← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 154

Sashe 139

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dauke idanuwansa yayi shima daga kanta yana cigaba da magana da Maamah kafin Dr Mum itama ta shiga zancen nasu Mommy kuwa barin gurin tayi kafin SANAAH ma ta miqe tabi ta dakinta suka basu guri dan suyi magana da kyau.

Anan yayi breakfast kafin ya fice bai dawo gidan ba sai yamma wanda a wannan daren ahalin Jeerahs din suka taho gidan Abbu a karo na farko bayan shekaru masu yawa neman aure a karo na biyu.

Fleet Raheem jeerah da Abbu ne suka sake bawa jeerahs auren Dr fammah a karo na biyu wanda su Dad din suka nema kuma a daren suka biya sakakinta wanda Raheem ya amsa da hannunsa.

Neman auren ya tafi a al'adar Moroccon dan kuwa hadda zinari suka gabatar wanda duka anyi wannan al'adar a daren an gama batareda kowace hayaniya ba bakuma tareda sani ko gayyatar kowa dan shedawa ba bayan iya su din.

Koda gari ya waye da wata nutsuwan da bai taba samun kansa ba Dad jeerah ya tashi gashi har lokacin tin a Nigeria rabon daya sake sakata a idanuwansa dan haka a cikin yunwar ganinta idanuwansa da ruhinsa suke.

Ita kanta SANAAH bata koma gurin mijinta ba anan ta kwana cikin gida dan haka ko washe gari ko kayanta bataje dauka ba zamanta tayi anan sedai aka neman mata wasu kayan tana sakawa bai kuma ganinta ba.

Hidimarsu kawai sukeyi dik da babu komai da akeyi jiran jibi kawai sukeyi a daura auren wanda anayinsa zasu kwasa su koma gabaki dayansu.

A cikin kwanakin biyun haka Maamah ta ringa kulawa da komai nasu itada Mommy sbd ita kam batada ma wani moriyan dan kuwa batada kowace kuzarin aikata komai ta saba da shagwabarta da yanda yake mata basa aikin komai sai bata kulawa da tarairayanta.
#MAMUH
09033181070
[23/06, 4:24 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

138
Washe garin ranar da zaa daura auren da wata irin nutsuwa da farin ciki mara hayaniya ko kadan dukkaninsu suka tashi duk da basa jin abinda daga Dad din har Dr Mum sukeji amma farin ciki ne mai dukkanin nutsuwa sukeji da jin kaman yau zaa sauke wani nauyi a cikin kirjin kowannensu.

Karfe 11 da kusan arbain su Dad jeerah suka iso masalaccin gidan wanda daidai lokacin shima Fleet Raheem da Abbu suka iso ciki tareda dukkanin mutanen da zasu halarci daurin auren wanda zaayi bame hayaniya komaiba.

Karfe 12 daidai aka daura auren wanda ana gamawa Abbu ya sauke ajiyan zuciya yana yiwa Allah godiyansa da Allah ya kuma nuna masa wannan ranar daya yanke rahama da gani.

Shi kansa Raheem shiru yayi kafin ya dago ya kalli mahaifinsa wanda idanuwansa suka sauya zuwa jan da jarumtarsa da kaifinsa suka boye abinda yake ji a kirjinsa da zuciyarsa na saukan wani nauyi mai nauyin gaske daga kirjinsa daya sakasa sauke ajiyan zuciya guda uku a jere cikin nutsuwa da kwanciyan hankali tareda kamewa.

Daga can aka watse batareda kowace doguwan taro ba dan haka koina ya koma daidai musamman da akai sallar azahar tini ma su Dad din suka koma masaukinsu.

Shi kansa Raheem Dad din yabi tareda su Alhaji tsohonsu har sai dare ya dawo gida baima shiga cikin gida ba ya shige sedai yayi waya da SANAAH wadda take fama da zazzabi kadan kadan kuma yayi ta bari ya ganta taqi bari kuma nauyin zuwa gurinsa takeyi gasu Dr Mum da kowa a gidan.

