← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 154

Sashe 61

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu wani damunsa da zaayi yana bangarensa hakama ai mu munyi kewan hayaniyar ai tinda ba yawa ne damuba acan sannan gaskia su barki ki dan huta wa hayaniyarsu ta dan lokaci so kawai su shirya su koma can"

SANAAH data rasa kwanciyan hankalinta lokaci daya kallan Mum din ta dago tayi ta bude baki da kokarin hana kanta bayyanarda tashin hankalinta na maganar tace

"Dad ne bazai barni ba ai sbd ya hanani kwana ko ina tin da dadewa"

Kallanta Mum din tana murmushi tace

"Kada ki damu da hakan ok my baby"

Shiru SANAAH din tayi tana jin kaman zata rasa nutsuwanta dan kuwa bazata iya komawa can bangarenba sam bama zata taba yadda ba.

Daga nan tata firar ta qare ta silale tayi kitchen ta sakawa aikin Safiya hannu sunayi suna tasu firar.

Anan Mum tayi dinner dinta tareda su sai dai aka je can aka jere masa nasa a table.

Da daddare gabaki dayansu su uku hadda Mum din suka nufi gurin Dad gaidasa SANAAH tana dauke da tea dinsa.

Suna shiga cikin rashin Saar SANAAH Fleet na bangaren gurin Dad dan suna shigowa dukkaninsu sukaji qamshinsa dan haka SANAAH tayi ma baya a gurin shiga tana qin dagowa sosai.

Gurin Dad ta nufa gefensa daga qasa ta zauna a natse tana ajiye tray din hannunta akan table.

Gaidasa tayi ya amsa yana kallanta da wata irin kauna da kulawan da bai hada da amsa gaisuwan sauran ba.

Mum itama cikin girmamawa ta gaidasa ya amsa itama cikin kulawan kafin ya amsa ta Fammah da itama yake jinta har cikin ransa ya ambaci sunanta da nutsuwa.

Daman Mum din data shigo mijinta tafara yiwa magana hakama fammah Dad dinta tafara gaidawa.

Kafin a fara kowace magana kaman daga sama sukaji Mum tace

"Dad daman su fammah ne nace su koma bangarenmu da zama kafin mu tashi komawa sbd itama Mommysu ta dan huta daga hayaniyansu so SANAAH tace ka hanata zuwa koina da zama acikin gidan shine nake rokan abarta su koma can din tareda fammah"

Daga Dad din har SANAAH da Fleet tsit sukai cikeda wani irin mamaki da jin zancen kaman shock sbd abune da babu wanda a cikinsu yayi tsammanin ji daga bakinta dan haka Dad datake wa zancen shiru yayi tareda kafeta da kallan nutsuwa kafin ya dago ahankali ya kalli inda RAHEEM din yake zaune shima yana dago nasa idanuwan a natse ya saukesu akan Meenah din kafin ya daukesu yana qin kallan Dad.

Murmushin manya Dad ya sake yana dan mayar da bayansa a tsanake yana maida idanuwansa akan SANAAH wadda tayi qasa da kai cikin damuwa da dacin kirji ya bude bakinsa yace

"Babu damuwa a hakan ta tattara ta koma din ni nace"

Sake qasa da kai SANAAH tayi tana jin jikinta na mutuwa gabaki daya sbd batada zabi akan duk abinda Dad din yace.

Da farin ciki sosai Mum tayi masa godia harda fatan qarin tsawon rai da lafiya mai dorewa.

Sallamarsu Dad yayi yace su tafi suje suyi shirye shiryensu kawai.

SANAAH ce tafara miqewa ta a sanyaye ta nufi kofar ta fice kafin su Fammah din suka fito.

Danne tsananin damuwan data shiga take tayi tana dan yaqe cikin tsananin karfin hali a lokacinda suke tafiya Mum din na mata magana da farin cikin shikenan yanxu ba kowace sauran abinda zai hanasu dawowa gurinta dan tana buqatan hakan.

Rabuwa sukai a hanya ta nufi bangaren mommy su kuma suka wuce can din,

Tana isa palonsu dakatawa tayi tareda dan dafe goshinta tana jin kaman zata fasa kuka idanuwanta na sauyawa sosai.

Mommy dake zaune da mamaki ta kalleta tace

"Yaya dai?
Me yake faruwa??

Zaunawa tayi a hankali kan kujera tana sanar da ita abinda ya faru.

Shiru tayi itama cikeda rashin jin dadi sbd harga Allah batason abinda xaije ya dawo ya zama matsala babba amma kuma tinda har maganar takai gurin Dad kuma yace aje babu yanda zasu iya dole sai hakuri.

Miqewa tayi ta shige dakinta ta nufi toilet ta shige ta jingina da kofa tana rintse idanuwanta saida wasu siraran hawaye suka gangaro mata taji dan nauyin daya danne kirjinta ya fada.

Bayan ta fito xaunawa tayi bakin gado tana dan dafe kanta.

