← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 154

Sashe 39

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

38
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Umma fadeela matar uwargidan Dad din itace ta fara dagowa ta zubawa baqin nasu ido batareda bayyanarda kowane yanayi a kan fuskanta ba sbd batasan matsayin da zata ajesu ba tukuna dan ita sam dawowansu gidan bai dameta ba tinda suna bangarensu tana nata kawai dai mamakinta daya ne akan Mommy da bata wani manyata ba dan bazaka ce itace uwar data haifi Al'amin ba duk da wahala taso jigatar da sauranta amma dayake jikik buzaye ne zata ce ko fulani gashinan dai jikinta bai rikice ba,

Akan SANAAH wadda babu wanda ta dago ta kalla bayan Dad data bude bakinta a sautin nutsuwa ta gaidasa ya amsa mata da kulawan shima kafin ta dago a natse ta gaidasu suma Umman ce kadai ta iya amsawa amma Hajiyan Samad kasa motsawa tayi tana kafe SANAAH da idanuwanta da suka sauya har saida mommyn itama ta gaidasu suka amsa hankalinta kuma yana dawowa akan mommyn tanajin kaman ta dora bindiga akansu duka ta fasa dan tasani zuwansu rayuwarsu ba alkhairi bace ko daya babu khairan,
Kofofin masifarta ne data Samad suka bude dan ya gama zama mahaukaci akanta kuma yana tabata anan din su duka mugun gani da mugun ji zasu fuskanta daga mahaifinsa,

Ta wani bangaren ma jin tayi kaman kishiya ce Dad jeerah ya kawo musu sbd dai da alama duk abinda akai musu yiwa su mommyn zaayi dan haka duk ta qarasa rasa dadin ranta.

Dad kuwa a natse ya gabatar dasu ga kowa ya kuma gabatar musu da kowa tareda dora bayanin girmama juna da zauna lafiya ba hayaniya ba fitina kowa zaiyi rayuwar dayake so ba takurawan kowa hakama SANAAH yarsa ce daya shedawa kowa cewan shine ubanta a kaf duniya yanzu dan haka cikakken iko daya take dashi da Samad a gidan da duk abinda yake gidan dan haka kada wanda ya shiga hurumin kwanciyan hankalinta ko wanene kuwa.

Wannan matsayin da SANAAH ta samu ne ya saka Mommy jin idanuwanta sunyi nauyi taji tana bawa dad din girman da bazata iya hadasa da kowaba itama dan kuwa ya musu abinda suka rasa daga kowa.

Shi kansa Al'amin jin yayi tsananin kauna da girman Dad ya qaru sosai a ido da zuciyarsa dan haka sukai godia sosai suka fice.

SANAAH kuwa itama kauna ce ta take ta shiga zuciyarta me karfi tasa sbd a bayyane ya nunawa kowa kaunar dayake mata da matsayinta dan haka sukaji yanxu basada shakka da tsoron rayuwa a cikin ahalin.

Da kanta ta bude baki tayi masa godiyan data sake bata matsayi a idonsa dan zallan girmamawa ne daga 'yar datake jikarsa tinda shekarunsu daya da jikar tasa wadda bata taba sabuwa dashi ba batama yi masa wani sani ba dan hakanne yake jin SANAAH din itama kaman jikarsa ce jininsa zai samu kauna da kulawa da kusanci daga gareta tareda bata matsayin Fammah a rayuwarsa da zuciyarsa ma ta ishesa.

Suna dawowa bangarensu Abinci sukaci suka zauna palo suna tattaunawa banda SANAAH data lafe tayi shiru a gefen yaya Al'amin din tana jin yana yabo da bayyanarda halayen Dad jeerah masu kyau da karfin akida da zazzzafan hukunci.

Har dare sosai suna palo suna firarsu tukuna suna shige kowa yayi shirin bacci suka kwanta.

Washe gari wuni sukai su kadai sai safiya da mommy ta kira taxo ta zauna cikinsu tana tayasu fira dan SANAAH bata wani cika firar ba,
Al'amin ya fita Mr S ya saka dan daukesa antafi gurin wani abin dashi na shirin tafiyarsa da sauran siyayyar abinda yasan mommy na buqata dan ita SANAAH kai tsaye mace aka saka ta qarasa mata siyayyar komai hatta su undies da duk wani abin da mace yar gata mai iko zata buqata.

****Cikin kwanaki qalilan aka qarada cike wardrobe dinsu da kayan alfarma na sakawa tin daga native wears da abayas da wasu kayan ma da komai,

Dakin SANAAH kana shiga bazaka taba dauka a qanqanin lokaci aka tanadar mata komaiba dan kuwa ko takalman sakawanta jerinsu wani kallan ne masu tsadar gaske designers da handbags suma manyan brands da tarin tirarika da cosmetics.

