← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 154

Sashe 77

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kuwa daki suka wuni yau SANAAH na lafe gefn Fammah kaman mara lafiya ta koma mata kaman baby daman haka take mata ta saba da shagwabarta amma yau duk ta sake narke mata.

Abincin rana ma yau a daki safiya ta kawo musu daman haka takeso ta zauna musu fira tinda batada sauran aiki.

Zaunawa tayi ta ringa musu fira Fammah na saka baki sunayi SANAAH na sauraronsu da murmushi akan fuskanta tana sauraronsu.

Sai yamma suka tafi bangaren mommy suka zauna acan tareda su saida sukaci abincin dare suka koma sukai shirin bacci suna hawa gado Fammah ta dauki wayarta ta saka kiran numbern Dad dinta ta America dan tasan yanzu da ita zata samesa.

Ringing kuwa wayar ta fara dan haka ta saka handsfree tana gyarawa SANAAH gashinta daya dan yi gefe da qananun kalba a kanta tana cewa

"Ya kamata muje Saloon"

Daukan wayar yayi a natse muryansa mai kauri ta sauka a wayar yana cewa

"Yes Fammah"

Cikeda farin ciki da kauna da kulawa tace

"Yes Dad ina wuni?
Yaya gajiyan tafiya?
Ka isa lafiya?

Numfashi ya sauke a natse mara sauti a natse yana fahimtar wayar a handsfree take sbd yanda muryan famman ke dan amsawa kadan dan haka ya dago idanuwansa da suke farare tas daga file din dayake hannunsa daya yana karantawa ya kalli wayar hannunsa ya danyi baya da bayansa ya jingina a natse sautin daya qarawa muryansa zama deep da zama strong yace

"Lafiya kalau alhamdllh,
Yaya kuke?
Kuna lafiya?
Yaya jikinku??

Murmushi fammah tayi tana sake gyara zamanta da dora hannunta akan SANAAH tana sake gyara mata gashinta tace

"Lafiya muke Dad,
Babu me rashin lafiya a cikinmu,
Kana America ne Dad?

Shiru yayi a wata irin tsanake kunnuwansa na nutsuwa da sauraro komai kankantar motsin dazai iya faruwa ta bangarensu sbd jiran jin alaman taji gaisuwan tasa wadda yayi jam'in da yasan zata san da ita yake idanuwansa a tsaye kan file din hannunsa amma kunnuwansa da nutsuwansa da zuciyarsa na kan abinda yake jiran ji.

Ita kuwa tinda ya bude baki yafara jerowa fammah tambayoyin tayi shiru lafe a gefen famman datake batareda ta motsaba saida kalmansa ta karshe ta ratsa kunnuwanta da wani irin nutsuwa da kaifin daya sakata motsawa ahankali tana saka hannunta qasan rigarta ta dora tafin hannunta akan fatar cikinta tana rife idanuwanta ahankali wanda kai tsaye motsinta ya isa cikin wayar ya sauka a kunnuwansa take ya sake wani lafiyayyan mayen murmushin tabbatarda abinda ya sani tana lafe jikin fammanta kenan kuma ta jisa dan kuwa yasan matiqar taji abinda ya tambaya din zata motsa ta taba gurin kokuma janyewa daga gurin wanda hakan zai sakasa jin motsinta gashi kuma hakan ta faru.

Sautin murmushinsa mai wata irin sanyi da nutsuwa da tsari da kamewa da steez ya saukar musu wanda ya saka SANAAH bude idanuwanta ahankali ta kalli wayar wani irin kallan da shi bazata taba iya masaba mai cool yanayin data sake narkewa gefen fammah tana kasa dauke kyawawan idanuwanta akai tana jin muryansa yana magana da fammah wadda kusan kowace kalman tana sane da maanar dayake jeho mata sbd yasan tana nan tareda fammah a lokaci.

Koda suka gama wayar fammah cikin farin ciki take sosai sbd yanda tayi fira da Dad dinta duk da bata wani gane wasu maganganun nasa ba.