Acan ma gurinsu Dad bayan ficewansu babu abinda Dad yacewa Raheem wata maganar ma ya janyo musu sbd yasan shima Raheem din bazai taba cewa komaiba tsabar miskilanci.
##MAMUH
09033181070
[10/05, 10:43 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

58
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Sai dare sosai bayan fammah ta gaji da jiranta akan kayan baccin sakawanta da zatai shirin bacci ta biyota tukuna suka hada kayansu a luggage biyu Safiya taja musu suka fice.

A cikin iyayenta fammah tayi fira sosai har daren ya qara yi tukuna taje nemo SANAAH din dan Mum ta dauka ma sai goben SANAAH ita zata taho so koda suka dawo da fammah already sun shige itada Dad din.

Bedroom din fammah din suka shiga Safiya ta tsaya fira tana jere musu kayansu a closet tana tsokanarsu da cewa gari yana wayewa zasu fara kewanta.

Firan sukeyi fammah na dan jin ciwon ciki kadan kadan dan haka taje tayi wanka tazo tayi shirin bacci ta kwanta take bacci ya dauketa cikinta na dan ciwo.

Itama SANAAH wankan tayi bayan Safiya ta wuce tayi shirin bacci ta rage hasken dakin sosai taxo ta kwanta.

Tsakiyar dare sosai wani irin mummunan ciwon ciki mai tsananin gaske ya tada fammah kaman zata mutu.

Tsoro mai tsanani da tashin hankali SANAAH ta shiga dan haka ta janyo wayar Fammah din ta bude ta nemo numbern Mum ta saka kira jikinta na dan rawa sosai sbd tashin hankali da tsananin tsoro ganin yanda famman keyi kaman zata rasa ranta.

Har wayar ta yanke baa daga ba dan haka ta sake saka kiran tana rungume famman a jikinta wanda duka jikinta yake neman saki.

Cigaba da danna kiran tayi dayake wayan na silent ne sai a kusan kira na tara sai Mum din ta daga cikin bacci tace

"Yes fammah"

Jin muryan SANAAH da abinda ta fada ya sakata bude idanuwanta gabaki daya gabanta na mummunan faduwa.

Tashi zaune tayi tana yaye lallausan rufan dayake jikinta ta ziro kafafunta qasa batareda tayi tinanin ko tada Fleet ba ta nufi kofa ta fice da wayarta a hannu hankali tashe kafafunta na rawa dan kuwa tsananin son datakewa 'yarta ya wuce yanda take son rayuwarta komai zai iya samunta idan ta rasa fammah.

Hankali tashe ta iso dakin sanye da wasu kayan bacci riga da wando har qasa masu kyau da suka kwanta a jikinta.

SANAAH na dago idanuwanta kallo daya tayiwa Mum din ta sauke idanuwanta cikin damuwa sosai ta sake tallafo fammah din daga jikinta idanuwanta sunyi jajir hawaye na neman fitowa daga cikinsu.

Da sauri Mum ta iso gadon tana kamo fammah da sauri da tashin hankali tace

"Meya faru?
Meya sameta?
Me taci??

Wasu hawaye ne suka fara gangarowa SANAAH ta girgiza kai tace

"Bansaniba kawai ciwon cikin ne ya tadamu,muje asibiti pls Mum"

A rikice Mum din ta sake tattaro Fammah jikinta kafin tace komai famman ta feso wani amai a jikin kayan SANAAH mum na ganin hakan ta sake jan bayanta da karfi wani aman ya sake fitowa.

Saukowa sukai da ita gadon tana sake jin wata azabar.

Fita mum tayi ta nufi bedroom dinta ta hado wasu magani acikin kayanta dan bata rabo da yan maganin buqata ta tinda tasan aikinta.

Tana dawowa maganin ta bude SANAAH taje kitchen da sauri ta dauko warm water ta kawo suka bawa Fammah din daqyar tana juye juye.

Tashin hankali da firgici suka fuskanta a tsakiyar daren batareda sanin kowaba dan ita SANAAH tsoro ta shiga sosai na ganin yanda famman keyi itama Mum din ta fice hayyacinta amma sbd batajin akwai likitan dazata iya barwa duba famman tinda itama karatun datai kenan yasakata kafewa akan dubata din tana bata taimakon da suka kamata har kusan asuba tukuna ciwon ya fada Mum ta kamata itada SANAAH din suka maidata dakin Mum sbd Dakin nasu ya hargitse.

Wani bacci mai karfi ne ya dauke Fammah din take dan haka a tare suka sauke ajiyan zuciya idanuwan SANAAH sunyi jajir tayi kuka harta gaji wanda sai lokacin Mum ta dan rungumeta tana rarrashinta da kulawa tukuna tace taje tayi wanka tayi sallah saita kwanta tayi bacci sbd shikenan kuma insha Allah famman ta samu sauki.
Chapter 61 · 0% Book details