Skincare set dinta suma suna jera a toilet da gaban dresser dinta ga sabuwan wayar da aka siya mata me tsadan gaske,
Duk wannan abubuwan mommy itama nata daban ne daidai jin dadinta,

Sun fara sakewa sbd anyi kwanaki sosai kuma babu takurawan kowa ba damuwan komai ga Al'amin tafiyarsa ta kammala zai wuce sun gama komai kuma farin ciki suke na tafiyarsa bawai damuwa ba sbd cigabansa ne babu abin damuwa a ciki.

Kullum kowace safiya SANAAH zataje ta gaida Dad cikin kulawa da girmamawa daga nan zataje har bangaren Umma itama ta gaidata daganan taje ta gaida umman Samad amma ita ba kullum take zuwa ba sai ankwana biyu sbd bata fatar abinda zai taba hadata da Samad da kuma yanda take mata kallan tsana da qyama ya saka bata wani zuwa dan bata iya daukan ana wulaqantata sam a rayuwarta.

Al'amin ma daman kullum yana gurin Dad din dan shima yana nuna masa kulawa da sakewa sosai dan haka koda zai tafi bai tafi da kowace damuwa akan ahalinsa.

*****Bayan tafiyar Al'amin sun sake sakewa basu takura kansu ba sun zama yan gida dan maganar watanni hudu akeyi da zuwansu gidan kuma zuwa wannan lokacin shaquwa da sakewa ya fara shiga tsakanin SANAAH da Dad dan hakanne ya saka duk zataje gaidasa sai tayi masa tea mai qara lafiya da nutsuwa takai masa da snacks da itace take da kanta sbd tareda safiya take aiki ta iya abubuwa da dama yanxu.

Yanda take bayyanarda kulawa da tattalinsa ya saka take sake samun matsayi a gurinsa dan haka aka fara shirin itama komawa karatunta a makaranta daban mai kyau da kudi.

Duka wannan tsawon lokaci Samad baya qasar yayi tafiya hajiyarsa ta takura masa yayi tafiyar dan jinya acan bayan ya warke kuma ya wuce America gurin Godfather dinsa dan gudanar da wasu manyan ayyukan company dinsu dayake can shiyasa bai dawoba sai kwanakin katsam ya sauka a qasar.

SANAAH KHALIL ta sauya gabaki daya ta tashi daga SANAAH din baya sbd hatta lafiyar skin dinta ba daya data baya ba,
Nutsuwa da kwanciyan hankalinta ya saka class dinta da kamewanta qaruwa zuwa daukan hankalin duk namjin dazai muamalanceta dan haka take da wani fizgan hankali,

Qamshinta shi kansa mai sanyi da nutsuwa ne bata daukan wulaqanci ko kadan dan daman hakan take a baya bata iya muaamala da duk wanda zai bata damuwa da matsala shiyasa take girmama matan gidan daidai gwargwado amma bata wani shiga ko yawan bibiyansu dan bata iya juran yanda suke musun daman ita mommy bata wani zuwa koina sai ankwana biyu taje su gaisa kokuma idan wani abu ya dan faru zata je ta dubosu su dan gaggaisa ta dawo dan kuwa zaman haka sukeyinsa kaman kishiyoyi dan babu kauna a cikinsa kowa ta cikinsa na cikinsa.

***Yau saloon taje tareda Safiya wadda ta rakata kuma drivernsu da aka ware musu ne ya kaisu dan haka sai yamma sosai suka dawo ta fito mota wayarta na hannunta sai handbag dinta tana duba sako a wayarta tayi haske sosai na samun lafiyar fata da hutun dayake cikeda rayuwa da fatar.

Safiya dake biye da ita surutu take mata tana jinta sama sama tana karanta abu har suka isa hanyar bangarensu suka shige.

Itace ta miqa hannu ta bude kofar palon tana sako kai ba tsammani taji mutum a gabanta ta dago kai ta dora a fuskansa kai tsaye batareda tsammanin ganin wanda ta gani din ba ko a mafarki.

Kasa motsawa tayi tana mutuwan tsaye a gurin idanuwanta na sauyawa akan fuskansa gabanta yayi mummunan faduwa.

Gyara tsayuwa yayi a natse yana kafeta da idanuwansa da suka fara qanqancewa da wata irin zazzafar soyayyarta data kusan kashesa a wannan tsawon lokacin daya dauka bai ganta ba a cikin idanuwansa ba,

Wani nauyi da dumi ne mai cin kirjinsa yaji yana mamaye zuciyarsa na kewan da idanuwa da ruhinsa sukai mata idanuwansa na sake sauyawa,
Chapter 39 · 0% Book details