← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 154

Sashe 7

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fammah da idan tanason abu itama zata iya komai akai bare hakeem da zata iya mutuwa akansa dan haka kai tsaye ta amince da zuwa ta zauna duk inda sukeso matiqar zasu kasance maaurata itada hakeem din har karshen rayuwarsu.

Tana amincewa iyayenta suka amince suma cikeda farin ciki dan haka babu sauran shamaki iyayensa suka taho har qasar Alh babba Ahmed ne da kansa yaxo shi da Alh husain suka nema masa aurenta tareda bada wata irin dukiya me yawan gaske da zinari wanda su larabawa dashi ake biyan sadakin su.

Babu daukan lokaci akai bikin auren wanda yayi suna sosai sbd irin dukiyar da aka zubar da kuma kasancewan Hakeem jeerah shine 'da namiji daya da jeerahs suke dashi da aka fara aurarwa dan haka kusan duka yan uwansa mata dake qasashe daban daban da wainda ke Nigeria ma duka saida suka halarci bikin nasa da dr fammah wadda take cikin tsananin farin cikin da duniya ta shedar da shi daga ita har hakeem duk wanda ya kalli bikin xai fahimci yanda suke tsanani da mutuwar son juna dan kuwa koina basu taba boye soyayyarsu ba wadda ta saka yan mata da yawa jin inama sune dan samun miji kamansa da babu abinda ya rasa a tsakanin kyau,dukiya,ilimi,wayewa,addini,soyayya da kuma zallan daukan hankali da kwarjini.

Bayan bikin kai tsaye Nigeria aka taho da amarya a cikin makeken lafiyayyan bungalow dinta dake cikin JEERAHs VILLAH.

Iyayenta suka kawota da kansu suka inda zatai rayuwa bawai wadatar gurin ba sbd sunsan idan dukiya da daula ake magana a JEERAHs to yarsu zatai dukkanin rayuwar da kowace mace ke buqata ta watada da jin dadi da zallar hutu amma suna son zuwa su kawota da kansu dan su samu kwanciyan hankalin sanin yarsu na qasar da basu taba zuwa ba har ita din sai a yanxu.

Kwanaki biyu sukai a Nigeria suka tattara suka koma bayan sun tabbatar yarsu tana cikin familyn da har 'yayanta da zata haifa a duniya bazasu shiga kowane irin qunci ba.

******sabon babin rayuwar tsantsan soyayya mai sanyi da ratsa jini da jiki Captain Hakeem jeerah ya bude da matarsa Dr fammah wadda ya sheda abu daya shine da soyayyarta zai mutu a rayuwarsa,

Kasancewansa bature kuma wanda bai tashi a tsakiyar uwa da uba ba ya saka bai iya boye abinda yake tsananin so dan haka babu wanda ya taba takura musu rayuwarsu sukeyi hankali kwance tsawon sati shida kafin suka tattara ya koma da ita America.

Babu wanda ya takurasu sbd su samu damar jin dadin amarci sbd tini aka gina mata wata lafiyayyar private asibiti me kyau da tsananin tsarin gaske wadda zatai aikin a nan Nigeri.

Kusan watanni bakwai suka kwashe acan qasar kafin ta dawo ta barosa can sedai ya ringa zuwar musu.

Rabuwarsu ta sake tsananta musu yanda suke jin juna amma hakanan suka hakura kowannensu ya rungumi aikinsa musamman shi da a yanxu komai na aikin ke sake nauyi dan kuwa matsayinsa dake qara gaba sbd jajircewansa da sadaukarwarsa dan kuwa ya qarasa sadaukar da rayuwarsa kaf gabadaya akan aikin batareda tsoron mutuwa ba ko shakka ko daya shiyasa yake tamkar wanda baida zuciya a fagen aiki.

****Dr fammah ma yanda take da kafiya akan aikinta ta sadaukar da rayuwarta akan nata aikin sosai ta zama busy akan aikinta dan shine yake bata nutsuwa da kwanciyan hankali dan haka bata wani zama gida sosai bata yawan shiga hayaniyar family sedai babu wanda bata bawa girmansa a cikin iyayen da yan uwan mijin duk da sunada wayewa da ilimi babu wanda yake takura kowa,

Iyayen mijinta dukansu suna nuna mata kulawa da kauna sosai musamman yanda itama ta tsayu tana samarwa kanta sunan a matsayin dr fammah jeerah batareda jiran sun daga hannunta duniya ta santa ba sosai,

Ba iya asibitinsu take aiki ba tana zuwa asibitin gwamnati tana duba marasa lafiya sosai a duk ranakun alhamis da jumaa dan haka sai ya zamana a ranakun manyan marasa lafiya da case dinsu yake babba ake tara mata tana dubawa tana kuma taimaka musu sosai ga wainda basuda karfin iya nemawa kansu lafiya.

Kadaicin datake fama dashi da kuma buqatar me tayata fuskantar abubuwan da bata san yaya zata iya fuskantarsuba a qasar ya saka da kanta ta nema P.a dinta da hakeem ya samar mata akan ta samo mata me aiki wadda zata rinta zuwa koina da ita sbd masu aikin gida idan sun gama komai sun jere abinci tattarawa suke su koma bangarensu na masu aiki sai kuma gobe dan haka kadaici yana mata yawa sosai duk da batason kowa a tareda ita.

