← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 154

Sashe 23

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda hannunta ya fito ne ya shiga idanuwansa da suka juyo garesu daidai lokaci daya yasaka ya dauke kallansa daga garesu gabaki daya a cikin nutsuwa da kamewansa tareda rashin sakewansa ya gaisa da mommyn ta sake masa godia ya dan yi magana da Al'amin akan kulawa dasu suka wuce hanya daban daban.
#MAMUH

GANIN IDO
1K
VIP 5K
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

23
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Suna fitowa daga asibitin taxi Al'amin ya tarar musu yafara budu musu cikeda kulawa suka shiga ya rufe tukuna ya zagaya ya shiga gaba suka bar gurin zuwa gida zuciyoyinsu da wani irin sabon yanayi na damuwa da kadaici da rungumar sabuwar rayuwarsu da kaddararsu yana shigarsu.

Ko bayan isarsu gida suna shiga Al'amin ya rufe gida babu wani zama ko abinda sukai kowa dakinsa ya nufa ya shige suka kwanta,

Washe gari tinda Asuba jirgin Raheem Jeerah da Maamah ya daga suka bar Nigeria bayan ya tafi yakaiwa kabarin dan uwansa ziyarar bankwana a jiyan.

Ya tafi bada niyar barin Maamah ta sake dawowa qasarba ta tafi kenan zata rayu a cikin danginta na yanzu wato mahaifiyarsa da danginta da suka karbeta hannu bibbiyu suka maidata tasu babu kowace shakka,

Ta tafi kenan babu abinda zata sake dawowa tayi a qasar da batada kowa tinda ba Nasir,
Sun tafi batareda niyar dawowa ba dan shi kansa baida sauran abin yi a Nigeria duk da yanada tarin dukiya a qasar da Nasir ne yake kulawa da ita amma ayanzu ta koma hannun wani.

Bayan wucewansu Al'amin dayaje asibiti tinda sassafe ya tadda harsun wuce sun tafi Maamah tabarsu itama kenan dan haka ya dawo gida ya sanarwa Mommy ta sauke ajiyan zuciya itama tana fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ga dukansu ya kuma bawa Maamah lafiya da danganar rashin Nasir da kwanciyan hankali.

SANAAH datake jinsu rufe idanuwanta tayi ahankali tana jin nauyin kirjinta na qaruwa amma ba kaman yanda takejin rashin Nasir a rayuwarta kwata kwata har abada na neman kashe zuciyartaba dan hakanne take ganin babu wanda bazata iya rabuwa dashiba tayi rayuwaba matiqar ta iya jure rashin Nasir.

Baa riga an daura aurensu ba amma tinda har a ranar daurin auren nasu aka kwantar musu da gawarsa gabansu jin kanta takeyi matarsa ita da aka riga aka daura aurensu tin ranar haihuwarta.

Kallan mace me takaba data rasa mijinta takewa kanta take kuma jin kanta,
Batada sauran walwala batada sauran jin zata iya son kowane irin namiji dan harta mutu babu namijin da zai sota kaman Nasir,
Bazata taba samun namijin dazai rasa kansa akan karfin sonta ba dan haka taji batada sauran shaawa ko buqata ga auren kowane namiji.

*****ba Morocco suka wuce da maamah din ba can qasarsa ya wuce da ita dole Dr Mum ta shirya ta bisu acan sbd yana buqatan Maamah din a kusa dashi.

Jinyarta aka fara yi cikin tsananin kulawa da kashe dukiyar da baama jinta ko kadan,

Dr Mum da Meenah harma da Fammah sune suke kulawa da ita cikeda wata irin kauna me tsanani da tattali da tausayawa.

Shi Raheem kwata kwata kaunar dayake mata kasa iya tsayawa yakeyi idan tana cikin halin tsanani sbd jikin ya koma yau lafiya gobe ciwo bata iya wata doguwar magana ta sauya kwata kwata ta koma me sanyi sosai da wata irin sabuwar kaunar Raheem mai tsanani sbd a yanzu shine kadai danta dan bata taba kallansa a matsayi daban ba da Nasir tinda itace uwar data shayar dasu su dukan,

Ta daure ta rungumi hakuri da kaddara ta sakawa kanta jarumta amma kuma zuciya na dauke da wani irin radadin rashin jini gudanta dashine kadai abinda ta mallaka cikakkiyar mallaka a duniya gashi ya tafi ko aure baiyiba bare bar mata gudan jininsa dazai rage mata radadin rashinsa.

A haka suka share wata daya a asibiti da ita kafin aka sallameta suka babban gidan Raheem din dake cikin birnin london.

