← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 154

Sashe 70

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********
Dad na rufe baki da maganar tasa fuska a daure yana neman sake basu pressure din da saita hukuntu da kwaso kafar datai kashe aure ba kunya wanda zafin nasa auren data kashe da taurin ranta tsawon shakaru yana taso masa yana jinsa kaman yanda take kokarin jin wannan auren da yasan ko zata rasa ranta bazata bari a kashesaba yanxu dan haka zai dandana mata radadin daya shiga a lokacinda tayi masa barazanar rabuwa dashi kafin sukai rabuwar duk da baida kowace niya ta raba auren SANAAH aurene da sai mutuwa insha Allah amma zasu dandana wulaqancin da sukaiwa auren da 'yarsa.

Sake hade fuska yayi sosai yana kallan Fleet wadda sai a lokacin ya dago a natse ya kalli Dad din babu kowace damuwa ko tashin hankali a tattare dashi bare tsoro ko fargaba.

Gyara zamansa yayi a natse yana sauke numfashi mai sanyi da bude baki zaiyi magana Dr Mum dake kallansa kaman kirjinta zai fado tsabar bugawa da nauyi rigansa magana tayi da wani irin saurin gaske sbd shakkar abinda kila zai iya fada dazai datse auren tace

"Me zaka ce?
Kanada abin fada ne akan hukuncin dayake son yankewa wanda ni ban amsa ba??
Komai bazakace Fleet."

Maida kallanta akan Dad tayi zatai magana sautin RAHEEM ya katsesu a tsanake da cewa

"Allah ya huci zuciyoyinku duka ya qara lafiya da nisan kwana,
Allah ya saka da khairan,
Ina kuma baku hakuri duka"

Yana gama fadan wayarsa dake gefensa ya dauka a natse ya miqe ya nufi kofa yabar palon batareda sake ko waiwayoba ya ficewansa dan baida abin fada a tsakiyarsu da suke wannan tashin hankalin hakama shine yakeda ikon komai akan auren dasuke hannunsa bawai su ba dukkaninsu sunyi iya ikonsu sun aura masa matan dan haka sakin aure ko zama dasu wannan zabinsa ne ikonsa ne kuma raayinsa ne duk da shi din mai biyayya ne akan komai.

Yana ficewa Dr Mum taji tashin hankalinta ya ragu ta juyo ta kalli Dad shima ita ya kalla yana kame fuska taji kaman ta ringa fada masa maganar da zata ringa yanka zuciyarsa da sakasa baqin ciki da irin tsaka me wuyar daya sakata.

Kasa cewa komai tayi sai mugayen kalaman datake nema a bakinta ta yaba masa amma ta nemesu ta rasa sbd hankalinta daya rabu biyu akansa da kan SANAAH.

Kallanta yayi yace

"Dr kiyi magana da danki ina nan ina jiran amsarku kafin gobe"

Yana gama fadan hakan maida kallansa yayi akan Mommy yace

"Shikenan zainab ku tafi saina sake nemanku"

Kallan SANAAH yayi wadda idanuwanta suka qasa yace

"Kada ki yadda kiyiwa mutuwan auren nan kuka ina raye bazakiyi baqin cikin rasa mijin aure ba insha Allah."

Yana rufe baki Dr Mum ta miqe tsaye tareda miqa hannunta ta kama na SANAAH ta miqar ta jata sukai kofa tana jin tafisa iko gaba da baya akan SANAAH dan haka bazai nuna mata ikon komaiba akanta.

Mommy baki ta bude a natse tayi masa godia da adduar qarin kwana da itama ta saba tukuna ta miqe tabi bayan Dr Mum din tareda Maamah wadda ita zainab din ce zata kama dan itace tata SANAAH kam uwar Nasir ta kamata mutuwa ce kila yanzu kawai zata rabata da ita.