Kwantawa sukai batareda SANAAH ta furta komaiba har bacci ya dauketa mai sanyi.

Washe gari da safe suna breakfast shine da kansa ya kira Mum wadda taketa wani jin farin ciki da nuna isan itace mai Fleet.

Duk wayar da sukai su SANAAH din suna zaune suna jinta suna cin abinci harta gama ta ajiye wayar tafara musu surutun batason ya dade sbd indai zai dade zata bisa saisu dawo tare.

Fammah ce ta yanke zancen Mum din da sanar da ita tayi magana da Dad jeerah akan zai samar mata daman attending wani babban program na doctors da zaayi da manyan doctors na qasa da wata qasar zasu halarta a lagos kuma sai wanda yakeda matsayi da babbar hanya ne ma kadai zasu iya attending a cikin upcoming doctors dan haka ma iya yayan manyan qasa ne masu power zasu iya zuwa ga wainda ke shirin zama doctors dan taro ne na doctors din bama ka taba tsammanin ganinsu ba.

Mum na jin hakan tayi farin ciki sosai ta kuma ji tana tsananin buqatan fammah da ita kanta su halarci 6days program din dan haka take ma taji tana buqatan fara shirin zuwa.

Fammah ma sosai take tsananin farin cikin samun damar halartar taron dan haka SANAAH ma tana tayata murna sosai duk da ita bazata samu daman binta ba kila.

Dr Mum ma tayi farin cikin hakan dan hakan zai taimakawa Fammah din a cikin karatunta.

Yau Mum bata je koinaba bayan taje ta gaidasu dawowa tayi suka zauna bangarensu tanata wayoyi da gida akan auren da zaa yi na kaninta da shine kadai takeda.

Fammah da SANAAH kuma futa sukai sukaje gyaran kai suna gyaran kafa da dan karamin siyayyar abunda suke buqata sai yamma suka dawo.

Suna dawowa bangaren mommy suka sauka suka zauna a palon tareda kowa dayake nan suna maganarsu.

Hannu Dr Mum ta miqawa SANAAH tana nuna mata kusa da ita tazo nan ta zauna tana cewa

"SANAAH ki dena dadewa sosai idan kin fita ba kyau karki manta kinada miji kinji"

Shiru kowa yayi a palon hadda Mum data sake baki tana kallan Dr Mum din cikeda mamaki dama tsananin shakka zatai magana Fammah ta yanketa da shirun kowa da cewa

"Grandpa ne fa yayi mata mijin kuma wlh batasonsa a dena maganarsa munada candidate dinmu"

Dariya Mum tayi tana cewa

"Ai kuwa dai indai hakane Dr mum inama ina bayan baby SANAAH dan Allah kada ayi mata auren hadi sam bai kamacetaba a bari zamu kawo miji"

Dr Mum rasa abin fada tayi sai kawai ta sake murmushi tana kallan Meenah kafin ta kalli SANAAH wadda tayi saurin qasa da kai tana dan kama yatsunta,

Maamah kuwa fuskewa ta dan yi tana taya Meenah dariya mommy ma murmushin karfin hali ta sake.

Da haka aka juya zancen da Meenah ta fara jarawa bayani tana cewa bazaa bawa SANAAH duk wanda bataso ba dan Allah.

Tin kafin ishai suka iso bangarensu fammah ce ta fara wanka kafin SANAAH tukuna sukai sallah.

Shirin bacci sukai SANAAH ta saka riga da wando na bacci maroon da suka kwanta mata ta hawo gadon ta zauna gefen Fammah tana daga wayarta itama tareda duba chats dinta a natse kaman daga sama taji bayyanar muryansa a cikin kunnuwanta tsanake yace

"Hi doc"

Wani irin zirrrrr taji cikin kunnuwanta xuwa zuciyarta ta dago idanuwanta ahankali ta kalli wayar Fammah dake gabansu ba tsammani idanuwansu suka shiga cikin na juna batareda shi kansa yayi tsammanin ganinta kai tsaye ba daga daukan wayan fammah din wadda kiran yake VidCall ne.

