← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 154

Sashe 30

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baya yayi ahankali cikin wani irin shock da mummunan tashin hankalin dabai taba shiga ba ko a lokacin daya rasa mahainfinsa,
Wani irin radadi ne yake cike idanuwansa suna sauyawa zuwa jajir ya dafa bango ahankali yana zamewa qasa yayi zaman yan bori tareda rintse idanuwansa ahankali dan kuwa baima iya yadda da rayuwar SANAAH dinsa bata lalace ba,
An lalata mata rayuwar dayake ta kokarin bawa kariya da tattalawa,
An bata rayuwar daya sadaukar da tasa rayuwar gurin ingantawa da bawa kariya da rayuwarsa,
Ya gaza ya zama mara amfanin dayake tinanin yanada shi,
Ya kasa tsare mutuncin qanwarsa da zai gwammaci ace shine aka lalata rayuwa ta karfi akanta.....

Cusa kansa yayi cikin kafafunsa wasu irin hawayen dabaima san suna fitowa suka fara gangaro masa yana jin kaman kirjinsa da kansa da idanuwansa zasu kama da wutar da babu sauki a cikinta,

Ita kanta SANAAH din zubewa tayi a qasa inda take tana fasa wani irin kukan dayake ratsa kunnuwansa da zuciyarsa suna tarwatsa duk wani kuzari da zuciyarsa.

Ita kanta wani irin rawa da tsoro me tsananin gaske jikinta da zuciyarta take ciki dan kuwa tasani rayuwarta ta riga ta lalace ta zama macen da babu cikakkiyar daraja a tattare da ita yan anguwan sunsan an mata abinda shine da wanda ba shine gashi har lokacin a firgici take tanajin AA a jikinta.

Mommy datake zaune ta kasa motsawa ajiyan zuciya ta sauke ahankali jikinta na sakewa tareda komai nata idanuwanta a kafe akan SANAAH wadda alamar jikinta da halin datake ciki da yanda jikinta ke fixga ya tabbatar musu da angama lalata rayuwar tata shikenan.

Wani nauyi me karfi da zafi ne yazo kirjin mommy ya danne mata numfashi ta bude idanuwanta da sukai jajir tana son magana amma ta kasa sai ganin zamewa tayi a gurin tayi kwance tana jin kirjinta da zuciyarta na bugawa ba daidai ba.

SANAAH ce ta rarrafo tayi kan mommyn a rikice tana kokarin fasa wani kukan amma bayama iya fitowa ta fada kanta tana girgiza mata kai da cewa bai nasarar lalata mata rayuwa ba amma sam mommy bata jinta sbd jinta daya dauke take numfashinta ya yanke a gurin.

Kuka SANAAH keyi tana girgizata amma ba alaman motsi ta juya ta rarrafa gurin yaya Al'amin ta fara jijjigarsa shima tana wani irin kukan dayake tayar da tsigar jiki.

Daqyar ya iya lalubo hankalinsa da ganinsa da jinsa yayi kan mommyn yana dagota gabaki daya ya fice da ita da sauri.

Miqewa SANAAH tayi batama gani sosai tabi bayansa tana jan hijabin mommyn dake tsakar gidan ta saka a jikinta suka fice.

Titi sikai anata kallansu cikeda mamaki da maganganun tabbatarwa da SANAAH dai AA yayi nasarar lalata mata rayuwa ta koma fankon da babu me iya kallanta da darajar aure idan ba dan iska mara Mutunci ba irinta dan uwanta ba.

Adaidaita suka tarar suka fada babu bata lokaci akai asibiti dasu har lokacin babu alaman rai a tattare da mommy.

Suna isa aka karbeta zuwa emergency ana tambayarsu meya sameta.

Fada sukai cewan zubewa tayi sbd shock.

Anayin ciki da ita suka koma gefe suka tsaya a rakube har lokacin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi idanuwansa na tsananta shiga mummunan halin dayake jin kaman ya dora hannu akai ya fasa ihun da duk duniya sai taji radadi da zafin kuncin da zuciyarsa take a lolacin.

Ita kanta SANAAH har lokacin kuka takeyi jikinta na rawa ta qanqame kanta a jikin bango tana kasa dagowa.

Zaman dayafi na daren baqin sukai a wajen babu wanda yace kala sai yanayinsu dayake nan bai sauyaba suna jiran farfadowan mommy da akace shock ne yaso bata attack na zuciya amma da dan sauki yanayin.

Har tsakiyar dare sosai suna zaune cikin tsaka me wuyar da duka suke fatan inama ace sun mutu basu sheda wannan mummunan ranar ba,
Mommyn bata farko ba sai guraren karfe uku saura na dare cikin wani irin yanayi na mutuwan jiki da rashin kuzari ko kadan tareda damuwa me tsananin data saka idanuwanta qanqancewa bata gani sosai itama hannuwanta rawa suke dan yi.

Shiru sukai jigum jigum babu me cewa komai har asuba tayi Yaya Al'amin ya fice sallah.

Suma zuwa lokacin sun dena kuka babu karfin jiki ba sauran kowace irin walwala da kuzari SANAAH ta kama mommyn sukaje tayi alwala da sauransu itama tayo suka dawo sukai sallah.

Suna idarwa sukai sake shiru jigum jigum da shiga tinani ba tareda motsin komaiba.