Suna fitowa SANAAH ta sake qasa da kanta tana jin yanda Dr Mum ke tafiya da ita batareda cewa komaiba har saida suka iso bangarorinsu dake jere Dr Mum din ta juyo ta kalleta da wata irin kallan datake jin zuciyarta na karaya da nauyin rashin Nasir dinta daya dawo mata sabo ta bude baki ta ambaci sunanta da sautin daya saka SANAAH din dagowa ahankali batareda ta iya kallanta da idonta ba.

Su Maamah ne suka iso Mommy tace su qarasa bangarensu ba kowa acan.

Wucewa sukai zuwa can suna isa ba kowa a sai safiya dake kitchen tana aikinta.

Zama sukai a palon kowa yana kallan dan uwansa cikeda kewa da tashin hankalin abinda ya kawo dukansu a nan ga kuma auren daya hadu batareda shiri da sanin sauran ba.

Shiru sukai saidai Mommy ta bude baki ta sake gaidasu da tambayar bayan rabuwa da lafiyar kowannensu.

Maamah da farin cikinta yake a bayyane babu damuwan komai ta amsa tana cewa

"Ina Al'amin?"

Murmushi da bayyanarda farin ciki itama mommy keyi ta sanar mata yana can qasar dayayi karatu yana aiki tukuna.

Dr Mum data kasa dauke idanuwanta daga SANAAH ganin kawai sukai hawaye masu zafi suna gangaro mata tana jin baqin ciki da takaicin kansu da suka kasa zuwa duba su SANAAH da kansu a qasar sai yanxu da dalili ya kawosu,
Irin son da Nasir yakewa SANAAH tazama uwar banza da bata nemeta ba ta bari har saida HAKEEM ya nemeta ya inganta rayuwarta gashinan yana nuna mata ikon da itace ya kamata ta nuna masa akanta,
Irin kaunar datakewa Nasir komai nasa daya bari tsananin kaunarsa takeyi amma ta manta da girma da matsayin SANAAH a rayuwarsa sai yanzu data ganta takejin radadi da baqin cikin kanta.

Maamah ce ta kalleta tace

"Ai ba hawaye zakiyiba Dr keda zakiyi farin cikin kin fara ganin matar kafin kashe auren"

Numfashi mai zafi ta sauke tana jin kirjinta na sake nauyi ta kalli SANAAH ta bude baki tace

"Baby SANAAH kisa a ranki indai ina raye wlh ko hakeem daya daura auren nan bai isa ya kashesa ba a maidaki bazawara,
Kuma koda auren ko babu a yanxu dana ganki kafata kafarki bazan barki anan ba a karkashin kowa"

Shiru SANAAH tayi sbd jin wani sabon tsari kuma a rayuwarta da cikakken matsayinta ma bata sani ba.

Dr Mum dinne ta dago ta kalli mommy tace

"Wai to ya akai Hakeem ya sameku da maganar auren Zainab?

Numfashi mommy ta sauke take ta sanar dasu komai babu boye komai sune kadai wainda tasan sunada haqqin sanin komai akan SANAAH ba boyo har irin yanda suke zaune dasu Ms Meenah yanzu wanda sun kasa iya barin tasan da auren da babu wanda yakeda tabbacin inda zashi.

Dr Mum jin tayi kaman zata kama da wuta sbd baqin ciki da tsananin takaici da radadi dan haka bata ce komaiba hadiye duka kalamanta tayi dan babu alkairi a abinda zata fada akan matar Hakeem da 'dansa.

Aure kuwa ai maganar ba wanda yasan inda zashi maganar banza ce dan kuwa inda kowane aure yake zuwa saita kaisa matiqar tanada rai da lafiya babu wanda zai wulaqanta SANAAH ko hana mata right dinta cikakke na matarsa.

Maamah kuwa tsananin zanyi jikinta yayi taji itama anata bangaren bata maida alkhairin Khalil gareta ba dan kuwa khalil shine wanda ya zama bangon rayuwarta da babu wanda zai taba maye gurbinsa na zama bangonta.

Numfashi itama ta sauke tana cewa su zainab din su yafe mata tayi kuskure mai girman da bama zata iya hada ido da Al'amin ba.

