← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 154

Sashe 63

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kadai ne a table din sedai ko fara serving dinsa Mum bataiba Fammah ta qaraso dining din jikinta ba qwari sosai amma ta warke kalau bata jin komai bayan kasalan dan hakane ma tana farkawa kusan after 9 kadan tayi wankanta ta saka kaya marasa nauyi ta fito cin abinci sbd samum karfinta ya dawo ganin SANAAH na bacci har lokacin ya saka bata tada itaba ta kyaleta tan tasan tana buqatan baccin tinda basu samu sunyiba da daren a sanadin ciwonta.

Gaida Dad dinta tayi wanda yake kallanta da kulawa mai nutsuwa kafin ya miqa mata hannunsa ta kama tana dan dawowa gefensa ya shafa kanta yana mata sannu da fatan sake samun lafiya mai dorewa.

Breakfast dinsu suka fara sai a lokacin Mum ta dago ta kalli Fammah tace

"Ina Baby SANAAH?
Meyasa bata fito breakfast ba??

Cikin rashin iya daga murya Fammah tace

"Tana bacci haryanzu sbd kinsan sam bata rintsa ba cikin daren kuma yanzu sai kiga tafara zazzabi sbd hakan coz she's too sensitive"

Shiru Mum din tayi tana cewa

"Bare kin daga mana hankali sosai fa a jiyan tayita kuka dole ma zatai ciwon kai"

Shiru suka sake yi kowa na cin abinci a natse har suka gama babu wanda ya sake cewa komai suna baro dining room din kai tsaye fammah daki ta koma gurin SANAAH ta kwanta itama Mum kuwa mijinta tabi zuwa palonsa sika koma.

Bayan kusan awa daya sai ga Imran na knocking kofar palon farko maana main sitting room din tareda budewa ya shigo da wata sabuwar qwararriyar likita itama halfcast ce ya nuna mata guri ta zauna ya daga wayarsa bai kira Fleet ba sbd sanin abinda yakeyi kai tsaye Fammah ya kira.

Tana dauka ya mata ya jiki ta amsa a dan natse kafin yace

"Ga Dr zata duba ku tana sittin room zaune"

Dan shiru tayi tareda kasa fahimtar kalmar "ku" daya ambata sai ta juya a natse ta kalli SANAAH takai hannunta ta tabata taji jikinta yayi wani irin zafi sosai ta kalleta da dan sauri tana mamakin da gaske dai batada lafiyar itama.

Batada kowace irin doguwan nazari da hada lissafin tinanin komai na rayuwa wanda hali ne da Mum dinta data gado dakyau dan haka batai tinanin komai ba na yanda Imran ya saniba ta kalli wayarta tana gyara zamanta a kunnenta tace

"Gamunan fitowa SANAAH dince ba lafiyan yanzu sosai"

Kashe wayarta tayi tareda son tada SANAAH din amma kuma sai ta fasa ta sauk gadon ta fita zuwa sitting room din.

Tana isa gaisawa da Dr din sukai cikin yar kokarin riqe kuzarinta dayake dawowa tace su tafi can daki ta duba SANAAH din.

A bakin gado ta zauna tareda dan miqa hannu ta yaye rufar SANAAH din tana sake taba jikinta zafin sosai yana nan dan har wani hucin zafi ne ya fito daga rufarta data yaye.

Sake shafata tayi tana ambatar sunanta da sanyi.

Ahankali ta bude idanuwanta bayan ta farka daga baccin datakeyi din.

Bata motsaba idanuwanta kawai ta sauke akan fammah din tana jin karfin zazzabinta na qaruwa.

Sanar da ita Dr zata dubata fammah tayi da kulawa tana taimaka mata ta tashi zaune.

Kallan dr din tayi tareda bude baki cikin dauriya ta gaidata tana kallanta.

Dr tasowa tayi ta iso gurin SANAAH din fammah ta bata guri ta zauna gefen gadon tana fara dubata da tsananin kulawa da yan tambayoyi.

Yanda SANAAH din takeda sanyi da rashin sauri ko hayaniya a komai bare yanxu datake cikin tsananin zazzabin ya saka suka dauki time kafin suka gama tukuna ta duba Fammah itama wadda ta sake jinta ta warware sosai batajin komai.

Bayan lokacinda Dr ta bata mai tsayi ta wuce SANAAH ta samu ta sauko gadon ta isa bathroom ta shige tayi brush da sauran abubuwanta kafin tayi wanka da ruwan zafi sbd taji ko zata samu karfinta da abinda takeji na zazzabin ya sauka.

Tana fitowa sama sama ta iya dan shafa body mist na oud mai sanyi da tsada ta saka silk riga da wando marasa nauyi ko kadan ko bra bata iya sakawa ba tasha tea kadan akan tirsasawan Fammah tukuna tasha magani ta koma ta kwanta sbd kanta tsananin ciwon gaske yakeyi.

Tana kwantawa bacci ya dan sake daukanta fammah ta kashe mata wayarta sbd kada a bata kowace irin hayaniyar da zata hana ciwon kanta sauka.

Mum kuwa jinsu shiru ta fito tana waya ta nufa dakin ko data shiga taga halinda SANAAH take ciki dan haka ta nuna damuwanta da kulawanta itama dubata tace su bawa SANAAH din isashen hutunda har sai ciwon kanta ya sauka kada a bata kowace hayaniya.

