← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 154

Sashe 11

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta fammah dake kwance tana dan fahimta da jin wasu abubuwan tausayin fatima tafara yi ganin irin wahala da dawainiyar datake fama da ita a cikin kwanakin da suke tafiya na jinyarta da fama da jarirai guda biyu dama kuma ita kanta da jegon takeyi amma ba wanda ya tina da hakan.

*****wata irin jinya me nauyi da azaba da mawuyacin hali fammah takeyi da babu sauki a cikinta,

Babu daren da bata wani irin kuka mara sauti da taba zuciyar me kallo dan hakanne itada fatiman suke zaunawa suyisa a tare zuciya da gangar jikin kowannensu tana quna,

Fatima rayuwa tayi mata wani irin nauyi a dan lokacin sbd itama lafiyar neman gagararta takeyi sbd jikinta dayake danye amma wahala da dawainiya babu wadda bata yi.

Fammah na cikin mummunan qunci da baqin ciki da dacin zuciyar da takejin kaman zata mutu ne tabar duniya,

Iyayenta na can a cikin mummunan halin jinyar Amminta datakejin kaman bazasu hadu ba hakama mahaifinta tasan yana gap da kwanciyar shima matiqar jikin mahaifiyarta na sake rikicewa a kowane lokaci hakama nata jikin,

Koyaushe ya kirasu kwarin gwiwa yake bata yana danne dacin halinda yake ciki yana tabbatar mata da indai fatima na tareda ita hankalinsu zaici gaba da kwanciya suyi jinyar Ammin dakyau.

Hakeem ma fatima ce wadda ke saka zuciyarsa dan samun qanqanuwr nutsuwa akan fammah wadda a yanxu ta sallama ta cire rai daya rayuwa kwata kwata mutuwar kawai take jira.

A lokacinda akaiwa RAHEEM HAKEEM JEERAH nadin sunansa a tare da dan fatima akai musu yanka da komai akai musu yankan ragunan suna da shanu akai sadakarsu gabaki daya.

Tinda akai yankan sunan babu wata hidimar sunan da zaayi sbd jikin fammah dake kwance har lokacin.

Satinta uku a asibiti harda kwana hudu anata fama jinya ba sauki kafin aka sallamota tareda shawarwarin likitoci akan kada a fita da ita wajen da akeson fiddata a yanzu sbd yin tafiya da ita zai iya janyo matsalar da zaa iya rasata ayi hakuri ayi jinyar a hankali idan tayi healing ko yaya ne sai a fita da ita.

Wannan shawarar dole aka dauka aka dawo da ita gida aka bude babin jinyar da baa gane komai sbd tinda fammah tasan abinda ya gama samunta a ranar ciwonta dawowa yayi sabo sbd tashin hankalin da kowa ya shiga sai data sake kwana biyu a kwance bata san inda kanta yakeba tukuna ta farfado.

Farfadowanta sabo ya dawowa da fatima jinyarta sbd ko ruwa ake bata dawowa sukeyi,

Fammah dake rashin lafiyar da fatima dake jinyar a tare suke wata irin mummunan rama da bushewa da tsiyayewa sbd halinda kowannensu yake ciki,

Fatima ga nata rashin lafiyar dake cinta,ga jarirai biyu da dawainiyarsu ta tsayar da rayuwarta cak guri daya musamman Raheem da har lokacin ya kasa sabo da shan madarar kuka da wuya yake a cikinta wadda tafara sakasa rashin lafiya mai karfi,
Sannan ga jinyar fammah da itace wanketa itace shiryata itace bata abinci duka a kwance ga damuwan rayuwarta datake ciki da danta dama ta fammah duka.