Da farin ciki fammah ta daga hannu tace

"Hey Dad,ina wuni?
Yaya kake acan??

Dauke idanuwansa yayi daga inda suke a natse yana tsaidasu akan fammah din yace

"Alhamdllh,
Yaya kuke?
Ya Mum naki and her Baby"

Kallan SANAAH Fammah tayi wadda ta janye ahankali daga jikinta tana kokarin kwantawa gefe ta janyota tana cewa

"Gata nan Dad she's always acting and behaving like a baby shiyasa Mum take kasa kiranta da baby"

Qarasa fadan hakan tayi tana jan kumatun SANAAH din kadan dan kulawa wanda ya saka SANAAH dan ture hannunta cikin wani yanayinta daya sakas tsaida kallansa akan farin hannunta tas daya sauka akan na fammah tana dan tureta ahankali tana hana idanuwanta sauka akan wayar sbd jikinta ya mutu tana hana kasalarta bayyanuwa.

Magana yakeyi da fammah a tsanake yana zaune a lafiyayyan luxury sitting room dinsa dayake gidansa na America din.

Duk maganar da sukeyi da fammah bai kuma kallan SANAAH ba amma kowace motsi da bugawan zuciyarta dake fita yana ankare dashi wanda itama a jikinta taji hakan dan hakane itama bata dago ba tayi shiru da wayanta a hannu gefen fammah tana kallan sakwannin sabuwan number na shigo mata wadda take saka ran Prof ne sbd batai saving numbernsa ba har yanzu hakama bata taba replying massages nasa ba.

Suna gamawa a natse ya furta

"Ku kula sosai ok?,gudnight"

Suna kashe wayar SANAAH data rufe idanuwanta cikin sanyi bata sake motsawaba bacci ya dauketa a hakan sedai fammah data gama chatting dinta ta dan gyarata ta kwanta itama.

****bayan tafiyar nan tasa kullum a kwai daidai lokaci daya daya ware yana waya da 'yarsa sedai bai sake kiransu Videocall ba sedai normal voice call.

Satinsa biyu da tafiya babu ranar da baya jin motsinta a kusa da fammah waya kuma bai taba magana da itaba sbd kusan gabaki daya ta koma kaman wadda ta rasa bakinta ko magana bata iyayi yanzu tayi wani irin sanyi da qarin rashin son hayaniya,

Koyaushe tana daki sai idan taje gurin Dr Mum dake wani irin nuna mata kauna da tattali kaman baby qarama ga wata irin kulawa datake dan kusan da ita da Dad jeerah kowa kokari nuna mata kaunar datafi ta kowa.

Fammah ta koma tamkar itace sanyinta dake bata nutsuwa dan kuwa koyaushe itace take kallo kallan da bata gajiya dayi mata mai sanyi ita kuwa tarairayanta takeyi tana ganin kaman SANAAH na mata kaunar da bata iya boyewa ne shiyasa duk ta sauya mata zuwa kaman jaririyan baby.

Dad ya samar mata daman attending program din dan haka aka shirya tafiyarsu da Mommy wadda itace zata raka Fammah din sbd kada tayi tafiya ita daya bayan angama komai Mum dinga tace zataje dan haka tafiyar dole g
Ya zama su uku ne zasuyita.

Dr Mum taso ta hana Meenah tafiyan amma yanda ta yanke son attending itama ya saka ta kyaleta aka hada komai na tafiyar tasu tareda ware musu securities da zasu tafi dasu da kuma tanadar musu wani lafiyayyan luxury 5star hotel da zasu sauka Fleet kuwa dollars ya qara zubawa kowannensu a acct duk da basama buqatan kudin.

Ranar da zasu tafi SANAAH kaman zata shiga jinya sbd rashin kuzari da kasala dan haka da ita aka kaisu airport tana dawowa ta sake narkewa a dakin Dr Mum wadda taketa jinta har cikin ranta.
Chapter 77 · 0% Book details