Fitowa sukai suka barta bayan ta sake samun bacci,
Fammah bangaren Mommy ma takeson tafiya dan tabar SANAAH ta samu hutun itama taje can ta kwanta tayi hutunta acan.

Mum ma gurin Rabin ranta ta wuce acan take sanar masa SANAAH din ba lafiya sosai kaman Dad ne ya aiko Likita ta dubata sedai sai ahankali jikin nata kila zuwa yamma ta warware.

Baice mata komaiba wayarsa dake hannunsa yake ci gaba da dubawa batareda bawa zancenta hankalinsa ba kokuma alaman yamasan abinda take fada.

Safiya ce ta shirya musu dining da rana sukai lunch guraren karfe uku da mintina kafin suna gamawa Mum ta sake zuwa ta duba SANAAH dake bacci har lokacin bayan tayi sallan azahar daqyar ta koma ta sake kwanciya da rufe jikinta duka.

Ganin bacci take ya saka Mum itama barin bangaren bayan Safiya ta sake tattara komai fes ta bar bangaren itama.

Gurin Mommy ta tafi suka baje suna firarsu bayan ta sanar da mommyn SANAAH insha Allah taji sauki tana tashi lafiya kalau zata tashi.

Mommy ma sbd kara bata damuba firar su sukeyi hankali kwance da shagala gashi daman duk taxo bangaren sai dare ko magrib take komawa.

Sunacan sunata firarsu fammah ma bacci me nauyi ne ya dauketa bayan azahar dan baka babu wanda ya sake zuwa dubota.

Bayan sallan laasar wata kishirwa da yunwa mai tsananin gaske ta tada ita daga baccin bayan dan zazzabin ya dan saukar mata dan haka ta farka tayi shiru tana jiran zuwan wani dan tana tsananin buqatan ruwa tasha amma me dumi takeso sbd yanda takejin kaman zatai amai.

Shiru babu wanda ya shigo dakin dan haka ta tashi zaune ahankali da tsananin rashin karfi da da jiri sosai sbd rashin komai a cikinta.

Idanuwanta da sukai wani irin laushi da bayyanarda wata irin kasala da lumshewa akai akai ta juya ahankali ta kalli dakin dayake da rashin haske sosai da aka rage mata taga ba alaman fammah bata ciki dan haka ta hadiye wani numfashi mai tsananin kasala tareda yunkurawa ta yaye duvet din jikinta ta ziro kafafunta qasa tareda dan rufe ido ta bude ahankali tanajin kaman bazata iyaba amma yanda takeji kaman zata mutu ne idan bata sha ruwaba.

Miqewa tayi tana dan dafa bango ta zira soft slippers a kafafunta tukuna tafara takawa ahankali tana rufe idanuwanta da dan dauriya tana budewa jiri takeji sosai da amai na neman yunkuro mata amma haka ta isa kofar bedroom din ta fice.

Palo ta nufa tana tafiya ahankali tana dan dafe cikinta kadan da hannu daya tana barin dayan dan bawa kanta kariyar daga duk inda zata fadi sbd jirin dayake dibanta.

Kai tsaye hanyar kitchen ta nufa bayan bayan ta isa palon,

Tana isa kitchen bata rufe kofar ba ta dakata ahankali tareda dafa kitchen island tana rufe idanuwanta tana fidda numfashi ahankali da ajiyan zuciyan abinda takeji.

Dakatawa tayi tsawon mintina saida ta dan samu sassauci tukuna ta iya daga idanuwanta da suka sake laushi sosai ta janyo electric kettle takai bakin fanfo ta kunna ruwa ya shiga ta kashe ruwan ta jona kettle din tana yin baya tareda da dakatawa ta dan huta kadan daga muguwan mutuwan jiki da kasala da rashin karfi ko kadan.

Numfashi ta dan sake saukewa tukuna ta daga kafafunta har lokacin tana jin jiri ta isa inda fridge yake takai hannu ta bude daqyar tukuna ta saka hannunta daya ta dauko yoghurt dayake ciki ta zuba a cup hannunta na dan neman gazawa ta mayar tareda kai glass din bakinta tasha da wani irin sanyi dayayi sosai.

Bata gama shanyewa ba wani irin amai ya yunkuro mata gabaki daya dan haka cup din ya subuce daga hannunta tayi sink din kitchen da sauri tafara fesa wani irin amai mai sautin yunkurin gaske sbd babu komai a cikinta sai yoghurt din daya shiga cikinta yanzu din.

Wani azababben yunkuri da kakarin amai takeyi mai sauti sosai da tana neman jin kaman zata mutu idanuwanta sun gama bayyanarda azaba take cikinta.

Tsit babu kowa a bangaren dazai jita bare bata taimakon datake tsananin buqata dan ta fita hayyacinta take.

Dawowansa kenan tin bayan daya fita sallan laasar sbd ya dan tsaya ya gaisa da mutane da har ya dan jima kafin ya dawo din.

Yana shigowa palon kafin ya doshi hanyar wucewa nasa palon sautin yunkurin aman ne mai karfin gaske ya fara shiga kunnensa daya sanyasa dakatawa cak daga inda ya dosa sbd a tinaninsa da saninsa babu kowa a bangaren dukan su suna can kuma yanda yaga Meenah din na yi sai dare ko yamma sosai dan haka a natse ya juya zuwa kitchen din cikin takun tsanaki.
#MAMUH
09033181070
[12/05, 9:16 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
Chapter 63 · 0% Book details