Basu komaba anan suka zauna itada Dr Mum din shi kuma ya sake juyewa aikinsa rayuwarsa kaman yanda mahaifinsa yayi a baya dan haka kwata kwata ya sauya shima ya koma babu time saina aiki da zazzafan gwagwarmaya yaqin rashin tsoro a cikin ruwa dayake sake qamar dashi da na principles dinsa.

Mahaifinsa ma har lokacin yana qasar ya jima sosai yana jinya kuma yana basa kulawa shima sedai haryanzu basu zauna sunyi maganar rasuwar Nasir ba sbd dukansu kallan kansu sukeyi a matsayin wainda sukai sanadin rayuwarsa sbd ya rasa ransa ne akansu sbd du musamman Raheem din dayake ganin daya janye a lokacinda akace ya janye da Nasir bazai rasa ransa ba hakama daya janye kuma mahaifinsa ne zai rasa ransa tako ina jin yakeyi shine kusan a tsakiyar sanadin komai.

Sir hakeem jeerah dayake jinya a qasar sai ya saka kusan iyalansa suna kasar duka suma sun dawo qasar,matansa biyu da dansa daya Samad jeerah sai kuma wasu daga cikin familyn.

Tinda yake qasar dr mum na qasar basu taba haduwaba kuma babu wanda Raheem yakewa maganar dan uwansa ko maganar daya a gaban daya sbd alaqace da tini ta zama yankakkiyar da babu sauki a ciki kuma ya jima da karban hakan tin yan yaro kuma ya saba ya zaunu a cikinta harta zama ba sabuwar abu ba saima hakan dayafi komai sauki babu hayaniya acikinta.

Bayan warkewansa bai koma Nigeria ba anan yaci gaba da zama da iyalinsa har tsawon lokacinda kwatsam rasuwar mahaifinsa Alh farouk jeerah ya sakasu tattarawa su koma Nigeria dukansu.

Hadda Raheem suka taho sedai irin halinda ya shiga na dawowan sabon kuncin da mahaifinsa ya sheda na rashin dan uwansa da tina rayuwarsu ta baya ya saka Sir jeerah da shima yake jin wannan nauyin na yanda rasuwan Nasir din tazo ya kallesa ya yafe masa zuwa Nigeria harsai lokacinda yaji rasuwar Nasir ta rage wannan zazzafan radadin a rayuwarsa dan yasan a yanxu kam Raheem bazai taba iya sauka Nigeria ba bai shiga mummunan halin rashin ba tinda shine ya rufesa a qasar da hannuwansa kuma sun kasa cirewa kansu nauyin mutuwar.

Raheem bai taba tsammanin hakan daga mahaifinsa ba dan haka yayi masa godia sbd tabbas bayajin zuwansa Nigeria zai ringa basa nutsuwa bayan dawowan sabon kuncin da baida magani.

Da wannan ya samu damar barin Nigeria kwata kwata bayan kaiwa kabarin Nasir ziyarar bankwanan karshe.

Bai sake kwanaki ba a qasar ana gama adduar sati biyun rasuwar Alh tsoho farouk ya tafiyarsa ya koma inda rayuwa zata cigaba da tafiyar masa cikin kwanciyan hankali.

Shi kuwa Sir hakeem jeerah ya dawo kenan bayajin zai sake zuwa wata qasar zama ya dawo kenan har abada shi da wata qasar sedai ziyara ko hutu ko business ko taro ko dubiyi kokuma ganin likita idan ta kama dan haka sabon tsari da suna da iko da wata irin power ta budewa familyn JEERAHs da koyaushe daularsu da daukaka da suna da power dinsu ke sake habbaka musamman yanzu dayake juya manya a hannunsa sbd kowa so yake ya rabi power din dayake da ita.

Shi kuwa Rear Admiral Raheem jeerah rayuwa a sabon matsayi da sabon tsari ya fara bayan shekara daya Maamah ta koma Morocco dan Dr mum ta koma bayan watanni ita tini dan haka maamah na komawa suka kama rayuwarsu da ajiye komai sbd acan Nigeria ma sunyi kokarin contacting su mommy amma sam babu komai sun rasa komai na contacting nasu hakama acan din sunyi kokarin nemansu amma sam babu kowane labari sun bace bat dan haka suka hakura suma suka kama sabuwar rayuwa dan sun dawo daidai a yanxu suna walwala da farin ciki da komai tinda dabia ce ta dan adam.
#MAMUH
#BEST STORY
#BEST LOVE
#FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH
#SANAAH KHALIL
#MEENAH WAHAB
#SAMAD JEERAH
#SIR HAKEEM JEERAH
#CRAZY LOVE
#FAMILY THRILLER

GANIN IDO
Mamuhgee
1k
Vip 5k
09033181070
[09/05, 4:20 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
Chapter 23 · 0% Book details