedroom dinsu na baya ta silale ta shige tayi kwanciyarta ba jimawa kuwa bacci ya dauketa sbd akwai yar gajiya a jikinta ta aikin datai.

Koda ya gama wanka da shirin baccinsa yaxo har dakin ya dubata yaga tayi bacci mai nauyi a tsanake dan haka sai yabarta sbd kada ya tadata ya tafiyarsa.

Abincinsa yaci kadan a dining tukuna ya koma dakinsa ya zauna yana wani karatu a ipad dinsa tsawon lokaci har dare sosai kafin ya kwanta.

Da asuba koda ya dawo daga masallaci kai tsaye can bedroom din ya wuce ya tarar da ita zaune ta gama sallah tana lafe a sofa idanuwanta biyu amma.

Gaidasa tayi da sauti mara karfi tana dan motsawa kadan.

Amsawa yayi yana mata kallan nutsuwan daya fahimci atleast yau dai bata cikin damuwa zaiyi magana wayarsa tayi ringing ya daga ya kalla yaga Ms Meenah ce mai kira ya juya a natse ya fice yana daukan wayan sbd shine ya kirata jiyan da dare bata daukaba.

Karfe 8 saura ta baro bangaren ta dawo ta wuce daki ta kwanta sai a lokacin zatai baccin safenta hankali kwance.

Da rana kai tsaye dr Mum tace yauma tayi masa abincinsa daban.

Wuni tayi a kitchen tana aiki sbd hadda snacks sukai sbd Maamah da itama tace ayi masa.

A gajiye sosai takai dare dan haka wanka da sallah kawai tayi taje takai abincin tana dawowa Maamah ta sake maidata kai fruits tana dawowa ta tadda an rufe dan haka bata wahalar da kanta ba tinda batada me kira ta koma tayi kwanciyarta a inda ta kwana jiya.

Shima bai dameta ganin tayi bacci da wuri kuma da alama ta gaji dosai sbd duka snacks din daya gani yasan itace tayisa.

Da sassafe tin kafin ya fito ta gudu dan haka kwata kwata wunin ranar basu ga juna ba.

Sake wuni tayi aikin abincinsa yauma wanda dana rana dana dare duk itace aka dorawa yanzu kuma itace mai kaiwa amma taqi barin su hadu boye masa takeyi sosai,

A bangare daya kadaici da kewan su fammah takeyi tanajin inama ta bisu sbd yanzu gabaki daya auren dayake kanta neman hawa matsayinsa na aure yakeyi gabaki daya da harta fara sabawa da hidimar duk da buya takeyi sosai.

Shi kansa busy ya zama a kwanakin na wani aikin dayake gabansa idan ya futa baya dawowa sai dare shiyasa haduwan tasu ta gagara saida suka kwana kusan tara a hakan basu sake wata haduwa ba sedai taji motsinsa ta lafe shima baya iya takurata sam dan haka ko tadata baccin dayake taddata tanayi bayayi.

Ranar daya kammala babban aikin daya sakasu zama busy sosai a ranar washe gari wuni yayi gida ya huta sosai bai tafi koina ba bayan masallaci har dare.

Karfe 8:48 dare ya fito a sanye da black silk pyjamas masu santsin gaske da suka nutsu a jikinsa da farar fatarsa mai lafiya kwarjininsa da kakkarfan jikinsa ya bayyana sosai na asalin lafiyayyan namiji yana fitowa palon ya nufi hanyar kitchen dan neman ruwa na fridge din palonsa sun qare.

A daidai wannan lokacin ta shigo sanyeda hijabinta har qasa da kayan baccinta black itama aciki.

Bata san dashiba sai data kawo tsakiyar palon taji qamshinsa a sanyaye ya shigeta ta dago a tsanake ta kalli gabanta jikinta na mutuwa da wata irin kasala tagansa a gabanta shima ya tsaya ita din yake kalla da wata nutsuwa da tsanaki na kwanakin daya dauka bai sakata a idanuwansa ba.
Chapter 81 · 0% Book details