A hakan yaya Al'amin din shima ya dawo ya bude baki ya gaida mommyn da jiki cikin wani irin sanyi da rashin walwala.

Itama SANAAH bude baki tayi ta gaidasa bai iya amsawa ba sai wani irin nauyi dayaji ya sake dawo masa sabo ya danne masa kirji da zuciya.

Daga shi har mommyn babu me iya kallanta dan kuwa suna kallanta zasu iya samun bugawan zuciyar kallanta a matsayin wadda wani ya ketawa haddi dan haka suke kasa kallanta gashi ita kanta ta kasa dagowa ta kallesu kunyar kanta da baqin cikin ganin halinda suke ciki takeyi.

Gari na wayewa sosai aka sallamosu suka dawo gida,
Koda suka sauka daga cikin adaidaita akwai mutane gefen kofar gidan sosai anata xaman da aka saba,

Kallo aka bisu dashi daya saka Yaya Al'amin din jin duniyarsa na sake duhu sbd rayuwarsu su duka a yanxu ta samu wannan mummun tabon da bazai taba gogewa ba hakama bazai taba barin SANAAH ta samu mijin daya kamata ba anan din dan kuwa abu ne da yan anguwa yanzu suka sani wanda kuma hakan ne sukaita masa gudu akan huldar AA da SANAAH dan haka da alfahari zaa ringa fada da kuma sanar da duk wanda zaizo neman aurenta.

Sallamar mai adaidaita yayi suka shige cikin gida ya rufo gidan sukai ciki.

Suna shiga daki suka kai Mommy wanda tayi weak sosai a dare daya dan jin nauyin kirji da ciwo sosai takeyi amma ta danne.

Ruwan wanka SANAAH da itama takejin batada lafiyar sosai ta hadawa mommy takai mata taxo ta taimaka mata har toilet tukuna ta dawo itama tai shirin wankan.

Bayan fitowan mommyn wanka tayi itama ta koma daki ta kasa komai ta dunqule a katifa sbd wani irin zazzafan zazzabin dayake cinta.

Kayan tea da bread Yaya Al'amin ya fita ya siyo ya dawo da kansa ya kunna dan qaramin gas din dasuke dashi ya dora ruwan zafin tea ya hada komai da kansa ya kaiwa kowannensu a daki ya sakasu tashi suka sha tukuna ya barsu suka kwanta shima yaje yayi wanka ya kasa fita koina ya shige dakinsa ya dunkule dan jikinsa har wata fizga takeyi sbd zafin zazzabin shima.

Wuni sukai gidan tsit a rufe kaman babu kowa sbd babu me lafiyar jiki data zuciya.

Sai kusan yamma kowannensu ya dan samu damar iya tashi suka fito daya bayan daya sukai wanka da sallolin dake kansu a lokacin ne ya sake fita ya samo musu abincin da zasu ci sbd daga Mommy har SANAAH din babu me iya girki.

Haka ya daure ya kula dasu har washe gari tukuna SANAAH ta warware mommy ma ta warware amma ta rasa kuzarinta kwata kwata dan abun ya tsaya cak a tsakiyar kirjinta ya kasa sauka kila harta mutu bazai taba sauka ba ace 'yarta mace daya a duniya anci mutuncinta haka.

Yanda yaya Al'amin ya danne ciwo da radadi da baqin cikinsa ya kula dasu sosai suka dan warware sai kawai shima ya fadi ciwon mai tsananin daya saka hankalinsu mummunan tashi sai gasu a asibiti an basa gado sbd ciwon nasa sosai yayi nauyi ciwon zuciya me tsananin gaske da nauyi.

Ciwonsa ya saka mommy sake shiga mummunan hali sbd shine bangonsu jigonsu,
Ita kanta SANAAH tashin hankali da tsoron da bata taba shiga ba a kusa kusa ta shiga ganin yaya Al'amin din kwance ba kyan gani,

Da kuka take wuni dashi take kwana dashi take sallah dashi take wanka da komai,
Damuwa da kuncin da basu taba shigaba suka samu kansu a ciki sbd yanayinsa,
Ana cikin hakan kuma kudi sukai musu qasa gashi me nemowan ne kwance.

Dole SANAAH ta dawo gida tana dan gudanar da Sanaar da sukeyi ta cikin gida wadda ma kusan sun dena,

Daga baya kuma mommy haka ta daure da yanayinta tana sanaoin SANAAH kuma ta koma itace a asibiti tareda Yaya Al'amin din.

Wata irin damuwa da qunci ne suka saka SANAAH ta fara wata rama da sake komawa wata irin me sanyi sosai da rashin son mutane da shakkar mutane sam bata iya ko zama cikinsu sbd rashin son hayaniya da tsoron abinda zai iya biyowa baya.

Sati hudu da kwanaki Yaya Al'amin yayi a kwance cikin jinya me tsanani kafin ya samu saukin da aka sallamosu suka dawo gida.

Ya rame ya zama kalar tausayi sosai dan kaman wanda yayi jinyar shekara ya koma ga yanayin rayuwar ya sauya musu ya dawo baya dan kuwa a yanxu suna cikin wani halin dasuke buqatan komawansa aiki sosai dukansu.
Sunada abinci da komai amma dai kudi kam sam babu sedai yan canjin da baa rasa ba.
#MAMUH
09033181070
[28/04, 12:49 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
Chapter 30 · 0% Book details