Dr Mum ce ta miqe ta bar bangaren suka bita banda SANAAH data kasa binsu suka tafi bangaren su Dr Mum din.

Acan kuwa hajiyar Samad labari da fira kala kala take janyowa tana bawa Meenah tana neman ta yanda zata sako mata zancen auren Fleet da SANAAH amma duk dinta ta fara bullo zancen sai Meenah ta sauka akai tana fadawa wani zancen da baima da alaqa da abinda take son isarma.

Takaicin Meenah dinne ya ciketa ta ringa tsinewa sakarcinta da rashin tinaninta daya kasa kaiwa ga abinda taketa son isar mata tsawon lokaci.

Ga hankalinta ya rabu biyu da abinda yake faruwa da aka aiko kiran Maamah daga bangaren Hakeem.

Cikin kuluwa da kai karshen takaicin meenah datake jin inda yar uwarta ce wlh saita mata dukan tashi kisha ruwan gishiri kuma taqi fadan dalili tace

"Ai wannan bangaren da akai na dauka sabuwar amaryar fleet akaiwa shi shiyasa ma ban taba shaawan shigowaba ko kallo sbd takaicin kada tarihi ya maimaita kansa"

Ajiye wayar hannunta Ms Meenah tayi tana yiwa Hajiyar wani kallan tsanar da a take ta cike kirjinta mai tsananin zafi da jin kaman ta jona mata wuta tace

"Ashe dai da gaske bakin cikin zamana anan cinku yakeyi ko??
Daga anyi sabon gini a cikin villa dinnan kaf a rasa wadda zaa fara haskowa mijinta aure saini??
Me nayi?
Kabilancin da akaiwa Dr Mum a baya data shigo cikinsu nima shi zaku fara nunan yanzu??

Fammah ce ta qaraso gurin daga kitchen data fito tana cewa

"Mum pls"

Katseta Mum din tayi da wani irin tsantsar bacin ran da bata taba ganinta dashiba tace

"Stay out of this"

Dawo da kallanta tayi akan hajiyar datai mutuwan zaune da mamaki tana kallanta da sabon takaici da baqin ciki da kunya duka lokaci daya sbd bata taba dauka Meenah zata tsaya akan ana neman mata maganar kishiya bane bayan a kalamanta baro baro anyi kishiryarma take nufi.

Ms Meenah dataji gabaki daya zuciyarta tayi duhun da zata iya shaqe hajiyar har lahira dauke kallanta tayi daga kanta dan zata iya fasa mata kwakwa akai tace

"Hajiya duk irin mutuncin da muke baima kamata kiyi irin wannan tinanin ba akainaba,
Meyasa bakiyi tinanin Dad ne zai karo aureba da kikaga sabon gurin?
To Dad dinne dai da bakiyi tinani ba ya gyarawa Dr Fammah dinsa guri....."

Da gatse da rashin nuna girmamawa ko daa ga matar uban mijinta ko kadan ta qarasa zancen wanda Hajiyar tajisa kaman saukan gudumar da aka sako daga sararin samaniya a tsakiyar kanta.

Kallan Ms Meenah din tayi da idanuwanta da suka rasa yanayin bayyanarwa sbd abubuwan kashi kashi a take

Bakinta ta bude zatai magana Dr Mum ta sako kai acikin palon a natse fuskanta a kame.

Bata lura da hajiyar ba saidai hajiyan data zuba mata ido ta kafesu akanta tana kallanta zuciyarta na wani irin qarasa mutuwa da tsananin tashin hankali da rikicewan abinda har abada babu wanda ya taba saka ran faruwarsa a kaf ahalin jeerahs dama na Morocco din wato dawowan wannan matar JEERAHsV.

Mommy ce da ganin Hajiyar a palon ya sakata mamaki mai tsanani dan haka ta dan kama yanayinta daman ba sakewa a tsakaninsu tace

"Hajiya kina nan ashe?ina wuni ya gida?
Chapter 70 · 0% Book details