Samo mata me aikin akai amma ko wata biyu bataiba ta sallameta sbd batajin komai na nutsuwa da rage kadaicin datake so daga gareta dan haka sai kawai tace a barshi.

Bata jima da sallamarta ba Hakeem ya dawo ta shiga farin cikin da bata taba shiga ba dan kuwa aikima dena fita tayi kwata kwata sbd samun nutsuwan ruhinta da farin cikinta.

Shi kansa yayi kewan matarsa kaman bazai iyaba duk da karfin zuciyarsa.

Hutu yayi me tsayi kafin ya tattara ya koma wanda a lokacin ne aka sake masa qarin matsayin da duka familynsa saida suka tafi har qasar akai bikin qarin girman dasu musamman matarsa dakejin farin ciki da kuka a lokaci daya sbd harga allah a yanxu jin takeyi kaman zata rasa rants sbd kadaici dake cin rayuwarta na rayuwa a inda ba uwa ba uba ba miji ba kowa ita kadai take rayuwarta a inda bata saba ba dan haryanzu ta kasa sabawa shiru kawai tayi sbd batada kowace irin mafita amma babu daren da bata kwantawa tayi kuka ta fadawa Allah.

Bayan dawowansu rayuwarta ta kadaici da damuwa taci gaba ahaka har depression yafara kamata wanda ya saka ta rage zuwa aiki sosai dan kuwa kanta yafara neman cakewa.

Ranar datai sati uku bata fitaba sbd damuwa da quncin take ciwo ya kwantar da ita wanda ya saka bata fadawa kowaba ta daure ta fita asibiti da kanta acan manyan likitocin asibitin yan uwanta suka kwantar da ita batareda sanin ahalinta ba.

A wannan lokacin ne dole P.a dinta ta saka daya daga cikin maaikatan asibitin masu shara ta kula mata da ita sbd ita a ranar tafiya zatai mahaifinta ya samu accident ya rasu.

FATIMA MUHAMMAD IBRAHIM shine sunan mai aikin wadda ta zauna ta zubawa Dr Fammah idanuwanta cikeda kulawa da tausayi tareda kauna me sanyi sbd dr fammah batada hayaniya duk da kallo daya zakai mata kasan ita din me zafi ce amma tanada tausayi da kulawa sosai ga mutane kuma kowa yasan balarabiya ce aka auro batada kowa anan kaman ita datake batada kowa a duniyar sai mijinta wanda baya tareda ita yana gurin qwadago sedai yazo yayi kwana biyu ya koma kuma itace take tsaye akan kulawa da kanta da kusan ciyar da kanta sbd idan ya tafi yakan dauki lokaci me tsayi kafin ya dawo.
#MAMUH
#BEST LOVE
#DR FAMMAH
#FATIMAH MUHAMMAD IBRAHIM
#SISTERS LOVE
#JEERAHS
#FLEETS

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank Maryam sani gummi
090331810170
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

7
_*LADY'S BEAUTY PALACE*_
08169307477

MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su

Location Katsina state
WhatsApp or call 08169307477
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)

********
Kasancewan Fatiman batada aikin komai daman bayan na asibitin datakeyi kuma bame jiranta a gida ya saka batai niyar tafiya tabar Dr fammah ba sbd har lokacin bacci take mai karfi cikin yanayi na ciwo.

Wuni guda tayi a zaune guri daya sallah kadai ke tada ita har sai bayan magrib Dr fammah ta farka cikin tsananin nauyin jiki da mutuwan jiki na wunin datai a kwance duk da ta samu saukin abinda take ji din sbd baccin ya taimaketa sosai tinda bata samun yinsa duk yanda taso sbd damuwa.

Akan fatima dake zaune a dakin idanuwanta suka fara sauka ta zuba mata su tana kallanta da mamakin ita din wacece.

Fatima na ganin hakan ta miqe tana dan gyara xaman hijabinta mara nauyi fes dashi sbd saida ta sake wanka a cikin asibitin acan toilet dinsu tayi fes sbd kada tama shigo dakin dr fatiman da kowace irin datti ko zufa duk da itama tanada tsaftar sosai amma tsayuwa ko zama a dakin da ahalin jeerah suke dole ta sake tsaftace kanta musamman dr fammah din datake kaman yau aka haifota sbd wankewa da haske da wani irin daukan ido.

Kallan dr fammah tayi da tsananin kulawa ta bude baki tana fara sanar mata da ita ko wacece tukuna sbd kada ta sakata tinani da cewa

'Ina cikin maaikatan asibitin nan ne haj Aishah ce ta sakani tsayawa sbd ita tayi tafiyan gaggawa mahaifinta ya samu hadari'

Shiru tayi sbd ganin har lokacin dr kallanta takeyi sbd ba komai haryanxu ta iya a yaren hausan ba duka duk da tana ji kuma tana kokarin yi dan ta dage da koyar tin kafin ma aurensu.

Ba duka ta gane hausan ba amma ta fahimci abinda fatiman ke nufi musamman yanda tayi bayanin a natse tana kama matsayinta na ko matsowa ta kasa yi kusa da ita sbd kada ta takurata kokuma ganim takeyi qyama zata bawa dr din.
Chapter 7 · 0% Book details