Ta fige ta lalace ta zama kaman me qanjamau babu sauran kowane jin dadi a rayuwarta.
#MAMUH

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

11
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
Ahankali ahankali suke tafiyar da rayuwarsu cikin damuwa da dacin jinyar da a yanzu wata uku ake magana kuma har lokacin fammah na jinya sosai sedai ta samu sauki tinda tana zama yanzu hakama tana cin abinci batareda ya dawo ba kuma tana magana sosai sedai babu karfi a tattare da ita da kuzari har lokacin,

Raheem ya koma mara lafiyar kwata kwata shima sbd yunwa data kamasa anyi yawon likitoci dashi har an gaji sam ya kasa zama cikakken lafiyayye dan haka ne aka dawo da kokarin ganin ko zai samu nono ne daga mahaifiyarsa amma a banza sbd koya samu din baida wani amfani sbd kadan ne kuma ita batada lafiyar samun kuzarin shayarwa.

Gabaki daya farin cikin samun Magajin jeerah komawa ciki yake kokarin yi sbd ganin halinda Raheem din yake ciki dan haka suka duqufa nemawa uwarsa lafiya dan ta samu dama da lafiyar shayar dashi.

Suna shiga wata na hudu Hakeem jeerah ya dawo Nigeria garesu dawowan da zai jima bai komaba kuma dawowan da zai jira kiran qarin matsayinsa da zai qarasa sauya rayuwarsa gabaki daya kuma ya qarawa ahalinsa suna da matsayi a idon duniya.

Fatima tafi kowa farin cikin dawowansa sbd halinda fammah take ciki da suke cire rai koyaushe daga tashin kowace safiya.

Dawowan hakeem ya saka fammah fasa kuka a gaban wani karan farko idan ba fatima ta rokesa ya kaita qasarta gaban iyayenta tayi jinya idanma batada rabon tashi ta cika a hannun iyayenta.

Shi kansa ya girgiza da mummunan ganin da yayi mata da mummunan labarin daya tadda wanda ya saka ya rasa ina zai saka kansa ga Raheem ma sai ahankali.

Irin yanda ta daga hankalinta da son komawa gida jinya ya sakasa fara tinanin amincewa amma ganin Raheem, ai iya rasa ya saka ya raba tinaninsa biyu iyayensa kuwa take suka kasa aminta da hakan.

Ita kanta a lokacin tana tsananin tausayin Raheem dan haka ta yanke hukuncin daya girgiza fatima da hakeem a lokacinda ta fada musu buqatarta.

Fatima dataji zancen kaman a mafarki zubawa fammah idanuwanta tayi shi kansa Captain Hakeem kafe fammah yayi da idanuwansa fararen da suka sauya yana mata kallan tausayi sbd tsoron ko ciwon ya taba kwakwalwanta ne.

Hawaye ne masu zafi suka gangaro mata batareda jin komai ko shakka ko fargaba saima kara jin yadda da hakan datake yi sbd tasan ko bata rayu ba Raheem dinta bazaiyi maraicin uwa ba matiqar fatima na raye dan hakanne ma ta yanke shawaran bawa fatima Raheem ta shayar mata dashi nononta.

Kasa yadda da hakan Hakeem yake kokarin yi amma yanda ta gama kashe masa jiki da wani irin kuka da maganganun da suka sakasa tsoro ya saka ya kalli fatima wadda idanuwanta sukai jajir batada zabi sai wanda suka zabar mata.

Hakeem dinne ya kalleta da nutsuwa da qasqantar da kai dan bata haqqinta na raayin zatayi ko bazatayi ba ya roketa hakan.

Fammah ma zuba mata ido tayi cikeda tsananin kaunar ta kasance wadda zata shayar mata da Raheem kada ya rasa ransa.

Batada zabin daya wuce yin duk abinda zai kawo sassauci da abinda akeso a rayuwar fammah da Raheem dan haka ta amince.

Amincewanta ta kawo sauyi me girma a rayuwar Raheem da iyayen nasa harma da Familyn jeerahs da babu wanda yasan abinda yake faruwa sbd daga fammah sai mahaifinta da Hakeem ne kadai suka san fatima na shayar da Raheem da Nasir a lokaci daya sedai kawai aka ga Raheem na samun lafiya yana warwarewa yana jiki yana zama babyn da suka jima suna tsananin son ganin yana zama.