Washe gari shirin tafiya suka fara yi har dare hakama washe gari dan haka saida akai kwana uku da daurin auren tukuna suka daga zuwa Nigeria.

Dad baiga Dr Mum ba har lokacin sai a airport da suka hade motocin Fleet sun iso airport dkn da iyayen nasa mata su duka da SANAAH wadda shima sai a lokacin ya sakata a idanuwansa bayan kwana biyu dan haka kallo daya yayi mata tana gefen Dr Mum ya dauke idanuwansa sbd wata fitinanniyar sonta daya taso masa da kewan shaqarta daya xama addiction dinsa.

Ita kanta SANAAH kallo daya tayi masa ta dan sauke kansa tana jin lokacin kaifin idanuwansa suka sauka akanta ya mata wani kallo ya dauke yana qarasawa gurin Dad.

Shi kansa Dad idanuwansa da suka dago suka sauka akan Dr mum wadda take sanye da wata purple doguwan riga mai kyau data fiddo asalin kabilarta da gyalanta dayake nade akanta ta dan fada ma kadan sbd zullumin yanda zatai rayuwa da hakeem din a yanzu baa matsayin matarsa ba ita daya daya hana zuciyarta da ruhinta sukuni....

Kallo daya yayi mata mai nutsuwa da kwanciyan hali dakyau kafin ya dauke kansa yana dawo dashi akan Raheem daya iso gurinsa yana gaidasa ya bude baki yana amsawa cikin tsari da girma.

Babu bata lokaci aka gama komai suka daga zuwa Nigeria.

A jirgi ma dayake can suke first class kusan iya sune dan haka a zaune sike cikin nutsuwa da walwala.

Dr Mum kusa da Dad take tareda shi batareda suna iya wata doguwan magana bama sbd wani kamshinta dayake fita daga kowace motsinta yana hana kansa da tinaninsa sukunin dabai taba samun kansa a hakanba dan haka babu wata magana mai tsaye sosai da sukeyi saidai kallanta datake jin nauyin hakan itama sbd tarin mutanen dasuke tare dasu.

Shi kuwa Fleet SANAAH bata tareda shi sam tana tsakiyar Maamah da mommy sbd baida hakurin dazai iya zama a kusa da ita batareda ya iya kamata yaji hannuwanta a cikin nasa ba ko janyota jikinsa dan haka ya kame kansa yana riqe control dinsa batareda ya iya juyawa ya kuma kallantaba sbd hakan ma zai iya tabasa duk da yana jin idanuwanta masu sanyi da kyau akansa tana sauke masa su tana kwantawa jikin Maamah tana masa wani sanyayyar kallo duk abinda yakeyi tana kallo har bacci ya dauketa mai sanyi.

********
Rayuwar Fammah da Al'amin kuwa ta kai matsayi da matakin da zuwa yanxu wuya ce mai tsananin gaske dukkaninsu suke sha wadda batada magani dan kuwa shaquwa da kusancin da suka samu bame hayaniya bane mai sanyin daya musu muguwar shigar da a yanzu suke wahala ne daga yanda Al'amin yafara janyewa daga gareta sbd hanasu shiga azabar dasuke fama da ita ayanxu.

Har cikin jininsa yake jinta da duk abinda ya shafeta batareda yasan yaushe hakan ta faru ba kawai dai yasan tafara zama illa ga rayuwarsa data rasa suninta da nutsuwanta kaman baya yanda yake,

Mutum ne shi mai principles da kiyayewa sosai tareda tsayawa akan gaskia dan haka tinda zuciyarsa ta gama kamuwa da abinda baisaniba akan Fammah jeerah wanda yakejin kaman he's obsessed with her saiya ja baya daga gareta sosai sbd kallanta kadai sakasa jin yana rasa kowace nutsuwa da kansa yakeyi bare jinta dayake dakatar da komai nasa cak..