Kulawa sosai Hakeem yake bawa fatima da fammah sbd dukansu suna buqatar kulawan.

Lokaci yaja samun lafiyar Raheem da fara wayonsa ya saka Zuciyar Mahaifiyarsa samun nutsuwa da amincin data kasa samu tin haihuwansa sbd tsoron rasasa,

Hakama samun lafiyarsa ya saka walwala da farin cikin ahalin jeerahs dawowa gabaki daya anata hidimarsa da nuna masa zallan gata da kaunar daya saka yanxu mahaifinsa ake tsananin tausayi ya qare a gurin jinya da kulawa da matarsa baida walwala baida farin ciki masu aiki ne da fatima ke kulawa dashi abinda bai kamata ba sam dan haka kai tsaye kaman saukan aradu iyayensa suka nemasa suka basa umarnin sake aure sbd samun mai kulawa dashi yanda ya kamata kafin samun dawowan fammah daidai tinda lokaci yaja sosai babu wani cigaba.

Da farko tashin hankalin maganar yaji amma daga baya saiya fahimtar dasu sam baya buqatan hakan musamman tinda shi din ba mazauni bane kada ya tarasu ya tafi ya barsu.

Sam Alh babba Ahmed bai yadda da hakan ba sbd babu wani uzurin daya wuce ya auro wadda ba iya shi kadai zata taimakawa ba hadda ita kanta fammah din.

Kasa fadawa kowa maganar yayi sbd yasan qarin aure garesa a yanxu ba abinda yake a tsarinsa bane tukuna musamman a yanzu da fammah ke jinya irim wannan amma yasan bazai kuma iya kauce hukunci idan iyayensa suka yanke ba.

*****Maganar qarin aurensa ta saka yaji yana son kai fammah din gida yanzu sbd kadama taji kota sani gwara ta tafi daga baya idan ta samu lafiya zai sanar mata sbd lafiyarta.

Su kuwa iyayen nasa babu bata lokaci aka fara shirin hadasa aure da daya daga cikin yan uwansa amma kowacensu nada maneminta kuma suna son juna dan haka aka ba bata lokaci kuwa aka hadasa da yar Ambassador Nuhu Sultan.

Auren gata da gata ne zaayi musu dan haka tin a gurin neman auren maganar ta fara bayyana a duniya tana yaduwa.

Fammah da fatima duka basusan abinda yake faruwa ba anata hidima da shirin yin auren wanda Sam ba wata hayaniya zaayiba sbd kada a tada hankalin fammah.

Tinda kwanakin bikin suka matso fammah ta fara rasa gane kanta sbd zuciyarta da lafiyarta dataji suna nauyi dan haka tayi sanyi ta rage kuzari sosai.

Fatima ma da tini ta zama uwar yan biyu ganin yanayin fammah sai ta dauka jikin ne ya dawo tinda yanzu haka yakeyi gashi a lokacin su Raheem din sun wuce shekara daya sosai biyu suke neman cikewa dan haka yayesu daga nono take kokarin yi har lokacin babu wanda yasan Raheem na shan nono.

Ana saura sati daya daurin auren Hakeem daya rasa inda zai saka rayuwarsa gurin sanar da fammah sai gashi kwatsam ta samu labarin daga bakin mai aikinta ta amanarsu itada fatima wato saratu.

Fammah sam bata yadda ba sbd tasan abune da bazai taba yiyuwa ba daga Hakeem dinta da bazai taba mata kishiyaba sbd sanin baa yimusu kishi hakama a daidai lokacinda take cikin wannan mummunan halin na jinya me wuya sama da shekara ga mahaifiyarta data rasa har abada itada haihuwa sedai kallo.
Chapter 11 · 0% Book details