Ita kanta yanda a yanzu tagama mutuwa da rasa kanta da tinaninsa da rayuwarta da zuciyarta tasan She is madly inlove with him amma shakka da tsoron makomar alaqar yake sakata jin hankalinta na tashi kaman yanda tagane shima yana janye kansa ne daga gareta dan tsare iyakarsa da duk fitinar da alaqar zata iya janyowa daga mahaifiyarta.

Ya zama busy sosai da sam yanzu basa haduwa sosai duk da suna guri daya a waya ne kadai yake iya magana da ita akan jin yanda take daga nan baya iya doguwan magana yake mata sallama dan haka sai abin ya tabata tafara wata rama sbd damuwa da tsananin halinda take cikin itama.

Suna ci gaba da hakan harta kai ta kwanta ciwon da ita kanta batasan menene yake damunta ba da dole ya bayyanarda kansa a gabanta ya kaita asibiti da kansa sukaga dr wanda ya basu tabbacin lafiyarta kalau kawai damuwa ce da rashin cin abinci.

Suna baro asibitin yana driving a natse idanuwansa akan titi sunyi shiru dukansu har suka iso gida yayi parking yana kasa kashe motar ya sauke wani lafiyayyan numfashi mai nutsuwa.

Kuka ta fasa ahankali tana rufe fuskanta da hannuwanta duka biyu sautin kukan na ratsa kunnuwansa da wani irin yanayin dayaji kirjinsa yayi nauyi ya dan rintse fararen idanuwansa da suka dan sauya ta bude su yana juyowa ya sauke idanuwansa akanta bayan tsawon lokacinda rabon daya sakata a idanuwansa.

Jin saukan idanuwansa akanta ya saka kukanta karuwa ahankali jikinta na sake sanyi damuwanta na qaruwa.

Kasa motsawa yayi bare iya cewa komai yanajin kukanta na ratsasa suna yaga duk wata nutsuwa da karfin zuciyarsa ya bude baki da sautin daya sakata jin nauyin kirjinta na karuwa yace

"Bana iya jin kukan nan pls Doc"

Bude kofar motar tayi tana ficewa ya bude tasa kofar ya fito yana bin bayanta sedai taku biyu yayi ya dakata cak yana riqe kansa daga binta sbd yana ci gaba da jin kukanta zai iya kasa riqe zuciya da gangar jikinsa gareta dan haka ya dafe goshinsa da hannunsa daya sbd yanda kansa ke sarawa da wani bugun gaske.

A cikin daren bai iya rintsawa ba dan haka ya tashi da ciwon kai mai tsananin gasken da bai iya fita office ba daga karshe ya yanke shawara daya da zata hana kansa bugawa da zuciyarsa dake gap da rasa lafiyanta kwata kwata shine rabuwansu a guri daya.

Akwai fahimta da kusanci sosai na maganganu a tsakaninsa da Dad jeerah da kusan shine dansa da yanzu yake maganganu dashi wainda ma bayayinsu da ko Raheem daya haifa bare Samad dan haka sukeda wata irin nutsuwa ta magana da rashin boyo a tsakaninsu dan haka ya kirasa da daddare bayan yaje asibitin shima yaga Dr ya dawo.

Cikin nutsuwa ya sanar da Dad din a lokacin da suke Morocco ya sanar dashi time yayi da Fammah ta dawo gida.

Da farko Dad shiru yayi yana juya zancen kafin ya tambayesa akwai wata damuwa ne da zaman.

Shi kansa Al'amin din shiru yayi kafin ya sauke numfashin daya kusan bayyanarda asirin zuciyarsa ya bude baki da nutsuwa yace

"Babu damuwa amma kadaicin ya fara damunta"

Shiru Dad din yayi kafin ya juya zancen wanda ya tabbatarda kiyayewan Al'amin da zamansa wanda yasan kansa da darajar mace sosai yafara samun wasu feelings ne akan fammah tinda ya zabi ayi nesan da ita daga garesa.

Babu wata wata Dad din yace

"Akwai abinda yake faruwa ne a tsakaninku Al'amin??
Chapter 139 · 0% Book details